25

342 33 5
                                    

Sosai Juju ta canzawa Hajir har abin ya fara bata mamaki, duk yadda Hajir taso bugar ruwan cikinta ta kasa dan Juju tayi baya da ita sosai, ko hira me kyau bata bari sunayi balle hiran Yasir ya shigo ciki, zasu zauna wuri ɗaya a class idan sun fito kuma su tafi cafeteria suci abinci amma wani dogon hira baya shiga tsakaninsu har abin ya bawa Feenah mamaki, tun Hajir na gani kaman mood swings ne irin na Juju har tazo ta gane ba haka bane dan kuwa Juju na zagewa tayi hira da Feenah kamar yadda ta saba a can baya kafin zuwan Hajir, sosai Hajir ta shiga damuwa dan ita harga Allah tana son Juju, kuma abubuwan da take fadawa Juju ba tanayi bane saboda wani manufa ba, tana fadan abinda ke ranta ne kawai dan bata dauki hakan amatsayin laifi ko shisshige ba, dole ta tambayi Juju ko akwai laifin da ta mata ne ta daina sakin jiki da ita, inda ita kuma Juju tace babu abinda ta mata kuma bawai ta daina sakin jiki da ita bane karatu ne ke sha mata kai, haka Hajir ta hakura sukaci gaba da kawancensu sama sama.

A gida kuwa tsakanin Yasir da Juju komai normal, kaman yadda tace se sun gwada zasu gane hakan kuwa akayi, sedai ga mamakin Yasir tama fishi zaƙewa, sosai yasha mamaki dan beyi tunanin haka take ba, a zuciyarshi kuwa ba karamin dadi yaji ba dan ada yayi tunanin zata gaji da jarabar shi amma kuma se yaga tsaɓanin hakan. Ta bangaren Feenah kuma karatun ta kawai takeyi, yanzu tama daina kawo Mutabbir akai dan abinda tasa gaba shi takeyi, sosai take kokari a school har lecturers dinsu suka fara noticing dinta, wannan dalilin yasa idan za'ayi wani debate ko competition ko wani program haka suke sata a ciki dan tana cikin top 3 na set dinsu, inda Juju kuma ba'a rasata a top 10, tuni Feenah tayi suna a school dinsu har tutorials takeyi ma course mates dinta dama Juniors dinta, yayinda idan ana lecture a class sosai lecturers ke maida hankali kanta especially idan tana asking dinsu questions, they are always eager to answer dan kuwa reasonable questions take tambaya, ba karamin dadi Yasir yakeji ba dan kuwa yasan kudin ba'a banza suke tafiya ba, he's so proud of her and he always encourage her to do more, he always motivate her to move forward wanda wannan ke kara mata himma, duk wani association daya danganci course din da takeyi tana ciki, idan aka tashi yin abu a school tana gaba gaba, kwata kwata bata sanya saɓanin Juju da se Yasir ya tilasta mata takeyin wasu abubuwan, ita acewarta karatun kadai ma ya wadatar base ta damu kanta da wani kungiya ba kuma.

********

NIGERIA ABUJA,

A Abuja kuwa Mutabbir yayi nisa da aiki, hankalinshi ya kwanta yanzu, matsala daya yake fama da ita, shine na rashin mata, gashi baze iya zuwa ya fadawa tsoho yanason yayi aure ba dan kuwa ba za'a yarda a gida ba ya sani, wata uku kenan da abokinshi YK yayi aure, dan haka yanzu shi kadai ne a gidan, se kadaici duk ya dameshi, gashi yanzu wani shaye shaye da yawon zuwa club duk ya daina su, dan haka bashi da wani wurin zuwa chilling, kullum daga gida se aiki, babu abokin hira, wani irin muguwar kewar Feenah yakeji, koba komai she was once his wife kuma she will always be, dan kuwa shima ɓe cire rai akan dawowarta ba, a kullum addu'ar shi baya wuce Allah ya bayyanar da ita ta dawo gida cikin 'YAN UWAN ta, ta dawo gareshi, domin kuwa yama kanshi alkawarin cewar alokacin ne ze nuna mata soyayya wacce babu algus a cikinta, ada yasan yayi wauta ya kuma wulakanta amanar da aka bashi amma a yanzu kam ya gane kuskuren shi bugu da kari ga wani azababben soyayyarta dake mugun azabtar dashi, a kullum da ita yake kwana yake tashi, bashi da burin da ya wuce ya sake ganinta yasata a ido, get together din da sukayi a Kano ya kara daga mishi hankali ganin yadda kowannensu ya hakura da hadin da aka mishi harda brothers dinshi kuwa, toh idan su sunyi hakuri shi wanene da bazeyi hakuri ba, a lokacin daya shareta ya fita harkarta kaman yadda Mahbub da Walid sukayi da nasu matan da Feenah bazata gudu ba, amma shi seya zabi ya azabtar da ita da yunwa da bakin ciki ta hanyar hada party a gidanshi wanda yasan ya ajiye matar sunna a ciki, a duk lokacin da ya tuna se yaji ina ma ana maida hannun agogo baya, daya gyara zamantakewar shi da ita, amma ina, aikin gama ya riga ya gama, yanzu se zaman jiran tsammanin yaushe zata dawo, ta ina zata bullo, da lafiyarta zata dawo ko kuwa a'a, idan ta dawo zata yi marmarin komawa gidanshi ko kuwa zatace ita bazata koma bane, tambayoyi yake wa kanshi buba adadi, wanda duk bashi da amsarsu se ranar da Feenah zata dawo gidan.

FOUR YEARS LATER

Kuyi hakuri dani zanyi rushing din novel dinnan saboda wasu dalilai da kuma rashin samun lokaci da dai sauransu...

Don't forget to vote, comment & share...

Mhizzdaddy ✍🏻....

'YAN UWAN JUNAWhere stories live. Discover now