NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.
GININ BAKIN TEKU
BOOK 2
RUBUTAWA
QUEEN MERMUE.
SADAUKARWA...LUBABATU MAI TAFSEER.
_Ba shakka zuciya ta riga da ta bushe k'auye, hawaye sun k'afe tamkar k'afewar alk'alami. Ba ni da sauran tsoro a tattare da ni, ba ni da sauram neman sulhu. Abubuwa ukku da nake tak'ama da su Laila ta yi nasarar wargazasu a duniyata, ban shagalta ba, ila, na canja launi ne daga mai neman shiryar Laila izuwa ga mai neman halakarta._
****
"Ba ni da kowa a duniya, na zo nan ne dan neman halalina. Dan Allah Hajiya ki taimaka mun kada ki bar ni anan."
Ta ajje kyakkyawan murmushinta da kan batar da tsufa da damuwar da take shimfid'e a fuskarta. Ka na, ta iso har a gabanta ta dafa kafad'unta.
"A wancan lokacin na yi dana sani matuk'a na taimakon wata da ta siffanta da kamannunki, ko da yake..."
Ta mayar da jelar gashinta da ke yawo kan gadon bayan, ta gyara zaman farin madubin da ya k'ara fito da nagarta ta ci gaba.
"Kasancewarki 'yar k'asata Nigeria, ba zan iya jurar ganinki a cikin baban birnin Turkiya a walak'ance ba... Ki zo gare ni zan taimakawa rayuwarki."
Ta ajje nunfashi mai nauyin gaske, ta k'ara matse hannayenta a tsakiyar cinyoyinta. Ta dago a hankali su ka yi ido da ido.
'Eng. Azumi Saraki har yau ba ki canja ba, har gobe ke mai son alheri ce.'
Nandra Jayyid Jamaica ta fad'a acan k'asan ruhinta...
*ASSALAMU ALAIKUM MY FIFUL*
GA NI NA ZO DA K'ARFINA, GBT YA ZO MUKU DA ZAFINSA...KU KASANCE A TARE DANI DAN NEMAN CI GABANSA.
BA KYAUTA BANE. INA BUKATAR TUKUICI A WANNAN KARON.
DOMIN KUWA YABA KYAUTA SHINE TUKUICI
DOMIN K'ARIN BAYANI KU TUNTUBE NI TA WANNAN NUMBER 09035218878