Assalamu alaikum fatan kuna cikin koshin lfy ina fatan hakan. Ma sha Allah ya kuma kwana dayawa in sha Allah in Allah ubangiji ya kaimu 25 Watan September zan saki sabon littafina mai suna AKASIN ZUCIYA! Wannan labarin daga jin jigon labarin (sunan littafin) kunsan yana dauke da abubuwa mabanbanta ciki:
Qaddarar zuciya; a rayuwa za ka iya son wani a yayin da shi kuma bai da buqatarka, hakan kuma ba yana nufin ya tsaneka bane, dalili kuwa shi SO mai duka ne ke ɗarsawa a zuƙatan bayinsa, babu wanda ya isa ya saka wa wani son wani ba tare da ubangiji ya rubuta hakan ba. So kan komawa ta zamto kiyayya a inda kiyayya ke koma wa ta zamto soyayya, shi yasa ma Manzon Allah ya ce " kaso masoyinka kaɗan kaɗan don watarana zai iya dawowa maƙiyinka, sa'annan ya ci gaba da cewa ka ƙi maƙiyinka kaɗan don watarana zai iya zamto masoyinka"
Labarin dake tattare da tausayi, ban takaici, maida alkairi da sharri, son maso wani, kiyayya, nadama, tsantsan talauci, arziki, biyayya, sadaukarwa. Duk a cikin wannan littafin mai suna AKASIN ZUCIYA!
Ku biyoni sannu a hankali dan jin wacce qaunar ake tauyawa a cikin wannan littafin? In sha Allah zai zo muku nan ba da jimawa ba. Banyi alkawarin yin littafin nan free ba ban kuma ce na kudi bane duk dai yadda ta kama fatan zaku bini?.
Fatan alkairi a duk inda kuke.
Ayshkhair