A kullum iyayen mu suna son mace ta zama 100%perfect to mijinta shiyasa mace tun tana karamar ake koya mata yadda zata kyautata ma mijinta wata tun kafin tasan meye aure tasan muhimmancin miji sbd yadda ake jingina komai na rayuwanta da cewa "YANZU IDAN KI KAI AURE HAKA ZAKI RIKA YI MA MIJINKI"
Amma kashe iyaye suna mancewa da shi ma namiji ya kamata a biya masa muhimmanci matarsa kai bama matarsa ba a fara nuna mashi muhimmancin tausayawa kanwarsa a kullum idan iyaye suka kira yaya namiji babba tou fa al'amarin bugu ne ya tashi ina soyayya da tausayawa ta yan uwantaka.
A wani bangare suma wasu mazan suna so mata su kasance 100%perfect to them amma hakan ba zai taba yiwuwa ba kasancewar su masu rauni irin na dan adam, sannan masu rauni a matsayin ya'ya mata. A garin son matan su zama 100% perfect to them Sai tunanin mata ya bambanta game da halin wasu mazan wata tana ganin Wasu Mazan Azzalumai ne wata kuma tana ganin ba su da adalci wata kuma gani take ba su da tausayi sbd rashin uzurin su ga matansu, da rashin hakuri halayansu wata ma gani take shin addini ya basu wannan damar su yi yadda suke so, ko kuwa addini ne ke bai bama diya mace yancinta ba ko kuma kila Addinin ya bada amma Al'adu da al'ummarta suka tauye mata .
Shin ina matsalar ta ke daga ina wasu mazan suka samo wannan tunanin na son mata su kasance masu 100% perfect Ku biyo ni idan na gama Labarin ZAMAN YA'YA DOMIN mu ji daga ina matsalar take a cikin LABARIN HABEEBA(HIBBA) DA HABEEB DAN UWANTA.
#Yancinta a musulunci
#Nuna mata bambanci tsakaninta da yan uwanta maza.
#Rashin uzuri gareta idan tayi karamin kuskure.
#Rashin godiya da yabawa gareta
Kalu balen da habeeba ta fuskanta.
DANDANO
Kwance take yau zazzabi ya kamata tana kwance tana rawar sanyi,mama bata nan ta je unguwa daga ita sai yayanta habeeb da ke zaune can nesa da ita yana latsa waya.Mama ce ta shigo da sallama ganin ba'ayi shara da wanke wanke ba gidan kaca kaca ba yadda ta saba ganinsa ba ya saka ranta ya baci tana shiga daki ta ce "Haba hibba yanzu ace tun dana fita ba abunda ki ka yi na aikin gida?
Hibba ta ce cikin rawar sanyi " mama ban lpia tun zazzabin da kika bar ni da shi bai sauka ba mama.
Mama ta ce yanzu akan wannan dan zazzabin kika narke ki ka kasa tashi kiyi aiki yanzu hibba idan Kika yi aure kina laulayin ciki ko baki lpia shikenan haka zaki narke so kike mijin ya tsane ki ya koro mani ke in shiga uku.Hibba ce ta ja lumfashi cikin dacin rai kullum maganr daya kenan tun kafin takai haka tun tana fara wayau ake nuna mata muhimmamcin namiji a gareta kullum da tayi kuskure ko ciwo ba wani uzuri da za'ai mata irin na yau da gobe da ajizanci irin na dan adam sai a hau mata fada ana gaya mata tana gazawa tou fa miji zai koro ta ne shin shi miji bai san ciwo ba ko bai san ajizanci irin na dan adam ba.....
Habeeb ne ya katse mata tunani inda yake ce ma mama "kinga mama yunwa nake ji tun dazu amma yarinyar nan ta tsaya lalaci kan dan karamin ciwo ta langabe.Daga kai hibba tayi ta kalleshi cike da bakin ciki tunda suke da shi tun suna yara bata taba jin inda aka ce ma habeeb kada yayi kaza ba sbd zai cutar da matarshi ba ko kuma idan tana ciwo ace ya taimaka mata da yin aikin gida ba sbd rashin lpiar ta kai ko nuna tausayi da jinkai bashi da shi sbd jiya da ta tashi zata yi amai a bisa kuskere ya fara zuba bisa rigan habeb wanke mata mari yayi yana bala'i dan me yasa za ta yi mashi amai baza ta lura ba hakuri mama ta bashi akan cewa sakacinta ne yanzu haka zata je gidan miji tana aikata haka ai tsaneta.
Maimakon mama ta nuna mashi tausaywa ma mace idan bata lpia a'a ina idan kika ga habeeb ya ji tausan ta ko kuma yayi mata uzuri tou fa ciwo yakai ciwo wanda yake gani kamar zata mutu.
Haka yana zaune yana latsa waya mahaifiyarshi ta shiga kitchen ta tanadar mashi abinci tayi shara tayi wanke wanke yana zaune yaana latsa waya abunshi kuma a zamantakewa irin tamu shi bai yi laifi ba mahaifiyanshi na aiki shi yana zaune.wai sai ace ai aikin mace ne ko a wani nassi ya zo a haka ?
Baba ne ya shigo da sallama yana murna, ganin mama tana ta aiki ya saka ya fara ma hibba fada yanzu kina zaune mamarki na aiki baki taya ta?
Ce wa tayi "baba ban lpia fa ba ga yaya habeeb ba zaune yana kallon mama tana aiki amma bai taya ta ba....
Katseta mama tayi haba hibba baki ganin aikin mata ne ina ruwan namiji da aikin mata.Admission din habeeb ne ya bashi na samun gurbin karatun medicine a jami'a ya samu.
Hibba ta shi tayi zaune ta ce" baba ina nawa?
baba ya ce wai ina mace ina karatun likita salon mutane su ce na daure maki kugu kina karatu kin ki aure kuma idan kikai karatun likita ba kowane namiji bane zai so macen da ta zama likita sbd likitoci basu da lokacin zama gida kuma ina iya shan wahala in kashe kudina kiyi likitan sai kin gama kawai mijinki ya ce bai son kiyi aiki kinga nayi asaran kudade na ko.Kuka ne ya zo ma hibba yanzu shikenan namiji ya zama shamaki ga cikar mafarkinta Shin wai wani gata ne Addinin musulunci yayi ma diya mace wane yanci ne ya bata a matsayinta na diya mace.Shin shi ya habeeb ba'a nuna masu muhimmancin likitoci mata bane a wannan zamani da matsalolin mata suka ninka na maza.Shin ba sadaukarwa ba ce miji zai matarshi ta taimaki al'ummarta ba da kare martaban addininta ba?
KU BIYO NI DAN JIN INA HIBBA ZATA SAMU AMSARTA .IDAN NA GAMA RUBUTA ZAMAN YA'YA
YOU ARE READING
ITAMA DIYA CE
General FictionKALUBALE GARE KU IYAYEN YAN MAZA.A KULLUM NAMIJI YANA EXPECTING MATAR SHI TA ZAMA 100%PERFECT TO HIM AMMA KUMA HAKAN BA MAI YIWUWA BANE BA SBD RAUNI IRIN NA DAN ADAM. A GARIN SON MATA SU ZAMA 100%PERFECT SAI SU KUMA WASU MATAN SUKA TA SO DA WANI T...