A yayinda rayuwa tayi wa wani dadi a lokacin ga wasu kam tafi rana zafi, tafi wuta kuna haka tafi bagaruwa jima.
Gaba daya rayuwa ta a yanzu dai b zan karar da wani abu wai shi farin ciki ba, rayuwa nake yi kawai bisa doron kaddara da jarrabawa inda kullum nake kara karfafawa kaina gwiwa cewa komai ze wuce, duk da na san tunani ne kuma mafarkin da baze taba zama gaskiya ba, sedai ki fadi da son zuciya sun sa na kasa yarda da wnn gaskiyar.
Ba ni da muni, ba nakasa babu mummunar kama amma ana min kallon nakasasshiya, abar tausayi ga masu imani yet abun gudu ga masu son zuciya.
Gidan aure na ya juya zuwa wani karamin sansanin yaki, rayuwar aure na ta koma Wani tragedy life, komai ina yin sa ne bisa rashin dadin rai saboda rashin kwanciyar hankali, ba kuma komai yasa hakan ke faruwa gare Ni ba face *RASHIN HAIHUWA*, Kaddarar da bani na ɗorawa kaina ba, yanayin da in da za'a bani zabi so miliyan ba zan zabi kasancewa a ciki ba, sedai ya zan yi tun da haka Allah yaso gani na????
_Awwn, so heart broking, let's follow khadeejah in her marital life muji meke faruwa☺️