Turf out

226 26 11
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.

                    *♡MANAR¸.•💥*

               

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._

                                06.

#Turf out   
   
        Kamar wanda za ta tashi sama saboda saurin da take ta dunga ratsa compound d'in tana tafe tana zabga mita,ta tsaya balcony tana knocking kamar za ta b'alle k'ofar apartment d'in,Ruqayya mai aikin gidan ta bud'e mata,tana ganinta ta fara gaisar da ita da girmamawa,fuskar Dadda a tsuke ta amsa ta wuceta fuu,tun kafin ta k'arasa parlon take kwaloma Abba dake zaune kira "Yaro!" Abba yayi saurin waiwayawa ya kalleta yana sakin fuskarsa yace "sannu da zuwa Hjy" tace "yawwa" ta tsaya a tsaye tana k'arema parlon da occupants d'in cikinsa kallo,Mama ta had'e rai kamar wanda taga mutuwarta da kyar ta daure tace "sannu da zuwa Hjy" sakin baki Dadda tayi tana kallonta kamar wanda akayi pausing d'inta,for about 3 minutes tana haka then tayi mitsi² da idanu tace "ni dai yau ina ganin gulma iri²" d'auke kai Mama tayi saurin yi bata sake magana ba sanin a ko wane irin lokaci Dadda za ta iya tsigaleta yasa ta yima su Deejah alamar su bar gurin sanin,da sauri suka mik'e suka wuce sama,Abba yace "Hjy bismillah ki zauna" saurin girgiza kai tayi tace "um'um! Da ka ganni nan ba zama ya kawo ni ba,k'aran d'anka dai na sake kawo maka" Abba bai iya kallon fuskarta ba ya zubawa guri d'aya idanu yace "wanne daga ciki?" Da sauri Dadda ta kallesa tace "yo wa kake tunanin nake nufi idan ba Mamman ba? Kaima kamar baka san wanda zan kawo maka k'aransa ba?" Gyara zamansa Abba yayi yace "wani abu ya sake yi miki?" Dadda ta fara matsar idanu tace "yo akwai ranar banza da bazai je ya sani magana ba?" Abba yayi ajiyar numfashi yace "ki zauna bari na kirasa" zaunawa Dadda tayi tana girgiza k'afa,tana d'agowa za tayi magana suka had'a ido da Mama,ta tsuke fuska ta d'auke kanta ta fara mita,shi dai Abba bai ce mata komai ba yana ta gwada kiran Waleed,sai da ya masa kira ya kai biyar duka ba ya tafiya,then akace masa wayar a kashe yake,ya d'ago kansa ya d'an kalli direction d'in Dadda yace "Hjy ina ga sai dai mu bari zuwa da safe idan ya shigo" wani kallo Dadda tayi masa a fusace tace "ban gane mu bari har zuwa da safe ba? Anya ma ka kira shi kuwa?" Abba yace "na kira wayoyinsa duka a kashe" sakin baki tayi ta kafesa da idanunta,can kuma sai ta gyad'a kai tana mik'ewa tsaye tace "Allah kaimu,ai dai safiyar zai yi idanma tunaninka ka hanasa zuwa,zan dawo ne har sai na ga abunda ya turewa buzu nad'i" tana fad'a ta nufi k'ofa,Abba ya d'aga kai ya bita da kallo yace "sai da safe Hjy" bata tsaya amsa shi ba tayi ficewarta tana mita,da kallo Mama ta bita sanda ta fita ta tab'e baki k'asan ranta fari k'al dan murnan rashin samun Waleed da Abba baiyi ba a waya. A b'angaren Waleed kamar ya san abunda zai faru kenan yana fitowa daga apartment d'inta bai ma fara nufar hanyar gidansu ba ya shige motarsa ya bar gidan,wayoyinsa duka da ya san za'a iya nemansa ya danna su flight mode,ba shi ya dawo gidan ba sai after 10pm,yayi parking ya fito ya wuce cikin gidan,da sallama ya shiga though bai yi tsammanin samun mutum d'aya da yake ido biyu ba,Abba dake zaune parlon yana kallon news a Aljazeera ya amsa ba tare da ya juya ya kallesa ba,Waleed ya d'an kalli direction d'insa yanayin zamansa kad'ai yasa gabansa fad'uwa tun ma bai yi masa magana ba,ya danne ya k'arasa shiga ya gaishesa zai wuce sama Abba ya kirasa "Waleed!" Juyawa yayi at the same time yana amsawa,Abba