RAYUWA TA.....
ƙaddara ta
SHIMFIƊA
RAYUWA DA ƘADDARA wasu kalmomi ne guda biyu masu sauƙin ambata a baki amma kuma,masu wuyar fahimta. Ko wane ɗan Adam da yanda ubangiji ya hallice shi,ya ƘADDARO yanda RAYUWAR shi zata kasance tun daga haihuwa har ya koma ga mahallicin shi. Mutane da dama na shan matuƙar wahala a RAYUWAR su saboda rashin amsan ƘADDARAR RAYUWA a yanda tazo masu wanda shi kan shi gaba ɗaya RAYUWAR ɗan adam ba'a bakin komi take ba amma ga wanda ya fahimta kenan. Yarda da ƘADDARA mai kyau ko akasin hakan na daga cikin rukunan imani. Saboda haka,a duk halin da bawa ya tsinci kan shi a duniyan nan ya rungumi ƘADDARAR RAYUWAR shi da hannu biyu cike da imani.
Yana nan tafi nan bada jimawa ba