https://arewabooks.com/chapter?id=63b3f086246eaf4832d039ce
"Inna wai Yaya Khalil har yanzu bai dawo ba?"
"Kaji yarinya kamar tare muke dashi, dan kinibibi zaki dameni"
Aisha tasa dariya tana cewa "Allah da gaske tambayarki nakeyi Inna"
Inna tayi mata banza,
Suna zaune Khalil ya shigo, ta tashi da katon cikinta tana shirin zuwa rungumeshi Inna na shirin guduwa ta bangaje Inna bata Sami ba Inna ta baje a k'asa, Aisha ta toshe baki da hannu zatayi dariya tace "sorry Inna"
"Wata uwar harara Inna ta zabga mata tare da cewa "soro"