🧵🧵🧵🧵🧵
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
🧵🧵🧵🧵🧵Writing by
ALIYU H ISHAQ
(fast class)________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comDAGA MARUBUCIN
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now
↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)IG, haidar_Ishaq_576
Email, haidarishaq@gmail.com
WATTPAD, @FASTCLASS
Facebook, haidar ishaq
🅿 30↔35
...............Lokacin da wadannan birirrikan suka yi wa sadauki Razmir kawanya sai aka fara kallon kallo tsakanin su shi bai motsa ba suma basu motsa ba
A wannan lokacin gimbiya Numaira tana hannun wani gwagwgwan biri ya riketa tamkar kadan gare sai lilo take idanu sadauki Razmir ya zuba masa yayin da yake lila gimbiya Numaira kwatsam sai gani sadauki Razmir yayi wannan biri yayi wulli da ita zuwa wani bangaren wani birnin nehh ya chafe ta haka suka yi ta wulle wulle da ita suka raba masa hankali na karshene ya wulla ta wani bangare da ba kowa a gurin kafin ta dira a kasa sai ji tayi an chafe ta tana reto
Da sauri sadauki Razmir ya kalli sama abinda ya gani nehh ya matukar dugunzuma masa hankali ba komai bane ba illah wani zabgegen gwagwgwan biri girman birin ya kai girman tsauni ya kasan ce yana da murkushen kai da alama dai shine shugaban su
Kafin sadauki Razmir yayi wani yunkuri tuni wannan biri yayi wata kururuwa kawai sai gani yayi wadannan sun taso masa baki daya
Cikin bakin xafin nama yayi wata katantan wa a sama ya tsallake birirrikan kimanin su hamsin kafin ya duro yasa takobi ya labtawa wani Sara a kafada ji yayi tamkar ya sari karfe sai ji kake kal yana dirowa a tsakiyar su aka ruguntsume da azababben yaki ya zama na cewa yana kai musu Sara da suka cikin bakin zafin nama juriya da bajinta suko ba abinda sukeyi illah kawo masa suka da zakwa zkwan faratan su suna kawo masa mangari yana kaucewa idan yayi wata katan tan wa a tsakiyar su saidai kaga ya baza su amma kafin yayi wani Abu sun kuma yanyameshi
Saida suka shafe sa'a biyu suna wannan artabu amma dayan su bai sami koh da nasarar lakutar jikinsa ba haka shima ya kasa kashe ko da biri daya wannan abin nehh ya daga masa hankali San yasan a ko da yaushe zai iya gajiya su cimmasa nan ya kara zage dantse amma ba wani chanji
Daga chan gefe daya kuwa wannan gwagwan birin ne ruke da gimbiya Numaira tana reto yana kallon wannan bakin artabu da ake yi ba karamin mamaki yayi ba da ganin sadauki Razmir ya kai wannan lokacin yana fafatawa da dakarun sa kuma yana raye koh da aka kuma shafe wata Rabin sa'ar yaga ba wani chanji kawai sai ya takarka re ya kwarara uban ihu mai matukar firgitarwa lokaci guda wadannan birirrika suka janye daga gun sadauki Razmir suka yi masa kawanya suna masu muxurai kamar sa ci babu
Shugaban nasu nehh ya kalli wani biri ya wulla masa gimbiya Numaira shi Kuma ya shigo tsakiyar filin yana tafiyar kasai ta saida ya rage baifi saura taku ashirin ba tsakanin sa da sadauki Razmir ba nehh ya rugo da gudu zuwa kansa
Ohoho mai karfi sai ALLAH ya isa a lokacin da wannan shugaban nasu ke gudu akan kasa gabaki daya dajin sai ya kama girgiza saida ya rage baifi saura taku uku ba tsakanin su ba a wannan lokacin sadauki Razmir yana tsaye ya ruke takobin sa cikin yarda da kai
Shugaban birirrikan nan nehh ya daka wani wawan tsalle a sama ya ware hannuwan sa duka biyun ya kawowa sadauki Razmir duka da dukkan karfin sa da nufin ya talitse sa baki daya acikin kasa
