Rede

226 25 11
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.



                    *♡MANAR¸.•💥*
               


*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._


                                12.

#Rede..

     Tsawa ta masa,idanunta gaba d'aya sun kad'a sunyi jaa tace "ka rufe min bakinka a nan gurin.. Kada ka kuskura ka furta ko wane irin kalma" kamar yadda ta buk'ata yayi shiru ya sunkuyar da kansa k'asa,cikin masifa tace "waye ya ba-ta wayar?" Bai d'ago kansa ba yace "Azaan" ta dunga kallonsa tace "wane Azaan d'in? Mutumin da ba ya k'asar" ya d'ago da sauri ya kalleta zai yi magana a fusace tace "ka san ba zan tab'a yarda ba ko?" Yace "why not Mom?" Cikin masifa tace "ni za ka rainawa hankali Waleed? Munafurcinka kuma wanne ne ban sani ba?" Girgiza mata kai yake yace "Mama!" Ta sake masa tsawa here ta dunga sirfa masa ruwan bala'i sanda tayi iya yinta ta gaji tace "billahillaziiy idan baka mayar da hankalinka jikinka ba za mu samu sab'ani da kai" shi dai ya mata shiru,tsabar mamakinta gaba d'aya ya kasa ko bata hak'uri dan kanta da ta gaji tace "tunda ka iya siya mata kace ba kai bane su kuma k'annenka fa?" Ya d'ago yace "Mama na fad'a miki fa ni ban siya mata waya ba" tace "dallah rufe min baki ni za kawa k'arya?" Ya d'auke kansa ransa a b'ace,tace "ni dai na fad'a maka ka fita harkar yarinyar nan,idan ba haka ba kuma duk abunda ya faru kayi kuka da kanka" ta juya ta nufi k'ofa tana ci gaba da bambamin fad'a,ajiyar zuciya ya dunga saukewa bayan fitarta,ya rik'e kansa da yake jin yana sarawa da hannuwansa biyu,ya jima a zaune yana tunani kafin ya tashi ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom,yana fitowa ya shirya ya d'auki keys d'insa yayi waje fuskarsa babu annuri,kafin ya k'arasa parking space Manar ta fito daga gidan tana tafiya kamar tana counting steps sanye cikin wani red colour d'in riga,hancinta ta mak'ala masa ring shaped d'inta,kallonta ya tsaya yi musamman lips d'inta da suka sha red colour chapstick,ya lumshe idanunsa a hankali yana jin wani irin yanayi yana mamaye jikinsa,yana bud'ewa suka had'a ido ta zumb'uro masa baki ba tare da ta kulasa ba,harara ya maka mata ya d'auke kansa ya k'arasa gurin motar ya bud'e zai shiga,gigitaccen ihun da tayi yasa shi fasawa da sauri ya saki murfin motar ya nufi inda take,ganinta a durk'ushe ya kai hannu zai tab'ata tayi sauri ta d'ago,mamakin abunda ya gani yasa shi zuba mata idanu ya kasa mata magana,ta tashi tsaye tana karkad'e rigarta ya d'aga kai ya kalleta,a hankali ta fara tafiya tana barin kusa da shi ta masa gwalo ta fashe da wani dariya,sakin baki yayi yana kallonta ya kasa mata magana,haushin raina masa hankalin da tayi yasa shi mik'ewa a fusace zai rik'ota,tana gama karantar abunda yake niyyar yi ta fella a guje,da yaga haka kawai sai ya tsaya kallonta yadda take gudun k'afafunta kamar za su tsinke ya fi komai basa dariya,ya dunga kallonta daga inda yake yana darawa,sanda ta kai balcony kafin ta tsaya tana maida numfashi,kamar ance ta waiga ta hangoshi a inda ta barshi,ya nad'e hannuwansa a k'irji yana kallonta,ta bud'e idanunta sosai tana kallonsa,dariya yayi mata wanda ya bayyana hak'oransa,ta dunga kallonsa daga inda take cike da mamaki duk a tunaninta ya biyota ne,yayi mata wink kafin ya juya ya shige motarsa ya bar gidan yana