Shigowan su Farha be sa an daina hayaniyar da ake yi a gidan ba, gaisawa sukayi sannan aka yi musu iso da shigowa parlor, mata ne sosai a cikin parlor 'din suna ta hira a cikin su ko harda Maman Husnah da Husnah, babu abunda akeyi se zallar wayewa na rashin hankali, Mamma ce tace
"Bari muyi introducing kan mu kafin mu fara gabatar da kayan, ni suna na Hajia Fadeelah, ni qanwar mijin babbar yayar su Mahaifiyar Aryan ne wato Hajia Tasneem, wannan ita ce Hajia Jamila Siyamah ita ke bi ma mahaifiyar Aryan, se wannan ita kuma ita kuma sunan ta Hafsat Noorie cousin 'din Aryan ce 'yar Hajia Tasneem, suruka ta ce kuma tana auren yaro na, se wannan ita kuma sunan ta Amina Anaan ita ma cousin 'din Aryan ce 'Yar Hajia Siyamah, se wannan ita kuma sunan ta Hajia Ameerah Cousin 'din Mahaifiyar Aryan ce, se wannan ita kuma ita ce Matar Aryan 'din...."
Kafin ta qarasa se qanwar Mamar Husnah tace
"Wacce?"
Kallon mamaki dangin Aryan suka bi ta da shi, Noorie ta yi sauri tace
"Wannan da ake nuna miki ita ce Uwargidan Aryan wato matar shi, sunan ta Tasneem Farha"
Nan fa wasu daga cikin dangin mamar Husnah suka fara kuskus da gulmace gulmace, ana ta watso ma Farha harara, da su Ummi suka lura da hakan se suka ce zasu gabatar da kayan, ganin haka se Mamar Husnah tace
"To muma dai nan duk dangin Husnah ne, qanne na ne nan se yayye na, ni kuma ni ce Mahaifiyar Husnah, ga kuma Amaryar ku Husnah nan"
"Ayyiriri Ayyyiriiri"
Dangin Husnah ne suka fara gu'da, kallon kallo kawai su Noorie suka fara, ita ko Farha murmushi tayi saboda tunda ta shigo ta lura da Husnah, Noorie da ba ta barin ta kwana tace
"Ikon Allah ashe amaryar ta na nan, ai ban ta'ba ganin amarya ba a wurin ansan lefe ba se yau, sannu malama Husnah amarya kin sha qamshi"
Jikin dangin Husnah ne yayi sanyi saboda maganar da Noorie ta watsa musu, nan dai sukayi ta sake ma su Noorie habaici, da ummi taga abun bana qarewa bane se ta fara magana
"Ga akwatunan Husnah nan, akwati ne guda goma sha biyu, Noorie zata bu'de su se ku ga abubuwan da ke ciki"
Noorie miqewa tayi ta fara bu'de kayan su ko suna ta kallo suna santin kayan, se da ta gama bu'dewa sannan ummi tace
"To ga kaya nan Allah ya sanya alheri ya sa ayi damu"
Kowa ya amsa da
"Ameen"
Farha ce ta ciro ku'di a cikin jakar ta sannan tace
"Ga kudin 'dinki nan, dubu 100 ne "
Qanwar mamar husnah ce ta miqe ta anso nan dai sukayi ta qauyanci da sakarci, sallama 'yan bangaren ango sukayi zasu wuce, uwani wadda tafi kowacce natsuwa a cikin dangin Husnah ce tace
"Ku dan dakata bari a 'dakko muku tukuici"
Tashi tayi da sauri ta miqe ta shige 'daki, ruwan da drinks 'dinda aka tanadar ma yan kawo lefe ta kawo musu, godia sukayi sannan suka ce zasu wuce, mutum uku ka'dai sukayi musu rakiya sannan su Farha suka wuce, gidan mummy suka koma dukansu .
