PART OF OUR DESTINY.
Ya kasance yana jin kansa cewa shiba NAMIJI bane, duk da kasancewar sa acikin halittar jinsin MAZA, amma saidai yana da wani tazara me tarin yawa tsakaninsa da zama CIKAKKEN NAMIJI wanda yasan itace kalma d’aya tak arayuwarsa da bazai tab’a amsawa ba, rayuwarsa gaba d’aya RAUNI ce, akuma cikin wannan raunin, alokacin da yake jin rayuwar tafi mishi dadi, alokacin K’ADDARARTA dake surke da nashi ke soma harbawa acikin jinin jikinsa, akowace rayuwa akwai K’ADDARA acikin kowacce K’ADDARA kuma akwai SOYAYYA, domin yayi imani cewa K’ADDARARSA shine soyayyarta, soyayyar da yake jin ta acikin kowani bugun zuciya da shigar numfashinsa, duk da yasan bazai tab’a kasancewa d’aya daga cikin jinsin da zasu amfanarba kasancewar sa mutum me BABBAR TAWAYA, haka kuma mutum me B’OYAYYAR NAK’ASU, aduk rayuwarsa baisan SO ba sai akanta, saidai alokacin da yake jin ta zamo duniyarsa, adaidai wannan lokacin kuma WATA ZUCIYAR daban ta kasance tana rayuwa ne kawai saboda ita, ya kasance wani mutum ne shi na daban, daya kasance DABBOBI sunfi bashi farinciki fiye da komai, saidai saudayawan lokuta, me yake so? menene alkiblarsa? way’annan duk wasu abubuwa ne da bai sani ba, acikin rayuwarsa kuwa yana da wani TABO na kasantuwarsa FASIK’I, amma akowace rana yana numfashi ne da sanin an haliccesa da wani abu guda, wannan abun kuwa shine soyayyarta, shi ba koyan sonta yayi ba, halitta masa shi akayi acikin zuciyarsa, kamar yanda JINI ke gudana acikin jikin duk wani d’an Adam me RAI haka SOYAYYAR TA ke kewaye da duk wata jijiya dake cikin jikinsa.
TAE da kuma EMRAAN DUKA ZUK’ATA guda biyun kwana suke da tashi acikin muradin da suka san cewa duk wani kwanan duniya K’ADDARARSU nesanta su take da cikar BURIN SU, shin acikinsu WAYE K’ADDARA zata bawa DAMA TAAREEQ ATTOM EL-FAROUQ ne ko kuma EMRAAN EL-FAROUQ ATTOM da har yanzu yake kokonto tare dakin yardar cewa SHI ma NAMIJI NE?