AUREN DOLE
AUREN DOLE Zaune nake a katafaren falon gidansu wanda yake dauke da manyan kujeru na Alfarma . Tun karfe 4:30 Pm na yamma nake zaune a falon gidan na shafe kusan mintuna 30 bata fito ba , Ina zaune ina danna wayata saiga kanwarta maryam, ta shigo falon dauke da plate ruwa ne da kofuna akan plate din tace dani ina wuni...