PAGE 5

8 1 0
                                    

®Mrs Shabab

An karbo daga abi Huraira Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah  (S.A.W) ya ce, "Duk wanda ya yi min karya da gangan ya nemi wajen zamansa a wuta."
Muslim ne ya rawaito.

Nana Aisha Amman Abdul (Gam Bandirabe Fulbe group) wannan page din naki ne.
***     ***     ***     ***
Abuja

Washegari da safe bayan Sahl ya dawo daga motsa jiki, dama dabi'arsa ce kullum bayan ya yi sallar asuba ya gama azkar dinsa sai ya wuce wajenda aka ware a gidan domin motsa jiki, shi da daddy ne kawai suke yi, amma Suhail bai cika yi ba ka'idar sa ne za'a kawo masa coffe ya dan sha, kafin ya fara directly bedroom dinsu ya wuce.
Samun Suhail yayi ya kwanta yayi dai-dai yana sharar barci, girgiza kai yayi kawai yana mamakin son jiki irin na Suhail, shiyasa wani lokacin suke yin fada dan Suhail akwai shi da kasala shi kuma Sahl ba ya son wannan halin.
Bayan ya fito daga wanka ne ya jawo stool ya zauna a gaban mirror yana shafa mai, sannan ya gyara sumar kansa irinta fulanin asali duk da ma dai ba ya tarata saboda kasancewar sa soja, sannan ya dauki performs kala-kala ya fesawa jikinsa, kamshi ya gauraye dakin har ya so ya yi yawa.

Sahl yana son kamshi sosai wani trouser na jeans tiri kwata yasa, da wata t-shirt light Brown ta saje da kalarsa fatarsa.
yawanci kayansa brown ne dan yana son kalar sosai, ganin kamar Suhail ya takure alamar sanyi ya ke ji ya sashi rufa masa blanket, yana cewa "malalaci" tare da rage masa karfin AC.
Zama yayi a three seater wacce take facing din gadon, ya jawo laptop dinsa ya fara daddannawa cikin kwarewa.

Suhail kuwa dama idonsa biyu duk abinda Sahl ya keyi yana jin sa, murmushi yayi yana kara jin kaunar dan uwan nasa.
Misalin karfe sha daya Suhail ya farka yana mika gami da shiga bathroom, yana cewa "wallahi mi somi masin, bandu'an nawai..."(na gaji sosai wallahi, jikina duk ciwo yake).
Sahl ko daga kai bai yiba balle ya tanka masa, dan ya saba da wannan hali na suhail, kullum suka yi tafiya ya rinka complain na ciwon jiki.
Misalin karfe sha biyu suka nufi side din iyayen nasu kayansu iri daya sai banbancin colour, dan shi Suhail ya fi son coffee colour.
In ka gansu gwanin sha'awa ma'aikatan gidan da soldiers sai gaisuwa suke, yayin da Suhail yake amsawa cike da fara'a da kulawa, amma Sahl ko kallo basu ishe shi ba.
tafiya ya ke irinta zaratan maza fuskar nan a daure bayan shigarsu parlourn ne suka samu mummy tana zaune, ta sha kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau, dama mummy ba dai kwalliya da kwalisaba, in ka ganta da su Suhail sai ka rantse yayarsu ce saboda iya kula da jikinta, ga tsafta da kyau.
karasawa sukayi tare da sanya ta a tsakiyarsu, hadasu tayi ta rungume tana shafa kansu tamkar wasu kananan yara, Sahl ne ya fara cewa "Habibty walijam...?" (Ina kwana...?) ta amsa "jam kalau, on ummake jam..? (Lafiya lau kun, tashi lafiya?).
Shi ma Suhail ya gaisheta dama in dai mummy za su yiwa magana mafi yawanci da fulatanci suke yi mata magana, saboda haka ta dorasu, dan ba ta so 'ya'yanta su manta yarensu na gado.
Daddy ne ya shigo yace "oh mummy ba dai son 'ya'ya ba." dariya suka yi gabadaya, banda Sahl da ya dan yi murmushi ta gefen baki, suka gaida dad ya amsa cikeda kulawa,  yace "ai dole yara su ki yin aure kullum kina shagwabasu..."
mummy tace "ai dole na shagwabasu" haka suka yi breakfast sannan suka dawo leaving room.
News paper Sahl ya dauka yayin da Suhail ya zauna kusa da mummy yana shagwaba, dad ya kalli Sahl yana nazarinsa yana kuma mamakin halinsa na rashin son magana da muskilanci yace "son ya maganar zuwa course dinku yaushe ne tafiyar?
Sahl yace "upper week" Suhail yace "Dad gaskiya ni bana son aikin sojan nan wa bros akwai wahala, ka ce masa ya ajiye aikin kawai" Sahl ya harare shi "yace ok tell me what did u want me to do?.. sai na zauna kamar mace ina aiki a hospital ko na yi teaching ko...?"
Dama dagangan Suhail yayi maganar dan ya tsokane shi yayi magana, dariya su Dad suka yi sosai shi kuwa Suhail haushi ya isheshi yace "wallahi cnslt doctor like me ya wuce raini a ko ina, menene a aikin sojan in banda barazana da kakinsu ya ke yiwa mutane..."
mummy tace "ka manta da Dad dinku ma soja ne kake wannan maganar?.. Suhail yac e "amma fa Habibty kinji abinda yace, min wallahi mi jabata..."
Dad dai banda dariya ba abinda yake mummy ta cewa Sahl "who tell u aikin teaching da doctor abune mai sauki?.." Suhail ya ce "tambaye shi dai Habibty" Dad yace "ya zaku yi masa taron dangi ne? akan ya fadi gaskiya..."
Shi dai Sahl bai kara cewa komai ba tamkar baya wajen, haka Suhail yaci gaba da tsokanarsa Dad yana tare masa, haka suka yi ta hira Sahl ya mike ya fita ba tare da yace komai ba dan ba ya son yawan magana, surutun Suhail yana neman sanya masa headache.
Mummy ta kalli Dad tace "anya kuwa my heart yaron nan bashi da aljanu?.. Sam bashi da alkibla, shi ba dama a zauna ayi hira dashi kamar kowanne mutum, ni fa wannan abun yana damuna.."
Dad sai da ya bari ta gama yace "what are u trying to say? ba na son kina dangantamin d'a da aljanu, kina magana kamar ba ki san halinsa ba?..  yau kika fara ganinsa ko jiya? da za ki ce haka, ba wasu aljanu halinsa ne..." 
Mummy tace "Allah ya huci zuciyarka my heart, ba wai da wata manufa na fada ba, amma na ga kamar maganar ta maka zafi.."
Dad yace "Ok be carefull, ba na son irin wannan maganar.."
mummy ta ce "insha Allahu mi alai.." (Insha Allah zan bari) Dad ya ce "better" sannan ya tashi ya nufi side dinsa da ido suka bi shi Suhail yace "wallahi Habibty biyaye am Dad o roni.."  (wallahi mummy d'an uwana Dad ya gada)
Mummy tace "joddaki i b'e yimbe ai dun sad'i" (zama da wadannan murdaddun mutane akwai wahala) Suhail yace "Allah Ya canja musu wannan hali, har yanzu ba zan iya Doran da wasu halayen biyaye ba a matsayina na shakikinsa...
Ba wani abun haushin ma habibty, sai muna zaune sai nayi magana goma, bai amsa min daya ba, ammafa wani lokaci in ya so muna dan hira kadan..."

