*💥IZZAR MULKI💥*
*2020*
_Sabon Salo__Na marubuciyar👇_
_*TARBIYYA CE SANADI*_
_*UMMIEY*_
_*SARAUNIYA HAFSAT*__And Now_
*IZZAR MULKI*
*2020*
_Sabon Salo__*WRITTEN BY*_
_*HAFSAT IBRAHIM KHALIL*_
_*Cute HapCyyy*_*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*📚
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]____________________________
Visit to Like Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
___________________________
_*Dedicated to WHO?*_
🤔_*Yap my Yayu kuma kawayenah! Red color one ne fa😘 when I say red I mean bloody sisters woooo🙃 ZAKF Ubs U ohhhh*_
_*EPISODE 19/20*_
___________📲Da kyar ya tilasta shi ya cincibo Mama ba dan ya so ba, shi kuma ya goyi Haidar sosai su Munnir suke zuba masu wuta kasancewar border a kusa take tuni suka fada wata Kasa da ake kira BUSRA amma sun matukar galabaita.
Direct Hospital ya nufo da su, bai sha wahalar ganin Doctor ba dan a garin asibiti kyauta ne babu bata lokaci aka shigar da su Emergency dan basu cikakken kulawa.
****************
Ciwon kai mai tsanani take fama dashi ko daga kai bata iyawa, ta sirance sosai sai manyan idanu.
yau ta tashi da kwarin jiki kadan ta bukaci ganawa da Mijinta da kuma 'danta Yazeed. Lantana ta sa ta kira mata shi dama kuma His Excellency na tare da ita yana mata fifita, duk da sanyin A.c ga fans amma zafi take ji sosai.
A hankali ta bude kofar dakin dauke da sallama a bakinta, isar masa da sakon Mummy tayi ta fice hankalinta na kan Mubruka da fuskarta dauke da fara'a fal da tinanin me ya sanya ta jin dadi haka ta wuce nata bangaren.
"Zanje nazo ki tabbatar kin tanadar min da amsoshi na kafin na zo"
Ficewa yayi ba tare da tsayawa ya saurari amsarta ba."Allah ya shiryeka Yazeed ina tausayawa maka ranar da zaka gamu da Ubangijinka"
Mabruka ce ta fada a hankali.Zama yayi nesa da ita kadan duk da haka sai kare hancinsa yake da hannu. Magana ta fara bayan sun daidaita zaman su.
"Yazeed bazan gaji da maka nasiha ba, kana abinda kaso a garinnan, baka dauki 'yaya mata a bakin komai ba,ina kake son kai kanka ne? Me ka dauki rayuwa Yazeed? Shin ka tabajin labarin asalinka kuwa? Yazeed ya kamata ka canza, nasan ba lalle na rayu ba, kafin na mutu zanso na baka takaitaccen tarihinka ko hakan zai zama silar shiryuwanka..." Shiru tayi na wasu mintuna, shiko Yazeed sai ya tsine fuskar shi yake tare da sanya handkerchief a hancinsa wai Mommy na wari. Gyaran murya tayi ta cigaba da magana cikin sanyin murya duk da ba fitowa muryar tata take sosai ba
"Yazeed ba kowa bane kai fa'ce dan ta...." Tsayar da ita yayi da magana ta hanyar daka mata tsawa tare da daga mata hannu, a fusace ya bar masu dakin yana huci"Son! Son! Son!..." Gwamna ne ke kiransa amma ko a jikinsa ko juyawa baiyi ba.
"Sorry dear! Ki rabu da Yazeed dinan dan Allah, sanin kanki ne fa shi kadai Allah ya bamu, taya zamu takura masa ne mu hanasa sakewa? Ina iya juran ganin bacin ran kowa amma banda my only Son, understand ni banga wani laifin da Yazeed ke aikatawa ba da har kike daurawa kanki tunaninsa haka"