AssalamAlaikum zuwaga masu karatu ina fatan kowa yana lafiya.Ga wani muhimmin sako,
Wannan bashi band karo na farko,danake bayani akan cewar Ni Rubutuna bana rubuta Batsa,ma'ana Bana rubuta abinda bai dace ba,bazai yiwu ba don kawai zanyi bayanin daren farko na maaurata inzo in fayyace komai in rubuta rashin kunya,Agaskiya bazan iya ba ina rubutu ne saboda in fadakar,Bawai don in sakawa mutane sha'awa ba.
Dayawa daga masu karatun nan basuda aure to meye ribata aciki daakeso in tayarwa da mutane hankali?.
Sakonni sunata riskata nawai bana saka soyayya acikin rubutuna bana saka romance yadda yakamata,Haba jamaa Rubutun nan fa babu wanda baya karantawa daga iyaye,Kanne zuwa yanuwa da abokanan arziki,shikenan Mutane suna ganina da mutumci suna ganin girmana suna bibiyar rubutuna kuma kawai sai suga ina rubuta shirme?To bazai yiwuwa gaskiya,ni bana kauce hanya don kawai in farantawa Bayin Allah ko in sami daukaka inyi suna,gaskiya kenan,Don Allah mu lura,wannan bashi bane karo na farko danake fadar hakan,indai kinsan/kasan cewar burinka/ki karanta shashanci ko batsa a labari ne to labarina ba irin naki bane.
Bissalam