Dangantakar Zuciya
A heart touching story
Yanda ƴammata ke mancewa da kansu da martabarsu a yayin bikin sallah, burinsu su haska kawai wajen samari, ko ina suka zagaya a yabasu su da kwalliyarsu, ajiye al'ada da addini dan kawai ace kaine wane, bin kowacce hanya wajen neman kayan bikin sallah. matan aure masu burin gasa da wance tayi kaza a gidanta...
Labari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.
Wannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magidanta da yawa basa son a haifa musu ƴaƴa mata, abin kuma zai baka mamaki...
Labarin mai nuni da muhimmancin biyayya ga iyaye, gujema son zuciya, soyayya, zuminci, tare da cakwakiya tsakanin yaya da ƙanwa akan son abu guda.
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita...
Bahaushen mutum yana da kyawawan dabi'u wadanda addinin Musulunci da al'adunmu su ka koyar damu. Sai dai zamani yazo da wani salo, mun wayi gari bamu da abin koyi da tinkaho sai AL'ADUN WASU. Shin hakan hanya ce mai bullewa???
Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru ga Maamu har zuwa lokacin da Allah Ya azurta mata tilon danta Awaisu. A daidai lokacin da take tunanin kyautatawa wadanda suka wahalta musu a baya sai Gimbiya matar dan nata ta murda kambun da ko iyayenta basu s...