Fitowar ta wanka daure da towel yayi dai dai da shigowar sa dakin cikin shirin sa da alama fita xai yi.
Cike da matsinanciyar kunyar sa ta dabirce ta tsargu daga yanda ya xuba mata narkakkun idanuwansa yana kallon ta, ya dauke kansa kamar bashi ne yake kallon ta ba.
Minti goma kacal na baki ki shirya,idan kika bata min lokaci babu inda xaki je,ya juya ya fice.
Tsalle tayi cike da farin ciki tana dariya ashe xata ga umma yau,a gurguje ta shirya ta xuba doguwar rigar atampha da qaramin gyale ta fice batare da ta nemi hajiya ko marwan ba.
Tun acikin mota ya xuba mata idanuwa, irin kallon da yake mata tasan duk baxai wuce gyalen da ta dora a kafada bane,ta zumbure baki bayan ta daure fuska ta bude motar ta shiga, duk sai take jin wani iri.
Wani murmushi ya subulcewa fuskarta lokacin da taga sun hau titin unguwar su, ta gefen ido yake kallon yanda take wannan farin ciki kamar wacce xaa kai aljanna.
Cikin mintuna da basu wuce ashirin ba suka iso gidan,
Minti biyar kacal na baki ki shiga ku gaisa ki fito yanxu yayi maganar yana kallon wani gu kamar ba shi ba.
Komai nata ya tsaya cak,duk wani farin cikin ta ya gushe tayi rau rau da idanu tana kallon sa kamar xata fashe da kuka,
Tace baxaka bari da dare ba idan kaxo mu tafi.
Yace nooo yanxu xaki fito ina jiran ki.
Dan Allah kayi haquri ta fad'a kamar xata riqo hannunsa ta rarrashe sa, nasan kai mutumin kirki ne tuntuni na gane hakan.Murmushi yayi batare daya kalle ta ba, yace tau banajin yin kirkin ya kenan.
Tayi shiru batare da ta fita daga motar ba, yace kina bata min lokaci fa,
Tace ni baxan iya xuwa nayi minti biyar kawai aciki ba, shikenan na haqura ka maidani gida.
Olryt tam ya fada ya tayarda motar batare daya bi ta kanta ba ganin da gaske yake tafiyar xai yi sai ta fashe da kuka, ya juyo yana kallon ta cikin mamaki, kukan na menene kuma?
Dan Allah kayi haquri ka barni, shikenan jeki anjima da dare xan xo na d'auke ki idan na dawo daga asibiti hakan yayi maki.
Ta gyad'a kai da sauri tare da balle murfin motar xata fice yayi saurin riqo ta kamar a mafarki taji saukar hannunsa a nata ta juyo da sauri tana kallon hannun nata dan tabbatar da xargin ta kafin ta d'aga kai tana kallon sa, shima ita d'in yake kallo kafin yace haka xaki fita da hawaye a fuskar ki, tukunna ma ke ko kwalliyar da mata suke yi idan xasu fita baki iya ba, just look at you, a gida ma naga bakya yi ko miye dalili?
Ta soma qoqarin janye hannun ta daga riqon da yayi mata amma ta kasa, sai taji wata kunya data tuna yanda ta fito d'in saboda murnar xata je gida, kallabin Ma a baibai ta d'ora shi aka ga qaramin gyale da ta d'auko, amma meyasa ya damu da tayi kwalliya ko a gida ne yana so ne?
Kayi haquri ta fada cikin sanyin murya kamar ba ita ba, ya d'auke hannunsa daga nata kafin ya tabe baki batare da yayi magana ba, ta fita daga motar yana kallon yanda ta shiga cikin gidan da gudu, ya girgixa kai kawai kafin ya bar harabar gidan.
Tun qarfe goman dare take jiran xuwan sa tare da tunanin fad'a da nasiha da umma tayi mata tun bayan bata labarin irin xaman da take yi da mijin ta, dole xata gyara rayuwar auren ta kamar yanda ummanta ta fada idan ba haka ba xasu raba hanya xata daina ko amsa gaisuwar ta.
Horn d'in motarsa ya ratsa kunnuwan ta da sauri ta soma harhada kayan da umma ta bata ta je dasu, batayi tsammanin shigowar sa ba sai ganin sa tayi tsakiyar falon bayan yayi sallama, umma ta fito suka gaisa kana ya fita tabi bayansa tana yiwa umma bye bye.
Ganin qatuwar jakar da take janye da ita a bayansa ya saka shi kallon ta da mamaki, to ko dama bata je da kayanta na sakawa bane yake ganin ta d'auke da kaya haka, ta saka jakar a jaka suka bar gidan, suna isa gidan kamar d'axu ta fice da sauri ta barshi acikin motar.
A falo ta sami hajiya da marwan ta xauna cike da farin ciki tana xayyano mata irin tarairayar da umma tayi da ita da kayan da itama ta bata a matsayin tsaraba, hajiya tayi dariya tare da fad'in ashe ma xarah da marwan duk d'aya ne babu banbanci baa san an girma ba dai dai lokacin saif ya shigo janye da kayan fuska a daure na ganin ta raina masa wayo na barin trolly d'in ya shigo da ita, a falon ya ajiye ya tafi abinsa.
Ba dai duka kayan nan bane tsarabar da kike magana xarah, tace duk sune hajiya bara na bud'e maki ki gani harda kayan da Abbana Ma ya bani duka suna ciki
Hajiya tace aa ki barshi dare yayi kije ki kwanta nima barcin nake ji gashi gobe da wuri xan bar maku gidan.
Ta langabar da kanta, hajiya ki xauna da mu kada ki tafi.
Xan dawo wani lokacin xarah tashi ki tafi, ba musu ta tashi janye da kayan xuwa d'akin ta, wanka tayi ta shirya cikin kayan barci, tana qoqarin kwanciya ya shigo d'akin qamshin turaren sa ya had'e da nata ya bada wani qamshi mai shiga rai da sanyaya xuciya, kallonsa tayi lokacin da yake qoqarin kwanciya akan gadon, hankalinta ya tashi a ina yake so ta kwana meyasa baxai kwanta inda ya saba kwanciya ba, ta d'auki pillow tana bata fuska ya dube ta tare da fad'in kada ki damu xo kiyi kwanciyar ki, ba musu taje ta kwanta nesa dashi a takure murmushi kawai yayi ya juya mata baya.
Washe gari a airport idanunta sun yi rau rau lokacin da hajiya ke shiga jirgi sosai take son matar bata da matsala kuma tana xaune da ita kamar yar cikin ta duk taji ba dad'i ta soma hawaye, har suka iso gida tana kuka bai san irin shaquwa hajiya da xarah ba, tun jiya hajiya ke damunsa da xancen xarah akan ya kula da ita kada ya cutar da yarinyar mutane.
Janyota yayi ya had'a da qirjinsa Karo na farko a xamantakewar su bayan sun shiga d'aki, jikinta ya d'auki rawa ta nemi hawayen da take ta rasa tana jin yanayin da bata taba jin irin sa ba haka shima a nashi bangaren, a hankali ya kai bakinsa gefen wuyanta yana shaqar qamshin jikinta, ya sumbaci bakinta xuwa qirjinta, duk wasu qofofin sadar da jini cikin gangar jikinta sun daina aiki sun karbi sakon da bakori ke turawa a kowacce kusurwa ta jikinta.......