Haka suka yi ta tattauna lamarin, dama shi dad indai kana son bacin ransa ka fadi wata magana marar dadi akan Sahl, saboda yana matukar sonsa sosai, mummy tana mamakin irin son da ya ke yi wa Sahl, ko dan shi ya dauki irin halinsa ne oho.
Suhail ne yayi ta kokarin kawar mata tunanin, saboda kar ta shiga damuwa, yace "Habibty gobe Suhailat zata dawo ko?.."  mummy tace "eh" haka dai sukayi ta hirarsu.
Shi kuwa Sahl side dinshi ya koma, yayi wanka ya canja kaya, sannan ya dauki car key dinsa ya nufi parking space.
Wata Black Jeep ya shiga a ka'idarsa ba ya driving, saidai ayi driving dinshi, shiyasa wani soja wanda shi ne drivern sa ya nufoshi da gudu yace "sir.... " kafin ya karasa Sahl ya d'aga masa hannu tare da ba wa motar wuta ya fice girgiza kai sojan yayi yana cewa "ko ina zai je kuma shikadai..?"
Wani boutique ya nufa bayan kamar minti sha biyar ya fito da wasu kaya a hannunsa, tare da sawa a cikin motar ya nufi wani madaidaicin gida mai matukar kyau da kawa, hancin motarsa ya danna cikin gidan tare da diban kayan da ya sayo, ma'aikatan gidan sai gaisuwa suke masa amma bai bi takansu ba, ya ciro wasu keys a pocket dinsa ya bude kofar shiga parlour n.
kai tsaye ya nufi wani bedroom, tare da zama a kan gado sannan ya fara bude ledodin da yayi sayayya, abin mamaki kayan mata ne masu kyau da tsada kala biyar, sanna sai na maza da alama nasa ne da na dan uwansa, suma kala biyar-biyar ne dan komai za su saya tare suke saya.
tashi yayi tare da bude wardrobe cike take da kayan mata, ya sa kayan da ya sayo a botique ciki gami da rufewa.
Kwanciya yayi a gado yana lumshe ido yana motsi da bakinsa, Allah ne kadai ya san abinda yake fada, can kuma ya tashi ya nufi wani katon zane da aka yi mai kyau wanda baza'a gane ainihin fuskar ma'abociyar ciki ba.
Ya dade ya na kallo tare da sumbatar hoton gamida furta wasu maganganu a kasan makoshin sa, daga karshe ya rufe dakin ya fito.
ba kowa a gidan sai mai gadi, da mai bayi sai mai shara, wanda kullum zai share ko ina har dakunan.
Bai yi wa kowa magana ba ya ja motarsa cikin hanzari tareda barin gidan, sam Sahl ba ya son sanyin jiki, komai cikin zafin nama yake yin sa. maigadi da mai shara suka bishi da ido, mai gadi yace "oh ni Adamu ina ganin ikon Allah, wannan yaron ko aljana ce ta aure shi ne?.."
Isah yace "kasan Allah da har na zargeshi ko wani abu yake aikatawa, amma ranar da na bishi na lab'e sai naga wani zane kawai yake tsayawa yana kallo yana murmushi, kuma mace ce aka zana, ina ganin ko matarsa ce ta mutu, ko kuma aljanarce ta aureshi kamar yadda ka fada, dan na sha labewa har na gaji ni dai ban taba ganin komai ba..."
Adamu maigadi yace "gaskiya ba karamin so ya ke yiwa wannan mata tasa ba, ina tausaya masa ga shi da kyauta, sai girman kai.." Isah yace "wallahi ya na burgeni dan akwai shi da kyau ga aji.." haka hirar tasu ta kasance.

MUNTAHAL ISHQ (KARSHEN SOYAYYA)Onde histórias criam vida. Descubra agora