yace "daga ina ka fito dai² lokacin nan?" Kansa a k'asa yace "Abba! Na je duba wani friend d'ina ne ya yi accident" d'ago kai Abba yayi ya kallesa yace "dubiyan ne kuma sai kamar wannan lokacin kake dawowa gida? Me yasa baka kwana can ba ka tayasa jinyar?" Shiru yayi da farko sai da Abba ya gama masa fad'a sannan yace "i'm very sorry Abba,amma ba yanzun na dawo ba,na tsaya bakin titi wajen mai kiosk" Abba yace "saboda ka san ka yi laifi a gida ko? Shi yasa ka bari sai yanzun ka shigo,tunaninka duka munyi bacci ko me?" Saukar da kansa ya sake yi,Abba ya gyad'a kai yace "kaje! Za mu had'u da safe,tunda kai ba ka jin magana,jeka Allah tashe mu lafiya.." Jikinsa a sanyaye ya yiwa Abba sallama ya wuce sama. Da safe as she say tun kafin 7am Dadda ta fito daga d'aki taga Manar kwance kan pray mat,har ta wuce ta dawo ta fara mata magana,Manar da ba nauyin bacci ne da ita ba ta bud'a idanunta tana kallon Dadda cike da b'acin rai,Dadda tace "yawwa sai ki had'a mana abun kari kafin naje mu gama na dawo ko?" Da sauri Manar ta tashi ta zauna tana kallonta tace "ina kuma za ki da safiyar nan? Ko fa tashi babu wanda yayi yanzu" wani kallo Dadda ta wurga mata a fusace tace "yo to ni ina ruwa na da babu wanda ya tashi,idan naje ni kuma ce miki aka yi barinsu zanyi suyi ta baccin asarar nan?" Manar tace "dan Allah dai ki bari har rana ya gama fitowa" wani kallo Dadda ta dunga mata a kaikaice kafin tayi gaba tana fad'in "ke dai wannan yarinya ina ga ba ki da hankali ko d'is,idan ba haka ba ina k'ok'arin k'watar hak'k'i na kice na zauna har rana yayi,saboda ga asararriya wacce uwata tace min jeki kya gani ko dan kin maida ni sakarya?" Har ta fita bata fasa mitar da take ba,Manar ta tab'e baki ta koma ta sake kwanciya abunta. Tana tafe tana mitar maganar da Manar tayi har ta tsaya balcony,za tayi knocking kenan Amaar ya bud'e k'ofa zai fito,yana ganinta yayi murmushi yace "Hjy Dadda barka da safiya" washe masa baki tayi tace "ka tashi lafiya?" Yace "alhamdulillah!" Tace "fita za'ayi ne?" Yace "a'a zanje na amshi sak'o bakin get na dawo" tace "aihooo! To sai ka dawo" har ya yi gaba tace "uban naku yana nan ko ya fita?" Bai tsaya ba yace "yana nan" gyad'a kai tayi ta juya ta shiga,bata tarar da kowa a parlon ba,ta zauna shiru tana jiran taga wani ya fito,kusan mintunanta sha biyar a gurin sai ga Abba ya fara sakkowa cikin shirin fita office yaga mutum zaune ya k'arasa,fuskarsa cike da mamaki ya dunga kallon Dadda kafin yayi magana "Hjy" Dadda dake zaune gyangyad'i ya fara d'aukarta tayi firgigit ta farka tana ganin Abba tayi salati,Abba dai sai binta yake da kallon mamaki,ya daure yace "Hjy ba dai a nan kika kwana ba?" Tace "a'a ni kuwa ya za'ayi nazo na kwana nan da girma na? Sammako dai nayo kada d'an banzan ya fice baka masa fad'a ba" Abba ya gyad'a kai yace "bari na kirasa" da sauri Dadda tace "ya dawo gidan ne?" Abba yace "Ehh! Ya dawo tun dare" baki sake Dadda ta dunga kallon Abba tace "kuma amma baka sa an kirawo ni ba tun daren?" Abba yace "bari dai nayi dama sai da safe muje har can gidan mu sameki,saboda bai dace kun fara bacci mu tashe ku ba" da sauri Dadda ta katsesa tace "ku same ni ko dai ku fice tunda ga shi har ka gama shirinka za ka fita,ba don Allah yasa na ganka ba da shi kenan ka gudu ka cuceni ni" murmushi Abba yayi cikin zolaya yace "Hjy da na yi niyyar fita ai baza ki san na tafi ba" tace "Iiiiiihhh! Saboda me ba zan sani ba?" Yace "ko da na fito yanzun bacci na sameki kina yi fa" wani kallo ta masa tace "a'a mutuwa dai kaga ina yi" murmushi ya sake