AISHATUL MUWAFAK'A

14 2 0
                                    

💓💓 💓💓 💓💓
〰〰〰〰〰〰
*AISHATUL MUWAFAQA*
〰〰〰〰〰〰
💓💓 💓💓 💓💓
*1441H/2019M*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*STORY AND WRITING:*
*AYSHER AlIYU *HUMAIRA(INNARO)*

*Dedicated to:*
*ZAINAB AHMAD SHAREEF*
           &
*HAFSAT ABBAS BABI*

~🗓December~

'''Follow & Vote 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.'''

*Page 36↔40*

_____________📖Daga Ɗayan 'bangaren aka ce, "hello Assalamu Alaikum".  Wani ihu Muwaffak'a ta saka tace.



"Ya Ammar ashe baka manta dani ba, shine ko ka kirana ka daina  bari nayi maka fushi".

Gargiza Kansas yayi  yace.



"haba lil sis taya za'ayi na manta da ƙanwata, ai idan na manta dake tamkar na manta da kaina ne" .



Tace "I miss you so much Yaya Ammar".

yace.

"Miss you too ƙanwata".

tace "yaya Ammar na fara zuwa school fa yau".

Magana ya k'ara yi mata da cewa.



"Masha Allah  sweet ƙanwa sai ki mayar da hankali da karatu kinsan dai likita nake so kiza ma ko?".


Kuma  nasan halinki da tara ƙawaye Dan Allah a rage tara su  kinga pramry da secondary ba ɗai ba".




Murmushi tayi tace.

"Insha Allah yaya Ammar zan mayar da hankali,sosai naga na zama abinda make so".


"haka nake so ƙanwata idan har na samu labarin kin mayar da hankali akan karatun ki zan siya maki wani abu, amma  bazan faɗi ko mene ba".

Ya k'arasa maganar yana murmushin jin dad'i.

A haka sukaci gaba da hira har ƙarfe tara  tayi sannan sukayi sallama, ta jawo littafan ta ta cigaba da rubutu har tara da rabi tayi sannan ta gama.

  Yaya Muhaisin yazo ya karɓi waya taje ta watsa ruwa ta saka kayan bacci, sai ga Ammi sun dawo ita da Mubarak da Kausar.




Koda suka dawo Kausar ma tayi bacci tun suna hanya  Mubarak ne kawai yazo ya rungume ta yana murna itama ta rungumeshi tana  murnar dawowar ƙannen nata  saboda tayi missing ɗinsu ba kaɗan ba.





Ammi ce tace

"Muwafaqa ki ɗauki Kausar ki canja mata  kaya zuwa waɗanda take bacci dasu".




"To Ammi".

ta ɗauki Kausar taje ta canza mata kayan bayan  ta canza mata ta  shimfiɗe ta sannan tasa Mubarak ya canza nashi suka fito tare.

Koda suka fito Abii ma ya dawo nan suka zauna suna fira tare da Abii da  Ammi da Yaya Muhaisin
har ƙarfe  sha ɗaya  tayi basu ankara ba.




Sai can Abii yace "kowa ya tashi yaje ya kwanta dare yayi.

suka miƙe suka masu sai da safe.

yaya Muhaisin ya tallabi Mubarak da yayi bacci tun ɗazu suka wuce ita kuma Muwafak'a ta wuce ɗakin su  taje ta kwanta kusa da Kausar Abii ya shigo ya masu addu'a ya fita.





"Muwaffaƙa! Muwaffaƙa!! ki tashi lokacin sallah yayi".

Ammi ce ke tada ita,cikin bacci taji ana kiran ta ta miƙe tana karanta  addu'ar tashi daga bacci a bakin ta  da Ammi taga ta miƙe ta juya ta fita.





Ita kuma tashi ta wuce toilet ta ɗauro alwalla tazo tayi raka' atanil fajri  sannan tayi sallar subahin bayan ta gama tayi azkar ɗin safe.



