MUFEEDA
EPISODE ONE
By
SNOW WHITE
Holma,Adamawa state
Da tulelen cikinta taje diban ruwa duk cikin yan matan ita ce kadai matar aure idan mijinta na nan ba zai taba bari ta fita deban ruwa ba shekarar su daya da doriya a qauyen da ya zamo garinsu a yanzu ba ta da kowa bata san kowa ba in ba mijin ta ba komai na rayuwrata ya shafe hatta sunanta sai da ya sanar da ita.
Bata fita ko nan da chan in ba tare da shi ba shi kadai ta sani kuma shi kadai ta yarda da, ba wanda ya san kalar fuskarta duk cikin qauyen in ba qawayenta biyu da take tafiya da su nan ba jumai da laraba.
Yanzu ma ganin su tayi suna tafiya rafi dake mijin nata ya danyi nisa sai ta bisu da yana nan ba zai taba barinta fita ba ko rashin lafiya tayi da niqab take fita haka shi ma da zai fita daga gida da hutt yake yawo wanda ba lallai ne ka ga fuskarsa ba,akasarin rigunan sa kenan acewarsa wai "ana neman ran mu ne duk sanda za a gane inda muke to kashe mu za ayi".......
Jummai ce ta katse ta da tambaya "mufeeda na jiki shiru kodai mu karba miki ruwan ne kinga baki saba diban ruwa ba amma yau kika bimu kin san halin mijinki amma kika nace ni dai ba ruwana idan ya ganki"
Ai kia ce haka tunda ku na biyo kuma ma na san ba yanzu zai dawo ba zai kai yamma don cikin gari ya shiga kuma ai........
Mutum ta ga yana tsaye a gabanta kamar an datsa shi,wani kallo mai firgitarwa yake jifanta da shi maganar da take yi ne taji ya maqele mata a wuya.bata taba ganin bacin ransa kmar wannan ba tsoro ne ya shigeta har sai da yaron cikinta ya motsa, a wurin ta tsaya chak tana neman dauki daga wurin kawayenta ai tana juyawa taga sun arce ruwan na ta zuba a jikin su amma ko kula ba suyi ba suna ta qara sauri Tausayin su ta ji yadda ita ce ta ja musu wannan masifan don ta san ba barin su zaiyi ba sai ya je har gidan su,dama baya son kasancewar su kusa da ita daqer ta samu yana barin ta na muamala da su.
Ban ankara ba naji bukatin da ke kaina ya fadi passs a qasa tare da zubuwan ruwan da ke cikin,lokaci daya ya fara jan hanun na ina ta tirjewa sanin yau mai kubutar dani daga hannunshi sai Allah
:Don Allah kayi hakuri na daina daga yau bazan qara fita ba,kuma ma kaga na sa niqaf ba wanda ya ga fuskata,na san ranka ya baci amma na gaji da zama wuri daya na gaji da rashin hira da kowa na..........
Shut up ,ki min shiru.
Ai kuwa sit tayi don ta san hali.har suka kai gida.
Ya turata cikin daki sannan ya sa makulli ya kulle dakin ya fita daga dan qaramin gidan nasu,bai zame ko ina ba sai gidan su jummai,yayi sallama da mahaifinta bayan ya fito ne yace yana son yayi wa yarsa kashedi kada ta qara zuwa gidansa.
Hakuri mal. garba ya bashi akan hakan ba zai sake faruwa ba,ko sallama bai masa ba ya kama hanya ya tafi.
Malam garba kuwa yana shiga gida yana tuna irin hirar da ya taba jin jummai nayi akan bakin da suka zo garin su kusan shekara daya kenann da doriya,yadda mijin baya son alakar komai ya shiga tsakanin su da matarsa haka shima in ba gaisuwa ba ba abunda ya taba shiga tskanin su,yar sa akwai zokale zokale ba don haka ba yadda mutumin yayi ta korarsu agidan sa da tana da zuciya da ta daina zuwa.
amma yau zai korota gobe ta sake zuwa har ya gaji ya barta tana zuwa wurin matarsa ita da laraba amma yau daya matar ta fita shine ya wanke kafa ya zo to ai shima ba son alakar su yake ba kawai dai yana tausayin matar ne don jummai ta na yawan cewa matar ta manta komai na rayuwarta shi bai taba ma ji mutum na manta abu dangane da rayuwar sa ba.
YOU ARE READING
MUFEEDAH
Romanceits all about a yong girl who meet her destiny on her wedding day. come joint me, you won't regreat ever reading this story. happy reading guys.