Duban ta yake qasa qasa yana jin sonta ta kowane bangare ta juya ta fice, a bakin gado ta xauna tana tunanin wato wannan shine auren? Idan hakane kuwa aure abu ne mai nauyi da sai an kai xuciya nesa saboda girmansa da darajarsa wanda yafi qarfin tunanin ta da hankalin ta ba dan komai ba sai dan soyayya da kunyar bakori da nayi mata mugun kamu a xuciya da gangar jikinta, amma so nice xuciya da gangar jikinta na karban shi.
Jin hakan yasa ta qara sonsa da qaunar sa wanda bata taba jin irinsa ba a xuciyarta da baxata iya kwatanta irin sa ba, haka taji baxata iya kwatanta ganin sa da wata mace ba taji wani sabon kishinsa ya mamaye duka ilahirin jikinta, ta rumtse idanuwanta xuciyar ta na mata quna.
Sai kaiwa da komowa take tsakanin dinning da kitchen d'auke da warmers, marwan na biye da ita da nasa surutun.
Umma yanxu na gaji da bibiyar ki xan jira ki a sofa.
Tun da baka jin yunwa kaje kayi barci kada ka jirani a sofa,
Kallonta yayi tana qoqarin wanke hannun ta a sink yace umma yau tare xamu yi barci tunda Hajiya bata nan.
Tace tam shikenan je ka jirani kafin na gama.
Ya juya yana fad'in har da assignment xaki min yau fa,
Kaje ka fara kafin na xo ta fad'a dai dai lokacin da bakori ya shigo falon da sallama.
Da sauri yaje ya rungume sa oyoyo daddy, bakori ya d'auke sa my little boy d'an rigima, marwan ya tsaida idanuwan sa kan dattijuwar dake bayan bakori a tsaye tana kallon su da murmushi.
Daddy wannan wacece ya fad'a yana nuna dattijuwar tare da kallon bakori.
Amaryata ce jeka kira umman ka, marwan ya juya da sauri yana kiran sunan ta, umma xo kiga daddy yayi sabuwar amarya.
Saif ya dubi dattijuwar tare da fad'in ki xauna inna, ta xauna a qasa, yace aa ki xauna akan sofa, tace barni nan ma ya isa dai dai lokacin da Xarah ta fito daga kitchen d'in cikin sauri jin abinda marwan yaje yana fad'a mata.
d'agowa yayi yana kallon ta cikin mamaki yanda ta fito a firgice, itama kallon sa take kafin ta maida idanuwan ta kan dattijuwar dake xaune a qasa, numfashi taja a hankali tana hararar marwan a fakaice cikin takaicin sa domin ya tayar da hankalin ta sosai.
Bakori yace ki nuna mata sashen masu aiki ya juya ya bar gurin.
A sanyaye ta gaida dattijuwar kana suka nufi d'akin da xata xauna ta nuna mata, marwan ya qanqame hannun ta tare da shagwabe fuska kamar xai yi kuka yace umma ni baxan kwanta da ita ba dake xan riqa kwanciya ki gayawa daddy.
Tace dama waye yace tare xaku riqa kwanciya, yau kad'ai ne ina ji, ya girgixa kansa yana bubbuga qafafuwan sa,
Baxan kwanta da ita ba, she looks older kuma yar qauye ce,
Tace idan na sake jin wannan mgnr a bakin ka xamu yi fad'a sosai da kai, respect her she is granny also, I promise you gobe baxaka kwana anan ba just for today.
bai qara magana ko kallon ta ba, ya hau gadon ya kwanta tare da juya mata baya alamar yayi fushi dariya kawai Xarah tayi tana kallon ta tace inna kiyi haquri kada kisa abun a ranki nan da lokaci qanqani xai saba dake sosai.
Murmushi inna tayi kafin tace dama waye xai damu da surutu na yara.....
Kwance take tayi lamo akan luntsumemen gadon ta, ya shigo cikin shirin sa na kayan barci kallo d'aya tayi masa tayi saurin maida idanuwanta ta rumtse tamkar mai barci, wannan karon Ma akan gadon ya kwanta kamar jiya sai dai yau ya canxa akalar barcin ta hanyar rungumota sosai a jikinsa.
Cikin murya qasa qasa yake magana ganin yanda jikin ta ke rawa, ashe ba barcin gaskiya kike ba, shikenan qarfi da yaji kin maida ni mai xuwa d'akin ki barci a maimakon ke kije nawa, ta soma qoqarin raba jikin ta da nashi kamar ta nutse gurin saboda kunya dana mamaye ta, ya riqo qugunta sosai yana jan numfashi a hankali saboda dad'in turaren dake jikin ta.
Kiyi barcin ki ba abinda xan maki, idan kuma kin fison kwanciya da marwan ne naje na d'auko maki shi, bata san sanda ta girgixa kanta da sauri ba tare da riqo sa, yayi murmushin farin ciki tare da soma kissing d'inta ta ko ina wanda ya soma gigita kwakwalwarta, al'amari ne da ko a mafarki bata taba katarin yin irin sa ba, wai itace yau a jikin bakori, wannan wani abu ne da imagination d'inta bai taba bata ba, ya kashe duk wata lakka ta jikinta dake isar da saqo xuwa gangar jikin ta, labari ya canxa domin SAIF BAKORI ya birkice mata gabaki d'aya, duk magiya da roqonta, duk kuka da yakushin ta SAIFULLAHI D'AN BAKORI bai tausaya ko saurara mata ba, ya rungumota sosai yana sauke numfashi a hankali cikin wani tsatsan farin ciki marar misaltuwa, ta janye jikinta daga nasa tana kuka sosai.
Sorry sorry sorry yake fad'a yana kai mata sumbata a lips d'in ta, ganin da gaske ture sa take bata so yana kusanto jikinta ya saka shi sauka daga gadon, toilet ya nufa ya had'a mata ruwan wanka kana yaxo ya d'auke ta.
Nasa d'akin ya nufa yayi wankan kafin ya dawo nan d'akin har xuwa lokacin bata fito ba.
Bai jima da kwanciya ba yaji alamar bud'e toilet din ya juya da sauri yana kallon qofar idanun su suka sarqe dana juna tayi saurin d'auke nata cikin jin nauyin sa tare da turo bakin ta, murmushi yayi yana qara kallon yanda idanun ta suka kumbura saboda tsabar kuka, da kyar ta xauna bakin gado tana yatsina fuska a hankali.
Yana kallonta ji yake idan bai maida ta jikin sa ba xuciyarsa xata tarwatse, ya janyota ya had'a ta da jikinsa, ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka ya soma bata haquri tare da wasu kalamai masu ratsa xuciya tare da rufa masu blanket ya lullube su.