Kina tallabe kunnuwan maigida ki rera masa wakokin soyayya lokaci zuwa lokaci idan kuna cikin nishad'i, ko kina jiran ya ji a bakin wad'anda suka fiki zakin murya Jummala??
LIKITAR MA'AURATA... ✍️✍️✍️
Zanyi kira zuwa ga mazan da suke cutar da matan su da dama zaka samu mace ta kawo kukan mijin ta baya biya mata bukatar aure musamman wajan kwanciya hakan ɗan uwa bai dace ba kuma cutarwa ne.
Yana daga cikin abinda yasa mata suke fadawa zina shine idan mijin su baya basu kulawa baya biya musu bukatar su sai su fara bin maza yadda bukatar sa zata biya.
Haba ɗan uwa duk kai ka jayo ka sani Allah subhanahu wata'ata ya baka kiwo wanda kuma sai ya tambaye ka gobe alkiyama akan wannan kiwon da da baka.
Idan ita bata biya masa sai yace ai Manzon Allah sallallahu Alaihi Wasallam yace duk wadda ta kauracewa mijin ta Allah yana fushi da ita.
Tabbas haka ne amma ka sani kaima idan baka biya mata bukatar ta ba amma sai ya kama ka kuma Allah baya barin wanda aka zalunta domin zalunci musamman irin wadannan matan masu ƙarfin sha'awa wallahi maza kuna cutar da su.
Dan haka kaji tsoron duk lokacin da matar ka ta bukace ka idan har zaka iya ka biya mata bukatar ta ko ta kwanciya ne ko ta kuɗi ko sayan kaya ne wannan wajibi ne akan ka ko tarbiyya kaine zaka ɗora ta hanya daidai amma idan ka juya mata baya dole zaka ga sauyi tare da ita.
Kema ko biya masa tashi idan ya bukace ki kuma ki riƙe masa sirrin sa kada ki faɗa ma kowa sirrin ki sai wanda kika yarda dashi domin mutane sai a hankali.
Dan haka mu gyara.
Allah bamu ikon gyarawa