yi yace "bari na taso shi" tace "toh ko kai fa" ya wuce sama yana sakin murmushin halin Dadda,bakin k'ofar d'akin Waleed ya tsaya yayi knocking,Waleed da fitowarsa wanka kenan yana shiryawa yace "who's there?" Abba yace "sai ka bud'e za ka gani" shiru yayi yana tunanin me zai kawo Abba d'akinsa kuma a dai² lokacin,ya daure bayan yaje gaban press ya d'auko jallabiya mai short hand ya zura ya k'araso ya bud'e k'ofar,kallonsa Abba ya dunga yi kafin ya juya yace "follow me" a bayan ya biyosa suka sakko,tun daga nesa yake kallon Dadda suna k'arasawa ya d'aure fuska yace "ina kwana" a fusace tace "bazan amsa ba" fakar idon Abba yayi ya d'age mata shoulders had'e da tab'e baki,ya nemi guri ya zauna yana gaisar da Abba,ya amsa yana kallonsa kafin yayi magana Dadda tayi wuf tace "yawwa yanzu naji batu.. Yaro tunda Allah yasa ka taso d'an ban zan a gaba maza ka tambayesa laifin da na masa yake zuwa yayi min d'iban albarka ko da yaushe!" Kallonsa Abba yayi yace "me ya faru tsakaninku!" Waleed dake kallon Dadda ta gefen ido yace "nothing Abba" saurin katseshi Abba yayi yace "don't tell me nothing.." Wani kallo Dadda ta musu fuskarta a d'aure tace "a'a! Ban gane wannan yare da kuke ba,ya za ku sani gaba ku juya baki kuna magana,ko dai kuyi hausa ko kuma kuyi larabci,amma dai wannan shegen yaren da babu dad'i ni ba na sonsa gaskiya kuyi wanda nake ji tun iyaye da kakanni.." Kallon Waleed Abba yayi yace "da kai nake magana ka min shiru" Waleed yace "babu komai Abba" Abba da ya kafesa da ido yace "babu komai za ta kawo k'aranka?" Da sauri Dadda tace "kuji min munafukin yaro? Dama abunda kace kenan dan kada naji? To Allah ya toni asirinka" ta juya tana kallon Abba tace "tunda bazai fad'a ba ni ai sai na zayyana maka abunda ya faru ko?" Abba ya gyad'a kai,kaf Dadda ta kwashe abunda akayi da wanda ma ba'ayi ba ta fad'awa Abba,Amaar dake dawowa bayan ya karb'o sak'on ya bud'e k'ofa,tun bai k'arasa shiga ba ya fara jiyo maganar Dadda tana fad'in "yo k'arya zan maka da girmana? Ba'a yi haka ba?" Wani kallon gefen idanu Waleed yayi mata bai ce komai ba,Abba ya zuba masa idanu sai kallonsa yake bai ce komai ba,Dadda tace "ina fad'a maka Yaro d'an nan na-ka bai ko ji tsoron Allah ba bare ya tuna ni na haifi ubansa ya daddage ya dunga surfa min masifa,ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sai da yayi min tass kafin ya barni ya fita" Amaar ya girgiza kai yayi sallama direct bai tsaya ba ya nufi staircases,da sauri Dadda ta kalli Abba tace "yo Allah na tuba wannan yaro dan fodiyo ma yana gurin lokacin idan ni na masa k'arya ai akwai shaidu a gurin ko? Sai ka sa a kira su d'aya bayan d'aya ka tambaye su" Amaar yana jin ta ce haka da sauri yana had'awa da sassarfa ya fara haura matakalar benen zai yi sama,Abba dake kallon Waleed wanda ya sunkuyar da kai ya kwalo masa kira "Amaar!" Cak Amaar ya tsaya a gurin da yake,Abba yace "come back" badon ya so ba ya juyo ya kalli Dadda dake zayyanowa Abba bayani har sannan ta k'i yin shiru,ya k'araso ya zauna kusa da Waleed yace "here i'm Abba" Abba yace "ina son ka fad'a min abunda ya faru jiya tsakanin grandma d'inku da d'an uwanka" sunkuyar da kansa yayi yana jan numfashi a hankali,Abba yace "kai nake saurare" a nutse Amaar ya juya baki cikin harshen nasara ya fara fad'awa Abba abunda akayi,kafin ya kai k'arshe Dadda ta k'ule a fusace tace "ni dai yau ina ganin ta kaina,dan masifa duk wanda zai yi magana sai ya canja yare saboda kun san ba ji nake ba,salon a cuceni a ba-ni rashin gaskiya,ko dan me yasa kuke min haka?" Saurin