A wani adabi na hausawa akan ce "Yaro masomin babba" kasancewar sune manyan gobe.
Mu yara ne, amman kuma rayuwar yarintarmu ta sha bambam da ta sauran yara,domin kuwa maimakon zuciyarmu ta cika fal da soyayya da kaunar juna sai akayi mata tushe da ƙiyayya mai karfi tamkar ginin da ya samu wadataccen kayan aiki.
Iyayenmu sun shayar da mu dauɗar gorar da ta sanya dankon zumunci mai karfi tarwatsewa tun kafin zuwanmu duniya, azanci na hausawa kan ce "Mai ɗa wawa" ƙwarai kuwa domin da ƙarfin tsiya muka shanye duk wata huɗuba da suke yi mana amman kuma ba su san da cewa sunyi ɓatan dabo ba,jini jini ne a ko ina yake ba a haɗa shi da bare hakan ya sanya muka fara lalube cikin duhu.
*******
A wani bayanin da Mamina tayi min Shakuwace da kusanci ya haifar da gaba mai tsananin gaske a zamanin da ya shuɗe tun kafin a san za a haife mu.....•"Shin dama Shaƙuwa da kusanci a tsakanin ƴan uwa yana haifar da gaba mai tsanani?"•
Tambayar da har yau na ƙasa samun mai amsa min dole sai da na nemi mai mayar dani tushe na binchiko tsohon labarin da aka jima da binnewa, labarin sai ya kasance tamkar shuƙar da aka dasa kullun ake bata ruwa. Iyayenmu sun shimfiɗa rayuwa mai cike da tsabta da abin sha'awa sai halacci ya rikiɗe ya koma ƙiyayya daga bisani faruwar wani abu ya zaburar da zuciyoyin ƴan uwa masu ƙaunar junansu,maimakon kishin ya tsaya iya kishi a tsakanin bal-bali sai abin ya koma gaba mai karfi a tsakanin wa da kuma kanin sa uwa ɗaya uba ɗaya"
Tafiya ce mai ɗauke da darussa daban daban a nahiyar kishiyoyin bal-bali ko in ce kishiyoyin sauri.Taɓarɓarewar danƙon zumunci ya zama ruwan dare a duniyar iyayen mu, Tafiya ce mai cike da kalubale, sarƙaƙiya uwa uba hassada yana kuma nuni da mu'amular maƙotaka da kuma zamantakewa, A wani ɓangare babban jigo ne bisa ga tarbiyyar ɗiya.
FADILA IBRAHIM
Diela_Writer
https://www.wattpad.com/story/375098656