sakin murmushi. Har ya fita bata matsa daga gurin ba,Ameerah ta k'araso gurin ganinta tsaye ta zubawa get idanu ta dafa shoulder ta kafin tayi mata magana Manar da hankalinta baya tare da ita jin an tab'ata ta daddage ta kwalla k'ara,Ameerah ta koma baya da sauri a tsorace tace "dallah meye na ihun,ni ce fa kika wani b'are baki" harararta Manar ta juya tayi tace "kuma sai ki tsorata ni?" Ameerah ta kyalkyale da dariya tace "ke dai kin cika tsoro wallahi daga d'an tab'akin nan har kin tsorata" ta harareta tace "ban sani ba" ta wuce ta shige gidan. Tuk'i yake bayan fitarsa amma da ya tuna gudunta sai ya kad'a kai yayi murmushi,cike da nishad'i ya tsaya wani eatry ya siya abunda yake buk'ata ya fito,a hanya ya sake tsayawa wani bakery ya siya ice creams then ya juya kan motarsa ya nufi gida,yayi parking yana kallon apartment d'in yayi murmushi ya fito ya d'auko ledojin ya wuce part d'in Dadda,a parlor ya jiyo maganarsu ya k'arasa ya bud'e k'ofar yayi sallama,Manar tana jinsa ta waiga suka had'a ido,da sauri tayi zumbur ta mik'e za ta kwasa a guje,ya d'aure fuska ya d'auke kansa,ta dunga kallonsa sanda ya k'arasa shigowa ya zauna yana kallon Dadda da tak'i kallonsa,yayi wani murmushi cike da tsokana yace "wai fushi kike yi har yanzu?" Kamar mai jira tace "a'a dariya nake" ya gyad'a kai yace "ohooo! Thought fushi kika yi na rarrasheki" wani kallo ta masa tak'i tankasa,ya tashi ya nufi kitchen ya d'auko plates biyu ya dawo,ta d'aga kai ta bisa da kallo tana jira taga me zai yi,ya koma inda ya taso ya d'auki d'aya a cikin ledojin da ya shigo da su ya ciro coil paper da akayi wrapping ya warware,Manar dake tsaye ta zuba masa ido tana jira taga me zai fito da shi,kamar ya san me take ya d'ago ya had'e rai,ta b'ata rai itama ta wani d'auke kai kamar ba kallonsa take ba,yayi murmushi a ciki ya bud'e,zazzafan k'amshi ya cika gurin,ya juye ya ciro ice creams manya biyu daga d'ayan ledar da wani fura dake cikin roba shima,plate d'aya ya d'auka ya kai gaban Dadda da robar furan ya zauna yayi flexing legs d'insa ya d'auko yankan hanta d'aya yace "bud'e bakinki na baki" ta kalleshi ta kalli plate d'in hantar tayi murmushi tace "Allahu akbar.. Allah jik'an Malam ya masa rahama" Waleed yayi murmushi yace "ameen Hjy ta.." Tace "lokacin yana raye sai abunda nace ina son ci.. Dan wannan hantar kuwa ai sai na ture faranti" murmushi ya sake yi ya gyad'a kai yace "muci to sai ki ba-ni labari" tasa hannu ta fara ci,Manar dake tsaye ta tab'e baki ta juya za ta bar gurin Waleed ya kalleta ta gefen ido bai mata magana ba,sai da ta shige ya tab'e baki ya d'ago yace ma Dadda "ita wancan ba ta ci ne ta shige d'aki?" Dadda ta girgiza kai saboda dad'in dake hauramata cikin ka,sai da ta gama had'iye na bakinta tace "kai ma dai kamar wani baka san ba ta son hanta ba?" Shiru yayi ya zuba mata ido,ya d'aga girorinsa yace "Ohh! Na manta" ta ci gaba da cin abunta,sanda suka cinye ta d'auki fura ta kora,tana gamawa tayi hamdala tace "Allah maka albarka.. Yanzu da irin haka ne tsakaninmu har wani ma ya ji kanmu da kai?" Yayi murmushi ya koma kan kujera yace "saura labari na" tayi dariya tace "yanzu kuwa za ka ji su sai ka ce ya isa.." Labarin zamansu a Saudiyya ta fara masa tave "ai na fad'a maka zama Saudiyya ba dai dad'i ba.." Ya gyad'a kai yace "haba?" Tace "da gaske