****Khadeejah ko tana komawa gida ta iske Aunty tana qoqarin 'daura girki, da sallama ta shigo ita kuma aunty ta amsa, aje hijabin ta tayi a 'daki sannan ta fito ta fara qoqarin taya aunty girki, Aunty tace mata
"Kin kai su gidan?"
"Eh Mama na kaisu, 'daya daga cikin matan ma ta bani ku'di wai inyi ku'din mota, kinga yanzu gobe se ace ma baba ba se ya kawo ku'din cefane ba ko?"
"Eh hakane kinyi gaskia, Allah yayi miki albarka deejeh nah"
Murmushi Khadija tayi sannan tace "Ameen mama", lura da yadda Aunty ke ta aiki jiki a sanyaye yasa Khadija tace
"Mama"
Aunty ta 'dago daga hura wutar da takeyi tace
"Naam Khadija ya akayi?"
"Mama kiyi haquri da abubuwan da su Maman Ya Huseey suka yi miki, komai yayi farko ze yi qarshe, mahakurci mawadaci ne"
Murmushi Aunty tayi tace
"Haba Khadija kar ki damu wallahi babu komai, ki cire abun kema a ranki, ni ban 'dauki ma abun da zafi ba.."
Sallamar Baba ne ya hana ta qarasa maganar da take yi, amsa mishi sukayi "Washh Allah" baba yace sannan ya samu saman dakali ya zauna, gaida shi sukayi sannan ya amsa da
"Yauwa sannun ku da gida, girki akeyi?"
Khadija ce tace
"Eh baba"
Aunty ko tashi tayi ta kawo ma baba ruwa, amsa yayi tare da yin godiya sannan yace
"Har baqin sun wuce? ina Husna take ?"
Aunty na qoqarin kare maganar Khadija tayi sauri tace
"Yaya Husnah tana gidan maman ta, acan aka amsa kayan lefen"
Baba ya yamutsa fuska yace
"Ban gane ba, kamar ya acan aka amsa kayan, meyasa ba'a amsa anan ba"
Aunty cewa tayi
"Ai dayake kasan... "
Baba ne ya dakatar da ita yace
"Dakata Zuwairah bari Khadija ta bani amsar tambaya na"
Nan Khadija ta cigaba da cewa
"Ai baba Yaya Husnah tana ganin ka fita ta kira maman ta a waya, ba'a 'dauki ba lokaci ba se ga maman nata tazo ita da wasu 'yan uwan ta, girkin tarbar baqin da aka gama yi suka fara 'dauka sukayi waje dashi, suna ta zagin Mama wai baza'a amshi kayan Yaya husnah a wannan qazamin gidan ba, nan fa sukayi ta shuka rashin mutunci, suna gamawa Yaya Husnah ta bi su suka tafi can gidan maman nata, 'yan kawo lefe na zuwa na raka su can gidan maman Yaya huseey 'din, acan suka kai lefen"
Baba ya yi shiru yana ta nazari sannan yace
"Har yanzu Husnah tana can ne?"
"Eh baba tana can"
Be sake cewa komai ba ya tashi ya shige 'daki ranshi a 'bace, yana shiga 'daki Aunty Zuwairah ta kalli Khadija kallon meyasa kika fa'da masa, Khadija tace
"Kiyi haquri Mama amma rufa ma Yaya huseey asiri be da wani amfani"
Aunty tace
"Duk da haka amma yanzu ya shigo gida da kin bari na fa'da mishi da kai na in ya huta"
Khadija ta kuma cewa
"Nasan bazaki iya fa'da mishi ba Mama, InnshaAllah ze 'dauki mataki, ki qara haquri"
Taku a kullum
Aisha Ameerah❤️
YOU ARE READING
TASNEEM 2 in Tasneem series✅
Spiritual"'Daliba ta a makaranta ze aura" "......Se da na gama kwalliya na sa kaya fa, sannan na fita nayi kwaskwarima na 'dauraye qafa na da hannu na, ni brush 'din ma banyi ba chewing gum na sa a baki na" "......babu boka babu malam amma se zaman gidan se...