kallonta Abba yayi kafin yace da Amaar "fad'i da hausa" tsaf Amaar ya maimaita abunda ya faru da hausa,Dadda ta saki baki tana kallonsa tace "kuji min munafuki! Wato nice nayi k'arya kenan? Allah yaso ai akwai y'an albarkana a gurin,tunda shima d'an fodiyon ya zama magulmaci Yaro ai sai ka aika a kira takwarorina,idan shi ya goyama mutumin baya su kam babu shakka na san baza su k'i fad'an gaskiya ba" Abba yace "a'a Hjy ina ga ai ba sai an kira su ba" a fusace Dadda tace "billahillaziiy sai an kira su sun zo sun bada shaida,idan ba haka ba kafura uwata ta haife ni" Abba yace "shi kenan bari a kira su" yasa Amaar yaje ya kira Manar,ya kalli Waleed yace "je ka kira Ameerah" da sauri Dadda tace "a'a lala²! Billahillaziiy ba da yawu na  zai je ba,sam ban yarda da cewan yaje ya kirata ba,so kake kafin su zo ya kitsa mata abunda yake son tace? Ina laifin ma kai kaje ka kirata tunda abu dai ya had'a da uwarka" Abba dai bai ce komai ba ya tashi ya wuce sama,shi da kansa ya kira Ameerah,dai² lokacin su Manar suna shigowa,Abba ya zauna yana kallon Ameerah yace "jiya ance kuna tare lokacin da Waleed ya shiga gidan Hjy!" Ameerah tace "ehh! Abba" yace "za ki iya sanar min abunda ya faru?" Ameerah ta d'ago a hankali ta kalli Waleed da kansa yake k'asa then ta gyad'a kai,Abba yace "Uhn! Tell me what really happened?" Kamar ta san abunda ya faru ta juya baki itama ta fara magana kamar yadda Amaar yayi,a fusace Dadda ta kalli Abba ranta a b'ace tace "wai wane irin jaraba ne haka yake bibiyar iyalinka Yaro?" Not only Abba even Amaar,Manar da Ameerah sai da suka kalleta,Waleed da ya san kwanan zancen ko motsi bai ba,cikin b'acin rai Dadda tace "dan masifa kowa ya tashi magana sai yayi wannan kafirin yaren da babu dad'i babu dadad'awa,ni dai duk wanda ya sake magana da yaren nan a gurin nan wuta bal² tunda an san ba ji nake ba,kawai mutane saboda rashin tsoron Allah sai ku daddage ku dunga fad'an k'arya da wani yare salon a cuceni a lik'a min laifi" Abba yace "dan Allah Hjy kiyi hak'uri ba fa wani abu ake fad'a daban ba?" A fusace Dadda tace "idan ba wani abu ake fad'a ba ayi da yaren da aka san ina ji mana" da sauri Abba yace "Ameerah! Speak Hausa" Ameerah ta gyad'a kai ta zayyanawa Abba same abunda Amaar yace kamar tana gurin sanda ya fad'a,Dadda ta dunga kallonta baki sake tace "amma dai wannan yarinya kwai asararriya yanzu ki rasa wanda za ki goyi bayansa sai wannan mutumi?" Ameerah za tayi magana Manar ta rigata tace "to ba abunda ya faru aka ce ta fad'a ba?" Tsawa Abba ya musu suka yi shiru suna sunkuyar da kai,Dadda dake kallon Manarkammar za tayi kuka tace "da akace ta fad'i abunda ya faru kuma sai ta had'a da k'arya?" Abba dai sai kallonsu yake kafin yace ma Manar "Mamana!" Manar ta amsa,Abba yace "fad'a min abunda kika sani?" Tiryan-tiryan ta fara fad'awa Abba abunda ya faru ba tare da ta k'ara ko wasali kan abunda su Ameerah suka fad'a ba,Dadda ta saki baki ta dunga kallonsu ta kasa cewa komai,Abba yana gama saurarensu zai yi magana Dadda ta mik'e tsaye ranta a b'ace tace "shi kenan Yaro! Ina ga ba sai ka ce komai ba tunda ni suka mayar mak'aryaciyar,dama tun farko sai da nace ka kira su suzo d'aya bayan d'aya kasa aka jaka tattaro su lokaci d'aya, tunda mutumin suke jin tsoro zai fitar musu da rai,basu ko ji tsoron  Allah ba,ni dai na barsu da fitowar rana da fad'uwarta tunda yana kallo zai sakamin" tana fad'an haka bata jira taji abunda Abba zai ce ba ta wuce tana matsar kwalla,tana fita Abba ya dunga binsu da kallo kafin ya tsayar da idanunsa kan