Sannan ta tada Kausar taje ta gwada mata yanda zata yi alwallah suka fito tayi sallah.

A lokacin ƙarfe shidda saura k'wata taɗau litattafan ta taja hannun Kausar suka yi ɗakin Abii koda suka zo,su Abii sun dawo daga masallaci.




Gaida Ammi da Abii da Yaya Muhaisin ita kuma Mubarak da Kausar suka gaida Ita.



Bayan sun gama gaishe -gaishen  ko wanne su ya buɗa littafin sa da Ammi aka fara sannan yah Muhaisin sannan Muwafaƙa sai Mubarak Kausar ce k'arshe.


Bayan sun gama Abii yace.

"Koda mai wata buƙata?".

duk suka ce babu yace.

"shikenan
Ku tashi zuwa shirin makaranta".

  Suka miƙe su kabar Ammi anan.








Suna shiga ɗakin su Miwafaƙa ta aje littafan ta ita kuma Kausar ta kawanta, ita kuma ta fito ta shiga kitchen tafara aikin haɗa masu abun kari.








A ɓangaren Malam Arrida kuwa bayan sun dawo daga masallaci sallar asubah har zai wuce ɗakinsa yaji motsin Mummynsa a kitchen yaje ya gaida ita Ƙanwar sama ta gaida shi yace.




"Mummy dami zan taimaka maku?".

suka sa masa  dariya Amnah tace "Kai kam Yaya matarka taji daɗi komai ka iya kai zaka riƙa yi mata".




Harar wasa ya mata yana cewa "wallahi Mummy ki jama yarinyar ki kunne inba haka ba ko...."

Koda yake bari Nasan Maganin ta cikin Ƴan uwan Abba dake ƙauye zan sami guda na bata Kuma fa tsofaffinan........"

ya ƙarashe faɗa yana dariya.




Amnah ta turo Baki a gaba,kamar zatayi kuka tace.

"Allah Yaya nadaina".

suka sa dariya gaba ɗai Mommy ce tace.




"Ai har mun kusa gamawa jeka abunka".

ya fice yana dariya direct ɗakinsa ya nufa domin ya shirya.




Bayan tagama haɗa break  ta zuba ma kowa nasa taje tayi wanka koda tafito  tashirya cikin uniform ɗinta ta ɗauko school bag ɗinta tafito
zuwa ɗakin ammi.





A can  ta iske yaya Muhaisin Yana break itama zama tayi tayi join nashi bayan sun gama sukayi ma Ammi sallama suka tafi sai Makaranta.




Koda sukaje yau bai shiga ciki ba bakin gate ya aje ta yaba ta kuɗin break yayi gaba.



ita kuma tayi cikin makaranta koda tazo bakin gate prefect on duty na nan ga wasu d'alibai gefe Itama sai ta tsaya ta gaidasu suka amsa fuskar su da murmushi (kunsan prefect akwai son girma😜😜).




Suka ce ta wuce dan tazo  da complete uniform ɗinta ta wuce class koda tazo su  Ramlat kawai tatarar suka gaisa ta ɗauko buks ɗinta ta bata.







Suna haka saiga Bak'areeya Muwafaƙa ta tashi da gudu ta rungume ta ta karɓi jakarta Tana faɗin.



"Oyoyo name sake" Bakareeya  tayi murmushi tace "ya kike ya su mama?" Muwafaƙa tace.

"lafiya ƙalau Suke ya kika baro mutanen gidan?".

  Bakareeya tace "kowa ƙalau yake".

Suka zauna Bakareeya ta gaisa dasu Ramla.




Ramlah tace masu "ku tashi mu tafi wurin Assembly tun masifaffen can bai zoba".

suka ce.

"wa kenan?".

  tace.

"sajent Mana".

Suka sa dariya daganan suka wuce wurin assembly.





Taku har kullum



© *INNARO*

AISHATUL MUWAFAƘAWhere stories live. Discover now