Oh My Goodness!, ƊIYAR DR. ABDALLAH is really really interesting, educative and romantic. Salonnan dabanne kuma na yarda da rubutunki da narrative sensitivity ɗinki. Na daɗe ban ci karo da material mai matuƙar ƙayatarwa, ilimantarwa da sanyi nishaɗi irin wannan ba. The characters just stuck, tun daga farko har ƙarshe, babu abinda yake canzawa cike da ƙwarewa, iya magana, da sanya kowani magana a muhallin character ɗin da ya dace da shi. Lallai ke ɗin ta musamman ce. Ina fatan duniyar Makaranta littattafai za su lura da ke, you're really an inspiration to me, ba a matsayina na makaranci ba kaɗai, a matsayina na marubuci wanda ya fara rubutun littafi. Kin hau dani doki kin mallaka min linzami a hannuna, babu abinda ya rage min illa inja ragamar da kaina.
Godiya mara adadi da misali akan irin yadda kike kashe lokacin ki domin ilimantar da mu, nishaɗantar da mu, da faɗakar da mu cikin tarin ilimi da baiwa da Allah ya miki. Tabbas kowani ilimi is not a waste kuma duk mai bayyana ilimi ana fatan Allah zai bayyana masa hanyar shiga Aljannah. Duk da cewa naji haushin yadda labarin ya tsaya kamar yadda naji daɗin yadda yana ƙara tsayi yana ƙara armashi, idan har complete ne dan Allah ina buƙatar shi zan biya ko nawa ne domin in fanshe shi. Idan kuma Ongoing ne dai har wa yau bazamu fasa jira ba, muna godiya ƙwarai da gaske!
Allah ya ƙara basira da ilimi mai Albarka!...