Waleed yace "haka kake son gani ko? Kullum ka dunga sa mahaifiyarmu zubar da hawaye?" Waleed yayi shiru bai amsa ba,Abba yayi k'wafa yace "bazan tab'a d'aukan raini daga gareka ba,abunda bazai yuwu bane na zuba maka idanu ka raina min mahaifiya,either ka girmamata yadda muke yi,ko kuma dai tabbas na sake jin wani abu makamancin wannan zan yi mummunan sab'a maka ta yadda baka yi zato ba.." Fad'a sosai Abba ya dunga musu dukansu kamar zai aro baki,kafin yace su tashi duka su bashi guri,Ameerah ce ta fara tashi then Manar suka yi sama tare,Amaar ma ya mik'e yayi saman,a hankali Waleed ya d'ago kansa ya kalli mahaifin nasa ya fara bashi hak'uri,Abba ya gyad'a kai yace "jeka! Allah kiyaye gaba" godiya yayi masa then yayi shiru,Abba ya kallesa ganin ya k'i tafiya,yace "akwai wani abu ne?" Jikinsa a mugun sanyaye yace "ehh Abba" Abba ya kafesa da kallo yana studying d'insa yace "Uhmn! Kai nake sauraro zan fita" Waleed yace "Abba ko za mu bari sai an jima idan ka dawo?" Abba yace "maganar ba shi da muhimmanci kenan?" Waleed ya girgiza kai yace "not at all" Abba yace "uhn! kai nake sauraro" sai da ya fara sauke numfashi kafin yace "arhmm! Dama Abba shawaranka nake nema" Abba yace "akan mene ne?" Waleed yace "akan maganar kai Manar skul" wani murmushi Abba yayi yana sake maida hankalinsa kan maganar da Waleed d'in yake yi yace "Uhmn! Me ya faru?" Waleed yace "i just think bai kamata ace an sa mata idanu ba ta zuwa ko wane makaranta ba,duka yaran gidan suna tafiya skul but ita sai dai tai ta bin apartments har sanda za su dawo,ina ganin me zaisa baza'a nema mata makaranta ba ta fara zuwa?" Gyad'a kai Abba yayi yace "ka yi tunani mai kyau,but ina ga ka fi kowa sanin halin grandma d'inku,yanzun a gaban idanunka ka ga abunda ya faru,so kake ta tado mana wani rigimar? Ko da ma ace na amince da maganar an nema mata skul ta fara zuwa,duk ranar da Hjy za ta koma ka san dagewa za tayi akan lallai sai an cireta su koma tare,right?" Waleed ya gyad'a kai yace "haka ne Abba! But haka za mu saka ido a barta ita kad'ai ta fita daban? A can ba skul take yi ba nan ma idan ta zo sai a barta ta zauna haka? Idan aka yi haka an yiwa rayuwarta adalci kenan Abba? Nan gaba da su wa za tayi kukan rashin ilimi?" Shiru Abba yayi ya kasa magana,sanda ya tafi tunanin maganganun Waleed d'in kafin yace "It's ok! Kaje later za muyi maganar in sha Allah" godiya ya sake yiwa Abba then ya tashi yayi sama,yana zuwa corridor ya bud'e k'ofar bedroom d'insa zai shiga ya hangota a cikin d'akin sai tab'e² take a gaban mirror, ta d'auki wancan ta ajiye ta juya wancan,a door way ya tsaya ya k'ura mata idanunsa,sanda taji alamun tsayuwarsa ta juya tana ganinsa da kallon da yake mata ta zumb'uro masa baki ganin yak'i shigowa tace "Yaya!" Saurin mayar da k'ofar yayi ya rufe ya k'araso inda take yana mata wani kallo yace "me ya kawo ki nan?" Kafin tayi magana yace "maza fice kafin na b'ata miki rai" rau² idanunta suka yi tace "to ni ba hak'uri nazo ba-ka ba" yace "na ce miki ina buk'atar bada hakur'in ki?" Kallonsa ta tsaya yi ya mata tsawa yace "get lost" wasu irin hawaye masu d'umi suka fara sakko mata,yana jifanta da mugun kallo ya wuce ya barta tsaye a gurin,da gudu ta juya ta fice daga bedroom d'in,tana fita corridor bata kula ba ta buge Diyanah bata tsaya ba ta dunga sauka da sauri tana share hawaye,da ido Diyanah ta bita sanda ta tabbatar Manar ta bar apartment d'in gaba d'aya sannan ta juya ta shiga bedroom d'in Mama tana tab'e baki..

#Share pls.
#Asli Smasher.

MANARWhere stories live. Discover now