21 & 22

1.4K 28 0
                                    

💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

      
💫💫 _*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_💫 💫

            ✍️ M SHAKUR



                   2️⃣1️⃣ & 2️⃣2️⃣



FREE PAGE
Yau tun karfe biyar tamai a airport sabida karfe biyar na yamma jirginsu zai sauka anan Abuja, Ammi tun safe take dannamai kira takirashi yafi sau biyar dan kwana bakwai dinan tai kewanshi kaman me, tace mai su sauka agidan ta tamusu girki.

5:05pm jirjinsu yay landing a nmandi azikiwe airport, yana zaune acikin Airport yana kallon gaban Airport din suka fito, tana sanye dawata matsassen doguwan rigan lace sky blue ta yafa dan mininin gyale da handbag dinta da wani Hill, sai shikuma Arham yana sanye dawata soft yard shima sky blue ka kagansu zaka dauka mata da mijine ma'aikatan Airport na turo musu luggage dinsu a cart, saikuma yaran dasukayo layi sunyi tsaf tsaf loking neat staff dinshi na jerasu suna dumfaro marcopolo bus din dake pake gaban motarshi, karasowa gaban motar Arham da Ilham sukayi hakan yasa ahankali yabude motar yafito murmushi dauke kan fuskarshi ya bala'in kewan Arham dan yasaba duk inda zashi aduniyan nan da Arham suke zuwa inba wanan emergency daya rabasu ba, cikedajin dadi yace "hey rascal welcome" sukadan kashe kafin suyi hugging juna Waleed na murmushi saikuma yasake shi yace "look yanda kai fresh abinka da nine da yanzu nai zuru zuru yaran nan sunsa na fita hayyacina" dariya Arham yayi yace "sabida kai stress ne baka saba da wahala ba saisa, niko nasaba saisa har wata kyau nayi" dan hararanshi yayi yace "dalla yanzun aikin dazanyi kokai bazaka iya yinshi ba" yay maganan yana dan juyawa ya kalli Ilham dayaga itama tai shegen kyau ta kara haske kaman mai shafamai, folding hannunshi yayi akirji yana kallonta, yanda yake kallonta kaman mai son gano wani abu yasa taji she's feeling uncomfortable, rasa mezatayi yasa tai gabanshi ahankali zata rungumeshi dan tsayawa tayi gabanta nafaduwa sanin Arham na wurin saikuma ta daure ganin yanda Waleed ke kallonta tace "oyoyo baby" "mesa kika saka gyale a irin wanan kayan, please this should be the last time" gyadakai kai tayi ahankali tana sakinshi, Waleed ya kalli Arham yace "ku shiga mota, bari na gaisa da yarana Ammi na jiranmu tamana girki" yay maganan batare daya jira amsan suba yay wajen yaran da sai a lokacin suka lura dashi ai motar dabasu shigaba kenan sukayo kanshi. "oyoyo teacher, oyoyo teacher" daga wayanda zai iya sama yayi cikin jin dadi sanan yace "ku wuce ku shiga mota, kuje kuhuta nasan amuku special treat" sakin su yayi sanan yaje suka gaggaisa da ma'aikatan shi sanan suka shige motar tsaf, yadan bubbugi motar alamun direban yaja su tafi sanan yawuce yakoma mota inda har Arham ya shiga gaba, Ilham abaya, zagayawa yayi yashiga gaba yaja motar, sosai suketa hira da Arham amotan har sukakai gidan Ammi, parking sukayi suka fito, tun kafin sukai gaban flat din Ammi ma Ammi tafito tana sanye cikin shigan alfarma wata atampa exclusive dake numfashi tayi ado da zinare akunne da yatsunta duka biyar, washe baki tayi tana fitowa tawani irin rungume Waleed, itafa Ammi danta shine nafarko kawai a komi nata kuma bata kunyan nunama danta so agaban uban kowa, tanason Ilham sosai amma son Ilham baitaba ketare na Waleed ba kaman yanda wasu surukan sukeyi sai kaga sunso matan y'ay'ansu sama da dansu ita ina danta ne number one.

Tadade rungume dashi shima yay mugun kewanta inyaga Ammi ko Mom shagwaban shi tashi take, dagoshi tayi ta mannamai kiss a goshi sanan tace "sannu da zuwa Son, ya hanya? Hope bakagaji ba ko?" gyadamata kai yayi yana yatsine fuska yace "I miss you Ammi" murmushi tayi kaman ta hadiyeshi take tasake shi tace "ina zuwa" sanan takalli Ilham dake tsaye tana kallonsu tace "daughter na" guwiwa Ilham takai kasa zata tsugunna ta gaidata da sauri Ammi ta dagata ta rungumeta tace "sannu dazuwa diyar kirki, my son is looking masha Allah, Allah yamiki albarka kinji" akunyace ta gyadama Ammi kai, sakinta Ammi tayi tace "wuce kishiga ciki, nasa an gyara muku daki a upstairs yau awajena zaku kwana jeki wanka kufito aci abinci" gyadama Ammi kai tayi tawuce, sai alokacin ma Ammi ta lurada Arham dake tsaye kanshi akasa, dan murmushi tasaki ba yabo ba fallasa tace "Arham mutanen yankari" dago kanshi yayi fuskarnan cikeda murmushi saiyadan rage tsawo yace "Ammi ina yini, mun sameku lpy" "lpy lau Arham" Ammi ta amsa tace "shigo mana" tai maganan tana juyawa takama hannun Waleed dayabi ya langabe mata kaman wani dan jariri sukai ciki Arham biyeda su abaya, hakanan yaji wani iri, Ammi ta rungume kowa harda musu peck amman shi ko kanshi bata shafaba kaman ba bataji dadin ganinshi ba, shine abokin danta tun yana yaro amman haryau bata wani sakemai ingaka murmushi da fara'an Ammi toda danta Waleed ne, bude kofa Ammi tayi suka shige ciki itada Waleed Arham biyedasu, ahankali Ammi tace "to go and freshen up saika sakko aci abinci" kaman zaiyi kuka yace "wlh ni yunwa nikeji Ammi I will do dat after eating, blood ai kaima yanzu zakaci ko"? Dan  murmushi Arham yayi sanan ya gyadakai, Ammi tace "to ai saiku taso kattin banza ko Khadija bazaku iya jiraba" dining din sukayi taja kujera Waleed yazauna Arham ma yazauna Ammi tace "Arham feel free zuba abinci kaci wanan abokin naka shirme zaitayi" kaman Waleed zaiyi kuka yace "nine mai shirme Ammi to bazan ciba ma" ya yunkura zai tashi da sauri Ammi tarike shi, zaunar dashi back tayi tana dariya.





DUNIYA BIYU MABANBANTA (TWO DIFFERENT WORLD) Where stories live. Discover now