🌐'YA TA

7 1 0
                                    

🌐 🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ Aѕѕocιaтιon
   🌐(Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

        
SADAUKARWA GA DUK WATA UWA DAKE DUNIYA,MUSAMMAN MA TAWA WACCE BABU KAMARTA MAMEENA ABAR SO NA,INA JINJINA MIKI INA KAUNAR KI LODI LODI

MAMEENA TA KAINA LOVE U 💕💕💖💞💌💝❤💋💋

Wannan littafin kirkirarren labarine ga duk wanda ya ga labarin yayi kamada rayuwar shi,ya sani an yi sara ne akan ga'ba.

Amina Sani Hussain
(Mrs ShehuShamaki~Oum Sahla)

Facebook:Amina Hussain
Email:Aminahussainsani@gmail.com
 

Ranar muke jira yau gashi ta xo💃🏻💃🏻
Mu Hikima muna ta murna ga shi ta xo 😘 💃🏻
Mrs noor muna taya ki murna🤗🤗🤗😄😃
Da Allah ubangiji ya bamu baby 👶

Allah ya kara miki lpy mrs noor ya albarkaci rayuwar baby boy

Wannan shafin da ke ya fara kyauta ga baby boy 🎁

KU YI HAKURI DA ABINDA ZAN CE🙏🏻🙏🏻😐😐😐

Wannan littafin ba ze dinga zuwa a koda yaushe ba sabida ina da uzururruka da suke kaina dan hak a yi min afuwa da yanda ze dinga zuwa,amma inshaallahu zan iya kokarin na ga kun same shi a sati sau uku ko hudu.
Fatan xa a fahimce ni,goyon bayanku shine kwarin gwiwar mu ,kar a gaji da yin comment dan yana kara mana kaimi.👍👍

Up up up masoya kuna kamshi ina binku da Humra💕👌🏼👍👍❤🎁

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

BA A TACE RUBUTUN BA(not edited)

1⃣

"Abinda xan fada miki yanxu ba sabo bane,na sha fada miki shi tun a baya,se dai na kara jaddada miki su.
Rayuwar da xaki shiga yanxu ba irin ta gidan ku bace yanxu ke ahalin wasu ce,xaki ga abubuwa sabanin yadda kike ganinsu a nan,inason ki zama me biyayya ga miji,me hakuri da juriya,ki zama me tawwakali,ki rike mijinki hannu bibbiyu,kada ki sake wani abu ya faru tsakaninki da shi  ki yada shi ga kawaye ko wani,na dadi ko akasin haka,ko mahaifiyarki ba komai xaki dinga fada mata ba se wanda ya fi karfinki shawo matsalar da kanki" shiru ne ya biyo baya kafin ta cigaba da cewa

"Hafsa ina son ki rike addua'a ki rike sallah akan lokaci kada ki bari wani abu ya dauke hankalinki ga wadannan abubuwa guda biyu da na fada miki.idan kinga al'amura na son kwabe miki game da xamanki  da mijinki bance ki xargi kowa ba domin ba abinda yake saurin bawa shedan damar mulkar xuciyar ka irin komai ya sameka kace ai wane ne ya samin hannu ,ba wanda ya isa ya cutar da kai da wani abu face allah ne ya kaddara hakan zaya sameka ,dan haka ki maida lamarinki ga allah shi xai baki mafita.Abu na karshe da xan fadamiki shine kirike tsafta,ki rike girki nasan ki a wannan fannin ba ki da matsala amma ki dada akan yadda kike ,ina rokon allah ya baki zaman lpy ya kare ku daga sharrin duk abin ki allah ya sanya albarka a xaman ki da shi da danginsa baki daya"

Duk xancen nan da Aunty Rukayya ta ke kan Hafsa na kasa ba abinda take se kuka,don a yau ne xa'a kaita gidan mijinta dake Kaduna.

Duk da tana jin nasihar Auntyn  tata kuma ta dauka amma hankalin ta tashi yake in ta tuno yau xata bar danginta da 'yan uwanta ,zata je can wani gari inda ba nata dangin se na mijinta xasuyi rayuwa tare,ya suke,ya rayuwar su take allah ne masani,fatanta daya allah ya  sa abokan arxiki ne wanda zasu zame mata dangin ta da ta baro anan Kano.

Tana wannan tunanin ne taji Aunty na mata maganar ta zo tayi wanka,tashi tayi tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta shiga bandakin (toilet).

Kafin tafito ta gama hada mata kayan da zata sa ta feshe  su da turarurruka masu kamshi da kuma humra tajiye su,sannan ta bar dakin .

Se da Hafsa ta gama wankanta tsaf sannan ta fito. Gaban mudibi ta zauna ta fara shafa mai jiki a sanyaye a haka Aunty ta kara dawowa dakin ta sameta,ita kanta ta bata tausayi dan rabuwa da iyaye ba dadi ko da a kusa kuke da su bare ita da aure xe kaita har wani garin,ba yadda xatayi haka  abin yake,shiyasa hausawa suke cewa_"Aure yakin Mata"_

'YA TAWhere stories live. Discover now