⚪⚫⚪⚫
⚪⚫⚪
⚫⚪
⚪♥️ *HASKE* 🤍
*BAYAN*
🤍 *DUHU*♥️
( _A beautiful love story 2020_)⚫
⚪⚫
⚫⚪⚫
⚪⚫⚪⚫Page1️⃣to2️⃣
WRITTEN
By🤍 *AMEENA UMAR FARUQ*♥️
OR
Meenat
Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
*_ZAUJUN-MAJNUN_*
And no
HASKE BAYAN DUHU_GABATARWA_
_*Bismilahirrahamaniraheem dasunan Allaha merahama mejinkai,tsirada amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S A W) da iyalansa da sa ameen ,ya Allah ina rokon ka yanda kabani ikon fara littafin nan lafiya kabani ikon gamashi lafiya ameen.SADAUKAR WA
Na sadaukar da littafin nan ga iyayena abin alfaharina ina godiya matuka da irin tarbiyyar dasukai mun, shiyasa kullun nake rokon Allah yasa sugama da duniya lafiya amin ya Allah love yours my dears heat._TSOKACI_ wannan littafin k'irk'irarran labari ne na rubuta shi don FADAKAR WA, ta iri yanda"iyaye yakamata surinka ba ya'yansu tarbiyyar labarine tsananin musluma da Christan yana dauke da NISHIDANTAR WA tare da tsantsan soyayya me tsafta da TAUSAYI, don haka duk wanda yaga suna ko hali yazo daya dana sa badashi nake ba just arashi ne so kubiyo ni.
Bismilahirrahamaniraheem
ENUGU STATE
Y k y farmer house
Da misalin marfe 10:00am nasafiyar lahadi
Wani katafaran gidan gona ne daya amsa sunansa gidan gona wani tsararran ginin bene ne acikinsa Wanda ko acikin gine-ginen zamani, wannan din yafita da ban acikin su kuma shidin na musamman ne domin kallo daya zakai Masa kagane tsarin bana gida najeriya bane,
2 apartment ne kawai sai wani katafaran gareje Wanda yake dauke da tsala-tsalan motoci kimanin guda shidda, apartment din suna kallon juna fantin su iri daya ne wato kalar ash da white ne wanda dagani bana kasar najeriya bane domin kuwa wani irin shining yake me daukar ido,
"Daya apartment din nanufa danashiga falon kusan suman tsaye nayi saboda tsabar haduwar shi, fantin shi silver da gold ne hakan labulaiyan suma kalar silver da gold ne hakan ma manya-manyan kushin din Kai komai na falon kalan kenan idan kacire tabkeken t.v bango wayanda suke jone da wasu tsala-tsalan sifiku,
bedroom na shiga wow! inji bature malam bahaushe Kuma yace masha'allah shima fantin irin na falon ne Kai nikam bazan tsaya siffanta maku bedroom ba saidai ku suffanta shi dakan ku hhhhh,
Katafaran gado ne da yakusa cinye rabin dakin gadon shinfid'e yake dawani expensive bedsheet me asalin kyau da taushi, silver color ne da ratsin gold hakama bargon da'aka rufa dashi oh! ni nikam nace masu gidan nan sunason kalar gold da silver,
"Ahankali naga ana juyi akan gadon gaba ɗaya harda bargon tsawon wani lokaci sannan sannun ahankali aka yaye lallausan bargon, tare da zuro dogayen kafafu masu dauke da kwantacce suma luf-luf ahankali yatashi zaune yayi abakin gadon sanye yakeda rigar barci me taushi fara tas irin me igiyar daurewa tagefe,
"sai kuma yasauko tare da tsugunnawa yazuba guiwoyinsa akasa sai yakalli gadon sannan yarufe idonsa ya dukar dakai tare da hada hannuwa sa guri daya sannan yafara motsi da bakinsa, nikam nace ikon allah domin kuwa gani nayi kamar yana irin addu'ar yan choch! yadauki tsawon wani lokaci sannan yatashi,
"Cikin lokaci kankani na kare masa kallo kai! masha'allah kyakkawan saurayi ne dogo sosai don har yadan rankwafa kaɗan fari tas dashi gashin kanta acukurkude take tamkar shuwa araf fuskakar shi tana dauke da dogon hanci Dan bakin Sha dai-dai misali jajir dashi shibaiyi faɗi ba shi Kuma baiyi karami ba,