TABARYA....mai baki biyu
" kin yaudareni BAHIJJA, ni zaki rainawa wayo, ki mai dani SAKARAI, ki rik'a saka wasu abubuwa a jikinki, wad'anda kinsan Allah bai Halicceki dasu ba?" Jikinta rawa ya fara yi kamar mazari, "Ahamd dan Allah kayi hak'uri." Ta furta tana share hawaye. Katseta yayi, ta hanyar d'aga mata hannu....