page 2

20 4 0
                                    

💅🏻💅🏻💅🏻SLAIM💅🏻💅🏻💅🏻

FREE BOOK

BY
AMNAH A MUHAMMAD

(MIEMIE MUHAMMAD)

PAGE 6-10

"Kekinzo bazaki shigo bane" Slaim dake durƙushe taji ana mata magana daga bayanta.

Nan take ta tsayar da kukan da takeyi sannan ta shiga goge hawayen dake fita daga cikin idanunta.

Ahankali ta juyo ta fuskanci Inna dake tsaye daidai inda kayanta yake, murmushi ta daura akan fuskanta tareda ƙoƙarin boye damuwanta.

Itama Inna murmushin ta mayara mata da kafin tace da ita "Baban nakai ya tafi ne?" waiwaye waiwaye Slaim ta fara kaman bata fahimci abunda Inna ke nufi bah,

ganin da tayi Inna ta tsare ta da ido ne ya sata yin wani ɗan murmurshi mai sauti wanda bayyanar da wushiryan ta ya kuma ƙarama fuskan ta kyau dukda cewa da ka kalleta zaka fahimci akwai damuwa atattare da ita kafin tace "wai kina tunanin tare nazo dashi ne?"

kallonta kawai inna tayi bah tareda ta ƙara cewa komai bah ta dauki akwatin dake gefen ta tana ƙoƙarin shiga dashi cikin gidan itama bata ƙara ceda Inna komai bah ta ɗauki jakan makarantan tah dake aƙasa wurinda ta tsugunna sannan ta ɗauki ɗayan jakan da Babanta ya ɗauko mata daga gida itama ta rufama Inna baya zuwa cikin gidan.

Da sallama ta shiga gidan sannan ta shiga bin gidan da kallo.

Gida ne dan madaidaici meɗauke da ɗakuna guda biyu kowanne da bayi aciki sai babban kicin dake Inna abinci take siyarwa inda gaban gidan tasa akamata wani ƙaton ɗaki data zuba kujeru da tebura domin zaman masu sayan abincin.

Kallon ɗakunan Slaim tayi inda taga ɗaya daga cikin ɗakunan an rufe shida kwaɗo, kallon Inna tayi ta 6ata fuska sannan tace "ya naga wannan ɗakin a rufe?" "haya na bada" Inna ta bata amsa ataƙaice bah tareda ta kallin inda take bah.

Murmushi Slaim tayi dan tasan haka sukeyi ita da Inna kaman sa'annin juna "lallaima kakale (kakale shine sunan da Slaim ke kiran Inna dashi) kinsandai ɗakinane shine kika bada haya koh" Slaim tana kaiwa nan a zancenta ta shige ɗaki da kayan ta.

Tana shiga tayi wanka tareda ɗauro alwala tayi sallah sannan ta haye gado tayi kwanciyanta inda Inna ta tafi wurin sana'anta ba tareda ta shiga ɗakin bah dan kayan Slaim ma daga ƙofar ɗakin ta ajiye amman ta cikin ɗakin.

Yau kwanan Slaim hudu awurin Inna koh ƙofar gida bata taba leƙawa bah tsakar gidan ma bata fiya fitowa bah hakan yasa taji zaman gidan duk ya isheta. Kwance take asaman gado kamar koda yaushe Inna ta shigo ɗakin da sallama a bakinta, wani irin qululun bakin cikine ya mamayeta sanin cewa mai amsa mata sallaman nata tana nan kwance tana baci wanda yake matuqar 6ata mata rai tsaki ta ja kafin ta fara jan bargon da ta lullu6e jikin ta dashi tana fadin "Silaimi!..........ke Silaimi waike bansan yanda akayi wannan baccin asaran ya zame miki jiki bah"mtswtakai qarshen maganan nata da jan wani tsakin. Slaim na jinta amman tayi burus da ita kaman mai yin bacci, Inna kuwa cigaba da jan bargon tayi tana kiran sunan Slaim amman taqi ta tayi koda kwakwkwaran motsi saida taji Inna na bubbuga gefen katifan da ƙarfi sannan tafara juyi daga farkon gadon zuwa qarshe, taje ta dawo taje ta dawo ɗauke da salati abakinta.

SLAIMWhere stories live. Discover now