[7/1, 8:35 AM] Lashminzy: 🔥🔥 *ZUCIYAR* *ƊAN* *ADAM*🔥🔥
*Story*
*And*
*Written by*
*Lashminzy**MARUBUCIYAR..........*
*Rayuwar ummiey*
*Rud'ani*
*Muneerah Muneer*
*Hukunci*
*Rayuwata Ce*
*Auren fansa* AND NOW
*ZUCIYAR DAN ADAM*________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*Wannan littafin na KUDI NEH* *Game bukata akan farashi mai sauki 200 kacal aiko da Kati MTN ta wannan number 09061103352 ko ta banki*
*Balkisu Aliyu*
*Acc no: 4000002605*
*Eco bank* *ka tabbatar kayi screenshot din shedar turowa saika turo ta wannan number 09061103352* *Kada ku bari labari ya wuceku*ﺑِﺴْــــــــــــــــﻢِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻢَ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴْﻢ
*FREE page 2*
"Maryam na fita daga gidan bakin titi ta nupa, me mashin ta tara ya kaita tasha inda zata shiga mota zuwa garin su, bayan ta sallami me mashin ne ta shiga motar, ta zaune tana jiran mutane su cika ta tashi, sedai duk jikinta a sake yake wanda tarasa gane dalilin dayasa hakan. Duƙar da kanta tayi ƙasa kamar me jin bacci tayi shuru sai numfashi take fitarwa a hankali wanda in kana kusa da ita zaka ɗauka ko bacci takeyi.
"Duƙe kanta yake har suka iso cikin garin birnin kebbi dake ba wani tafiya ce me nisa ba, duka-duka tafiyar thirty minutes ne daga Aliero, waton garin data fito zuwa cikin kebbi. Bayan ta sauka daga motar ne, ta kira wani ɗan almajiri yayi mata dakon kayanta zuwa bakin titi inda zata samu abun hawa, bada jimawa ba ko ta samu abun hawa, tayi mashi kwatancen anguwar dazai kaita, "cikin mintunan da basu wuce goma ba suka iso wani haɗaɗɗen anguwa mai suna Aliero Quarters, ba laifi anguwar ta haɗu sosai, sedai abunda yafi ɗaure mun kai da ban mamaki shine gidan da maryam ta shiga, wanda saida birona ya faɗi akan haɗuwar shi."Wani tangareren gida ne mekyau da ɗaukar hankalin mai kallo, daga pentin gidan har zuwa gate ɗin fari ne ƙal, tamkar yau akayi shi saboda sheƙin da yakeyi.
"A daidai gate ɗin ta tsaya ta fara buga ƙofar a hankali, megadi dake ciki leƙowa yayi ta ɗan hujin ƙofar dan yaga ko waye. "Washe haƙora yayi ya fito da sauri, ya duƙa har ƙasa ya gaisheta sannan ya ansa trolley ɗinta ya take mata baya, bayan ta shige gidan. Tafiya take jiki a mace harta iso wasu plat masu kyau guda biyu, kaitsaye ta shige na farkon, da shigarta taci karo da wata ƴar dattijuwar mata fara doguwa mai zubin larabawa sedai da ganin yanayinta zaka gane tana cikin damuwa dan fuskarta ta nuna hakan duk da murmushin da take sakarwa maryam dake shigowa.
Rungumar junan su sukayi, ayayin da megadi ya shigo da trolley ɗinta, saurin cikata matar tayi ta kalli Maryam tace daughter lafiya naganki da kaya haka? Ta faɗa tana pointing akwatin, wasu zafafan hawaye ne suka zobo mata wanda batasan dalilin zubar su ba. Cikin rikicewa matar ta amsa gaisuwar da megadi keyi mata taja hannun maryam suka shige ɗaki.A bakin gado suka zauna, cike da damuwa tace maryam meya faru kika dawo gida? Ɗan guntun hawayen daya zubo mata ta share tace mummy Aliyu ya sakeni, WHAT!!! mummy ta faɗa cikin tashin hankali tace me kikayi masa ya sakeki, shuru bata amsa ba, mummy ta ɗaga murya da ƙarfi wanda saida maryam ta firgita tace Maryam dake nake magana me kikayi wa Aliyu ya sakeki??? Tambayar ki nake???
"Cikin ƙarfi hali irin nata kaitsaye tace banyi mashi komai ba, ni nace ya sakeni saboda na gaji da zama dashi, maryam ta faɗa babu ko alamar tsoron uwar a ƙwayar idonta.. "Cikin zafin nama mummy ta sharara mata wasu lafiyayyun mari guda biyu a duka ƙuncinta tace kina da hankali kuwa maryam?? Maryam wallahi kin cuceni kin kuma cuci kanki, yanzu fisabilillahi kin kyauta kenan, duk wahalar dana sha wurin ganin na aurar dake ga mutumin kirki baki gani ba? Murmushi ta saki wanda yafi kuka ciwo tace shikenan yanzu kinba maƙiyan mu damar dazasu dinga jifan mu da munanan kalamai kenan, Wallahi maryam rayuwar mu na cikin haɗari. "Wai kinsan saboda ki samu farinciki da kwanciyar hankali na aurar dake? Amma gashi yanzu kin watsa mun ƙasa a ido??