*💥IZZAR MULKI💥*
_Na murubuciyar_👇
_*TARBIYYA CE SANADI*_
_*UMMIEY*_
_*SARAUNIYA HAFSA*__And Now_
_*IZZAR MULKI*_
_*WRITTEN BY*_
_*HAFSAT IBRAHIM KHALIL*_
_*Cute HapCyyy*_*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*📚
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]__*ƙirkirarren labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba.*_
_*Labarin ya kunshi abubuwa dayawa wanda ya haɗa da yanda ake wulakanta talakawa da sauran abubuwa dake faruwa a rayuwarmu ta yau da kullum*_
_Bismillah Arrahman Arrahim_
_Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon gamawa lafiya. Ameeen_
*EPISODE ONE*↩️
******* *TO FIVE*_____________📲Wani dattijo ne a kalla shekarunsa zasu haura hamsin ke saukuwa akan haɗaɗɗen beni,waya hankalinsa kwance ya kara waya a kunne da alamu kira mai muhimmaci ya ke.
kasa kunne nayi dan naji abinda yake faɗa...
"Duk wata matsala ku tabbatar kun kawar, bana son a ƙara samun matsala irin na baya, idan ma ta kama a kashe su gaba ɗaya". Bansan me aka faɗa ta ɗayan bangaren ba naji ya fashe da muguwar dariya ya ce "ai ba directly zakuyi ba, misali ace ƙunar bakin wake, ko cinna wuta da dai sauran su... Haba Faisal irin wannan makircin duk baka iya ba anya tafiyar zatayi dakai kuwa..?
Shiru yayi daga bisani ya ce, "That's good! Do what is better kai kanka kasan tashin hankalin da zamu shiga matukar mulkinnan ta bar hanunmu". sauraronshi yayi bayannan ya kashe wayar alamar sun gama fuskarshi dauke da wadataccen murmushi.
Harabar gida ya jiyo hayaniya, babu bata lokaci ya je. Dandazon samari ne ko wanne da makami a hanunsa. "Bamayi! Bamayi! Bamayi! Muna bukatar canji! Muna bukatar canji!" Abinda ake jiyuwa kenan.
"Calm down! Calm down ku saurara"
Shiru sukayi dan sauraran His Excellency Yakubu Manuwa.
"Ba sai kunyi min bayani ba nasan cewa batun aikin da muka muku alkawari ne ya kawu ko. To yau ma hakurin zan kara baku in shaa Allah this is the last time zaku ga upper through ur Email. Yana kaiwa nan ya shige ciki sojoji kuma suka koresu a wurin wasu ma sunji rauni sakamakon barkonon tsuhuwa da suka watsa musu tare da dukansu.
****************************Misalin ƙarfe uku ne amma kamar safiya sakamakon ruwan aka tafka .gari yayi sanyi sosai iska mai daɗi ne ke kaɗawa. Wata haɗaɗɗiyar mota ce wanda da gani kuɗi sunyi ciwon kai wurin siyarta na hango. Parking tayi dai² wata karamar ƙofa, cikin zafin nama wasu baƙaƙen mutane fuskarsu babu annuri ko kaɗan suka fito da lema a hannu, kai tsaye suka bankaɗe ƙofar da saura kiris ta karye. Shiga ciki sukayi suna huci tamkar wasu mayunwatan zakuna.
"Lafiya kuwa bayin Allah kun shigo gida babu ko sallama"
Wata mata ce tayi maganar lokacin tana hura itacen garkinta.
Bai kulata ba sai yayi wa ɗan uwansa alamar ya hau saman gidan, ɗaya kuma ya shiga ciki ya fara fito da kayan.
Haka ya hau yana ɗaye kwanun ɗakin ba ji ba gani, sauran kuma suna debo matattun kayan su tare da zubar wa a waje.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Me kuke yi haka dan Allah ku sauko ku rufa mana asiri gidannan kadai garemu idan kuka rabamu dashi ina zamu sa ranmu... Kuka ta fashe dashi sosai ta kuma ce wa "Malam dan Allah ka musu magana, ka basu hakuri kana ganin abinda suke yi bazaka hanasu ba.