G.W.A✍
*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.*
```13/05/2021M.```
```01/10/1442AH.```
_Ƙungiyar Masu Yi Dan Allah *(GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION)* na yima dukkanin musulman duniya Barka da Sallah tare da fatan alkhairi, da addu'ar Allah mai girma da buwaya ya karɓi ibadunmu, yasa munyi ibada karɓaɓɓiya, Allah yasa muna da rabo cikin ayyukanmu na alkhairi, Allah ya nufe mu da ganin sallar baɗin baɗaɗa da cikakkiyar lafiya, Idan kuma Allah bai hukunta zamu ƙara gani ba Allah yasa mu cika da imani._
_haka zalika ƙungiyar na roƙon Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, Allah ya zaunar da ƙasarmu lafiya da sauran ƙasashen musulmi baki ɗaya. Allah yaiwa kasuwancinmu albarka, Allah yasa muyi bikin sallah lafiya mu gama lafiya, Allah ya maimaita mana._
*AMEEN SUMMA AMEEN, BARKA DA SALLAH.*
_Haka Kuma Ƙungiyar na miƙa goron albishir zuwa ga masoyanta, bayan hutun azumi da ta dawo insha'Allahu a ranar 17/05/2021 huɗu ga sallah kenan, zata ci gaba da sakar maku littafanta sababbi dama waɗanda ake kan ganiyar yi._
_Ku kasance da Gaskiya Writer's Association a ko da yaushe domin ilimintarwa, faɗakarwa, tunatarwa tare da Nishaɗantarwa._
Saƙo Daga *UMMU RAMADHAN✍*
(C.E.O).
______________________
Zaku iya Bibiyarmu a shafukanmu na
*FACEBOOK:*
Gaskiya Writer's Association.
*WATTPAD:*
GaskiyaWritersAsso.
*BAKANDAMIYA*
Gaskiya Writer's Association.
*TELEGRAM:*
_kuna iya tura saƙonku na shawara ko ƙorafi akan:_
*GMAIL:*
Gaskiyawritersassociation@gmail.com
*OR*
09030398006/08088360867.
{Walfere & President}.