Cikin bakin zafin nama sadauki Razmir ya kaucewa wannan hari ta hanyar daka tsalle daga inda yake zuwa wani bangaren
Lokacin da hannun birin nan ya sauka a kasa nan take ya nutse a cikin karkashin kasa sanda ya zare hannun sai ga shi ya haifar da wani rami mai zurfin tsiya yana wai gawa bayan sa yaga sadauki Razmir a tsaye kuma a raye nan take mamaki ya turnukeshi dan shi tunda yazo duniya bai taba kawo wa wani mahaluki irin wannan hari yasha ba sai yau su Kansu yaran nasa sunyi matukar mamaki
Cikin bacin rai ya juya ya fuskanci sadauki Razmir da yake tsaye kyam yana ruke da takobin sa kawai sai ya Kuma zare wani gatari ya kurban wawan ihu yayi kan wannan biri shima birin kururuwa yayi yana mai dukan kirjinsa Alamar rantsuwa yayi kansa da mugun gudu
Suna haduwa suka kachame da azababben yaki mai matukar ban tsoro shirin birin na kokarin ya suri sadauki Razmir ya daga shi sama shikuma ya wanzu yana mai zullewa tare da kai Sara da suka tako ina cikin bakin zafin nama amma duk inda ya Sara saidai kaji karar karfe ta ta shi kal tamkar karfe da karfe ne suka hadu sai da suka shafe sa'a daya suna fafatawa a wannan lokacin nehh sadauki Razmir ya fara gajiya kuma a sannan nehh wannan biri ya samu nasarar dankara masa wani wawan naushi a kirji sai da yayi katan tan wa sau uku a tsaye sannan ya zube kasa a yayin da jini ya furzo daga bakin sa koda wannan birin yaga ya samu wannnan nasara kawai sai ya kalli yaran sa yana mai kwarara uban ihu yana dukan kirjinsa suma ihu suka sa suna masu yi masa jinjina
A wannan lokacin sadauki Razmir yana gani dishi dishi sakamakon kunburar da fuskarsa tayi lokaci guda a hankali ya daga kansa abin da ya gani nehh ya matukar tashar masa da hankali ba komai ya gani ba face gimbiya Numaira wadannan birirrikan sun bankareta a kasa yayi da wannan shugaban nasu yayi kanta gadan gadan yana mai yin ihun nasara
Cikin bakin zafin nama sadauki Razmir ya mike ya suri takobinsa ya falfala da azababben gudu kafin kace wani Abu ya kamo wannan shugaban nasu wawan tsalle ya Daka ya dira a bayan sa ya kama hawa jikin sa tamkar yana hawa bishiya cikin kankanin lokaci ya isa kafadar wannan biri yana isa ya daka wawan tsalle ya dira a kansa ya daga takobin sa ya luma ta acikin kwayar idanun sa take idan ya Burma ciki birin ya kwarara uban ihu sakamakom tsananin zafi da zugin da yaji nan take ya haukace yana kokarin ya wantsalo da sadauki Razmir amma ina kafin yayi wani yunkuri tuni sadauki Razmir ya Kuma luma masa wannan takobi a daya idan take shima ya y burma ciki jini ya yi tsartuwa
Wani wawan mangari wannan birin ya kawowa sadauki Razmir da niyyar ya wantsaloshi cikin zafin nama sadauki Razmir ya daka tsalle a saman ya dankara masa wawan Sara a kai take kan nasa ya rabe gidan biyu ya tafi kasa luuuu sai ji kake Tim ya fadi kasa matacce
Shiko sadauki Razmir akan kafafunsa ya diro yana ruke da takobin sa da ta rune da jini yana mai kallon sauran birirrikan yana jiran koh ta kwana.............
Wannan kenan muje zuwa
A gsky ina jin dadin son da kuke nunawa wannan book din Kuma ina jin dadin comment dinku ALLAH ya bar kaunaVote
Comments and sharedWhatsApp number 08143314152
By fast class
YOU ARE READING
SADAUKI RAZMIR
AdventureAdventure story lbr nehh akan wata budurwa da wani matashin saurayi abin dai sai Wanda ya gani