ma kuwa.. Komai baja-baja kake samunsa,shi yasa idan muka je harami babu abunda muke sai ibadah. Wata rana kawai muna cikin tafiya ba sai ga askar ba" yace "askar?" Tace "ehh! Kan kace me mutane sun fara gudu,radadada kowa sai gudu,ni dai ban san ya akayi ba kawai sai gani na nayi a gida ina mayar da numfashi,nake fad'a maka ban sani ba ma ko suma nayi a lokacin,ko wani ya kawo ni,na kalli Hjy Tasallah nace "wa ya kawo ni gida?" Y'ar kan uban yarinyar nan tana kallo na kawai sai ta kwashe da dariya,Hjy Tasallah tace "wa kuwa zai kawo ki idan ba k'afafun ki ba" na kalleta nace "aradun Allah bani iya dawowa gida da kaina" tace "to ai shi kenan tunda kinyi min musu" nake fad'a maka yarinyar nan ta zauna ta dunga min dariya,sai daga baya take fad'a min wai "Dadda kinyi rabin gudun ki a duniya" na tambayeta "wane gudu kuma Allah na tuba zan iya yi ni?" Tace "wallahi yau dai kinyi" nace "ni d'in?" Tace "ehh! Kinyi rabin gudunki dai" ni dai kamar zanyi kuka dan haushi nace "wai wane irin gudu ne nayi?" Kawai ta sake fashewa da dariya tace "rabin gudun famfalak'i mana" wai ashe da ina gudun ceton raina ne hijabina ya cika da iska.." Dariyar Amaar da Ameerah yasa Dadda juyawa ta kalli gurin da suke,ta gansu zaune kan kujera bata san yaushe suka shigo ba Ameerah har da kwanciya,Waleed kam tab'e baki yayi yace "kuma yanzun wannan labarin yayi miki kama da wanda nake so?" Ta kalleshi da sauri tace "yo kai dai ba labari kace na maka ba" yace " ba irin wannan nake so ba" tace "Iiiiiihhh! Wane iri kai d'in kake so?" Yace "mai dad'i dai haka" kallonsa ta dunga yi can ta tab'e baki tace "kai ni rabu da ni bacci nake ji,ku dai da ba'a raba ku da surutu sai kuje kuyi ta yi" wani murmushi yayi yace "ai biyana za kiyi" ta kalleshi tace "me na ci maka da zan biyaka?" Ya d'aga mata gira yace "nufinki nama da furan da na kawo miki a banza kika ci?" Tace "Iiiiiihhh! Daman biyanka kake nufin zanyi?" Yace "Uhn! Ke nufinki da bati kika ci?" Kamar za tayi kuka ta kalli Amaar tace "yanzu fisabilillahi d'an fodiyo dan wani cikinku ya siya min abu na ci sai kuma ace na biya? Dukiyarku ba ni da hak'k'i a cikinsa?" Amaar dai dariya kawai yake yi ya girgiza kai yace "a'a Hjy ta,ya ma za'ayi ace ki biya ko duka dukiyar kika cinye ai kin ci bulus" ta gyad'a kai tace "Uhn! Ka ji batu Malam" Waleed ya d'aure fuska yace "da gaske fa nake yi sai kin biya ni" ta kalleshi da sauri tace "to ba sai ka k'wata ba" yace "haka muka yi da ke?" Dadda ta hak'ik'ance tace "yo ko bamu yi ba da yanzu dai kam munyi,naci dubu sai ceto" murmushi yayi ya mik'e yace "za ki biya ni ne wani lokacin yanzu dai na yafe miki" tace "yo ko baka yafe ba ma yaya za kayi da ni?" Hanyar kitchen ya nufa ta bisa da kallo har ya tura k'ofar bata daina masa mita ba,Amaar ya kalleta yana sakin murmushi yace "a'a fa Hjy dan dai kawai ya ce ya yafe ne" ta juyo a fusace tana maka masa harara tace "yo ko bai yafe bama ai dole ya yafe,tunda dai ba zai yanki namana a matsayin kud'insa ba ko?" Hannunsa ya wanke ya fito da ruwa a hannunsa na roba,sanda ya koma ya zauna yana bud'e ruwan yace "kyaleta dan ta samu na ce na yafe mata ne,sai ma nace na fasa sai kin biya ni" mik'ewa tayi da sauri ta kama waistband tace "yo Allah na tuba sai dai mu dambatu mai k'arfi ya k'wata" yayi murmushin da ya bayyana hak'oransa yace "yanzu ko cewa aka yi ni dake muyi dambe,ai kya gudu kice a'a" tace "Iiiiiihhh! Saboda me?" Yace "haba Hjy ki kalle ni fa,ko wani namijin zai ji tsoron mu had'a jiki bare ke" harararsa tayi tace "ehh! Namijin ma sai dai idan sauna ne zai k'i" dariya sosai Amaar ya dunga Ameerah tana tayasa,Dadda ta wuce kitchen tana mita,Waleed yayi murmushi ya kalli Ameerah yana d'aure fuska yace "ke je ki d'auke wancan kayan" da sauri ta shiga taitayinta ta tashi ta d'auke plate d'in,ta kai hannu za ta d'auki robar ice creams d'in yace "banda wannan" ta wuce kitchen ta kai,da ta dawo ta wuce hanyar d'aki because ta san zama kusa da shi baka isa kayi kwakwkwaran motsi ba yanzun nan sai rai yazo yana b'aci,har ta kai kusa da k'ofa yace "su wannan d'in kina jira sai na ce ki d'auke?" Ta dawo da sauri ta d'auka a hankali gabanta yana fad'uwa tsabar tsoronsa tace "Yaya ina zan kai maka?" Wani kallo ya maka mata yace "kin tab'a ganin ina shan ice cream?" Ta girgiza kai da sauri yace "kin b'ace min daga gani ko sai na zane ki?" Da sauri ta wuce za ta sa a fridge ya mata tsawa yace "idan kika bari na ganshi da safe jikinki sai ya fada miki" cak ta tsaya idanunta suna kawo ruwan hawaye ta juya tana kallonsa tace "Yaya to ni ban san na waye ba" ya maka mata harara yace "ki jira na fad'a miki" daga haka ya d'auke kai ya ci gaba da kallon sport da ake haskawa,tsaiwa tayi a gurin ta kasa tafiya sai da ya d'ago ya kalleta ta shige d'aki da sauri,ta tarar da Manar a kwance ta k'arasa tana sauke ajiyar zuciya tace "shi wallahi Yayan nan ya cika takura" Manar tayi dariya tace "ki fad'a ya ji" a tsorace ta zaro idanu tace "Tabbb' so kike ya karairaya ni?" Tace "ashe kina tsoron yaji?" Zama Ameerah tayi kusa da ita tace "ga shi" Manar tayi saurin kallonta tace "mene ne?" Ameerah tace "ice cream" saurin tashi tayi ta zauna,ta d'auki d'aya ta bud'e Ameerah ma ta d'auki d'ayan suka fara sha suna hira. Ranar monday 7am ya shigo part d'in cikin k'ananun k'aya da suka amshesa yayi sallama,a zaune yaga Dadda kan darduma tana gyangyad'i bai yi magana ba ya kalleta ya wuce hanyar bedroom,ya tura k'ofar ya shiga,ya hangota kwance a saman gado tana bacci ya k'arasa ya kai hannunsa ya yaye duvet d'in da ta rufa,tayi juyi ta kai hannunta tana laluben bargon,ya tsaya ya zuba mata ido sanda taji ta kasa kamo bargon ta bud'e idanunta a hankali,a kansa idanunta suka sauka tayi sauri ta tashi ta zauna tana murza idanunta,ya maka mata mugun kallo yace "get up Malama ki shirya kada ki b'atan lokaci" ta dunga kallonsa kafin ta daure tace "ina za mu Yaya?" Yace "ban sani ba" ya juya zai fita,har ya kai bakin k'ofa yace "mintuna goma ki shirya ki fito ina jiranki a parlor" ta zumb'uro masa baki tana k'unk'uni,ya juya yace "me kika ce?" Da sauri ta sauka daga gadon ta wuce bathroom tace "nifa ban ce komai ba" ya gyad'a kai ya koma parlor ya zauna,kusan mintinsa biyar a gurin yana danna wayarsa yaga Dadda ba ta da niyyar kwanciya,yayi murmushi ya tashi ya matsa kusa da ita,shoulders d'inta ya kama zai kwantar da ita ta bud'e idanu a firgice suka had'a ido dashi tace "A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiim" wani kallo ya mata ya saketa ya koma inda ya taso,ta gyara zamanta tana hamma,ya tab'e baki yace "ki kwanta mana" da sauri tace "na kwanta a wannan lokacin?" Yace "mene