Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GH8hcp1bjywGWfWPFe97Nv
*KUNJI MUNAFUKI...?*
_labari na ban dariya_~MALLAKAR~
👇🏻
~*OUM MUMTAZ*~*WATTPAD@UMMIE2018*
*FACEBOOK@OUM MUMTAZ*
*INSTAGRAM@itz_me_real_oum_mumtaz*
*G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com*
'''Sadakarwa ga mahaifina da mahaifiyata.'''
*~DEDICATED To~*
'''RAHMA( awallina)'''
*Page 4*Wato tin tasowarsu gidansu abbas nanne mahadarsu dasuke wasansu har kawo girmansu sbd yadda kowa keyi abinda yaga damaryi cikin gidan babu maice maka bari saima a zugeka!abinku ga yaro hakan yasa suka kullaci zuwa gidan sosai!
abbas yana da kanwarsa guda dasuke uwa da uba daya wato teema! ba kasafai take shiga shirgin yan gidan nasu ba amma idan aka tabota,to kuwa tabbas bata barin mutum saita dau fansa!
shi kuwa bobo bakomai ne ke burgesa ba daya sa shi nacewa gidansu abbas saidan yawan fadan dayake ganin matan gidan nayi,wanda hakan ke matikar sashi nishadi kwarai da gaske!
hakan yasa tin yana yaro karaminsa bai gama sanin mainene aure ba yaci alwashin auren mata hudu kodan yaga anayin fada akansa da zai samu abin kallo,dik wannan kudirin nasa kuma babu wanda yake da labari a cikin gidansu!
saikuma salim dashima yake da kanwarsa daya wato feena! yar gata ce sosai na bugawa a jarida dan haka yasa ko girki ma basu iya ba a gidansu sbd komai yimasu akeyi!
sannan ahmad daya kasance yayan ameera sukuma yaran yayar mamansa ce!
salmaty kuwa yar mai aikinsu ce da suka faso birni daga kauyensu har itama ta murje abinta tazama yar birni! gata da shen tsokala kamar me...? amma dikda haka sosai kakar bobo ke bala'in ji da ita kamar ba yar aiki ba!
soyayya baji ba gani ne ya kullu tsakanin teema da bobo kamar su ci kansu,wanda sam teema bata da labarin ko kuma sani dangane da kudirin bobo na son auren mata hudu a lokacin daya!
dan haka ta sakankance abinta cikin kogin kauna sbd yadda bobo ke tafiyantar da ita akan soyayyarsa
inda har manya ma suka san da zance! Sannan a gefe guda kuwa maman bobo da kuma yayarta wato maman ahmed da ameera! sun riga da sun kulla alkawarin aure tsakanin bobo da ameera sbd son kulluwar zumuncinsu yayi karko batare da ya samu nakaso ba ta wannan hanyar! sarai bobo yana da labarin wannan abin,amma bai dame sa ba,sbd shima idan aka barsa bai san ta inda zai samo mata hudun nan ba dikda yadda mata da dama ke kawo masa hari!
A kuma gefe guda ma ga hajiya kaka da nata🤣 inda ita kuwa sbd soyayyarta da salmaty ta kafa masu kahon zuka kan lallai lallai sai ta hada salmaty da bobo aure sbd kamasa da tayi a kwanakin baya ya kura ma matasan kirjinta idanu batare daya sani ba! sannan kuma bugu da kari ita salmaty din da kanta ta samu kaka sbd soyayyar dake tsakaninsu kan bobo na burge ta ! wanda hakan yasa kaka bullo masu ta wannan hanyar!
sai kuma fa mai gayya mai aikin wato abban bobo da abokinsa wato baban salim da suma suka kulla alkawarin aure tsakanin yaran su sbd son dauwamar da nasu amintakar ta har illa masha Allah! wannan ne dalilin daya sa a lokacin da bobo ya tara iyayen nasa kan yana so a je masa gidan su teema sbd yanxu a shirye yake tinda yana da aikin yi dakuma muhallin zamansa!
wato abinda ma zai bama mutum tabbacin cewa bobo _MUNAFUKIN_ maza ne,dik kudin daya ke da shi! dakuma gidajen da mahaifinsa ya mallaka masa masu part part daban daban hakan baisa shi daukar ko guda daya ba!
sbd shi a nasa ra'ayin yafi son yaga daku nan matan nasa a jere suke reras guda hudu,idan yaso sai nasa part din ya zamana yana kallon ma matan nasa ta yadda zaifi jin dadin kallo idan ya hado su!
a lokacin ne abba,umma da kaka ko wannen su ya fiddo da nasa kudirin,amma sai kakan bobo namiji ya fito ya dire masu kan basu isa ba! babu wanda zaima jikansa auren dole idan har ba shine da bakin sa ya amince ba! aikuwa bobo cikin rawar murya batare da damuwar komai ba yace ya amince sbd ai shikam abin gama ta kai sa gobarar titi a jos wai💁🏻♀️
wanda hakan yasa cikin kankanin lokacin batare da damuwar komai ba aka hade ranar daurin auren bobo da mayayensa guda hudu reras kamar yadda yayi mafarkin samu tin bai kai haka nan ba!
ba karamin tashin hankali ba kuwa teema da bobo suka gafza sbd wannan batun daya fito a lokacin da auren su ya gabato! wanda saida bobo yayi mata jan ido kamin ta shafa masa lafiya sbd soyayyar datake masa!
su salmaty da su feena tare da ameera kuwa ko wannen su dama ba kanwar lasa bane a fagen kishi dakuma fitina! wanda suka hade dikkansu tare da teeman da itama ba hakuri bane da ita to kuwa tabbas akoi gagarumin aiki!
ba tare da bata lokaci ba kuma ko waccen su ta kware ta fannin girki,kula da miji da dai sauran abubuwan da ake bukatar ko waccce matar aure ta iya su kamin shiga gidan miji sbd ko waccen su so take ta zamtoh tauraruwa wajen bobo,batare da sun san tana din da gogo bobo yayi masu ba!
idan ka dauke wau tar dake yawo cikin kansu da kuma masifaffen kishi da kowa ta dasa ma ranta akan bobo to kuwa gaskiya matan nasa fes ne ko wannen su ba daga baya ba!
domin kuwa dikkan nin su suna da kyawun su da kuma halitta mai kyan tsari! kuma tarbiyarsu ma ba ragaggiya bace babu laifi dai dai gwargwado!
inda a lokacin auren ne daya gabato salmaty taji ta raina kanta,domin kuwa irin uban kayan dataji labarin iyayen feena da ameera suka zuba ma yaran nasu cikin gida ba karamin abu bane ba! sai kuma teema da itama dai iyayen nata rufin asiri ne tare da taimakon yayanta dake aikin gomnati suka samu aka harhada mata dik abubuwan bukata,amma da shike ta hannun damar kaka ce salmaty sai kaka ta daure mata gindi ta tatsi dik wasu kudade daga aljihun abban bobo ta aika ma maman salmaty aka sayi mata kayan gayu itama sannan hankula ya kwanta
yau takama ranar daurin aure!
comment,share,and vote plsssssssss😖