ne idan kin kwanta yanzun?" Ta girgiza kai ta d'auki carbinta tana ja,tace "banji shigowarka ba yaushe ka shigo?" Bai kalleta ba yace "kina gyangyad'i ya za'ayi kisan na shigo dama" suna zaunen Manar ta fito sanye da dogon wando da t-shirt kanta babu hula sai kamshi take bakin nan bad'au da chapstick,tun kafin ta k'arasa turaren da ta sa ya sanar masa,ya d'aga kansa ya kalleta ya girgiza kai cike da takaici ya mik'e tsaye yace "d'auko hijab muje" kallon Dadda ta tsaya tana yi tana jira taji ko za tayi magana taga bata ko kallesu ba,shi kam tuni har ya nufi k'ofar fita ta juya ta d'auko ta kalli Dadda ranta a b'ace tace "mun tafi" Dadda ta d'auke kai tace "Allah tsare hanya" daga haka ta mik'e ta fara karkad'e kura,tana fita ta hangoshi a parking space ta k'arasa a hankali,ya bud'e front seat ya shiga ba tare da ya ce mata komai ba,ganin ta tsaya ya lek'o fuskarsa a d'aure yace "za ki shigo mu tafi ko tsaiwar za ki ci gaba da yi?" Ta tab'e baki ta bud'e ta shiga ta rufe,ya kalleta kafin ya fara warming motar then yayi zooming off suka bar gidan,suna isa makarantar yayi parking a inda aka tanada,science academy ne mai kyau da yake had'e boys and girls,yayi parking ya fita yayi gaba,ita kam tana ciki sai zare ido take sai da ya juya yaga bata fito ba ya mata tsawa yace "get down Malama" ganin yanayin fuskarsa yasa ta bud'e ta sakko ya wuce forefront ta dunga binsa a baya har suka k'arasa office d'in principal,cike da girmamawa matar tayi welcoming d'insu dan tsaf ta shaida Waleed ta nuna musu guri suka zauna,after sun gaisa da Waleed Manar ta gaisheta,matar ta kalleshi tace "Mr Maji dad'i! Meke tafe da ku?" Waleed ya gyara zama yana kallon Manar ya mata bayanin abunda ya kawo su,ta gyad'a kai ta kalli Manar tace "ya sunanki y'an mata?" Manar dake b'ata rai tace "Manar Muh'd Maji dad'i" cikin barkwanci matar tace "wow! Triple M ko?" A hankali Manar ta d'aga kai ta kalleshi,yadda taga ya had'e rai ta sunkyar da kanta tana wasa da fimgers d'inta,Waleed da ya zuba mata ido ya juya ya kalli matar yace "Zainab Muh'd Maji dad'i shi ne sunanta" principal ta gyad'a kai tace "wane class ta gama can makarantar da ta baro?" Wani murmushi Waleed yayi ya kalli Manar cike da takaici yace "madam a tunaninki wane class ne ya dace da kamarta?" Principal tayi murmushi tace "think s.s one ko j.s.s three?" Waleed ya sake yin murmushi yace "ku kaita j.s.s one.." Matar ta kalleshi cikin mamaki tace "j.s.s one?" Waleed ya gyad'a kai,principal tace "amma ba ka ganin shekarunta da girman jikinta ya wuce na y'an j.s.s one?" yace "wane aji kike ganin ya dace da ita idan ba can ba?" Principal tace "j.s.s one duk k'ananun yara ne babu sa'anninta a can,ina laifin ma a kaita ko j.s.s 3 d'in" waleed yace "Ko kin san iya karta primary daga nan bata ci gaba ba?" Matar tace "wannan ai ba wani abun damuwa bane" yayi wani murmushi mai had'e da k'wafa yace "please madam ku kaita j.s.s one" sheshshek'ar kuka Manar ta fara,ya waigo da sauri ya kalleta,babu shiri ta rufe baki,ya sauke numfashi ya mayar da hankalinsa kan principal yace "madam she deserved nowhere than j.s one" principal tace "why not baza'a a had'a ta da y'an uwanta ba,idan yaso sai ku nema mata lesson teacher da zai na guiding dinta a gida.."


#Share pls.
#Asli Smasher.

MANARWhere stories live. Discover now