JARABTA PAGE 16

246 2 0
                                    

🌹🍃🌹🍃🌹
🍃.•°''°•.¸.•°''°•.🍃
🌹                    🌹👈
*🍃JARABTA😭🌹*
🍃'•.¸            ¸.•' 🍃
     🌹° •.¸¸.•° 🌹
           🍃  🍃 ,
  🍒🌹🍒🌹🍒🌹

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_{Gidan karamci, rubutu don cigaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.}_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/106494781436168/

         🇼​ɾίttεη
             BҰ:​
ᕼᗩᒍᒍᏆᎩᗩ ᗰᗩᖇᎩᗩᗰ
─────────────

*M͟a͟r͟u͟b͟u͟c͟i͟y͟a͟r͟:*
➪FYADE 2020
➪KOMAI NISAN JIFA
➪ABBANA NE
➪ILLAR LUWADI
➪UZMA
➪'YAN BARIKI
AND NOW
*JARABTA*
TRUE LIFE STORY
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
*Dedιcaтed тo:*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
➪HAMDALA
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
*JARABTA GROUP  1*
*BARABTA GROUP 2*
*JARABTA GROUP 3*
*INA DAF DA ZUWA HUTU DOMIN COMMENT ƊINKU YANA YIN ƘASA🙄🙄🙄*

BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM

*🇵​αɡε ➪☾16☽*





            Na ce
"Amma Bello kana ganin anyi min adalci kenan? "
Bello ya ce
"Ki yi haƙuri kowane bawa da irin JARABTAR da Allah yake yi mai ke kuma taki irin Jarabawar kenan kuma bawai Allah baya sane da ke bane shi kaɗai yasan irin tanadin da ya yi miki ranar gobe ƙiyama ina mai baki shawara da ki ƙara haƙuri domin wasu mutanen ba sa iya jure jarabawar Allah wasu sukan kashe kansu akan abinda bai kai ya kawo ba, wasu kuma su haukace kagansu suna tafiya suna sambatu wasu kuma su koma saɓon Allah dan haka ki yi ƙoƙarin danne zuciyarki Allah zai kawo miki ƙarshen wannan matsala taki wata rana sai labari "
          Na ce
"To Allah ya sasauta min"
Muna cikin haka na jiyo muryar Ammi tana kwala min kira cikin sanyin jiki na fita na same ta ƙofar ɗaki ta ce
"Dama abinda yasa na kira ki kikwashe kayanki daga cikin wancan ɗakin gobe idan Allah ya kaimu za ayi jeren kayan Shukrah a cikinsa"
Kaina a ƙasa na ce mata
"Allah yakaimu"
Na miƙe nabar wajen
Bayan na juya baya naji tana cewa
"Shegiya mayya jikar mayu wallahi sai kinbar gidan nan tunda ba gidan ubanki bane"
Nidai ban juyoba na ci gaba da tafiya ina shiga ɗaki na duƙun ƙune na kwanta ga ƴata sai faman kuka take bani da Nonon da zan ba ta haka dole na tashi na samu dusar awakai na tace ruwan na samu na bata tasha muka koma muka kwanta, washe gari da kwalema aka tashe mu Ammi ta yi ta min shuri da kayana daman ba wasu kayan arziki gare ni ba jin hakan ya sa na miƙe na kwashe kaya na na dawo dasu ɗakin da nake, a daren ranar Shukrah ta tare habaici babu wanda bansha ba amma na danne zuciyata shima mijin namu ya fara canza min wannan duk ban ɗaukeshi komai ba saboda nasan lallai ne kowane ango sai ya yi ɗaukin amarci na ci gaba da haƙuri wajen wata biyu amma zaman mu babu daɗi ga yarinyata duk ta rame ta lalace ta koma kamar irin yaran nan masu ciwon ƙanjamau saboda rashin abinci da Nono ga baƙin cikin miji ga na uwar miji gana amarya koda mijina ɗakina yake wallahi banida saƙat dana kaimai ruwan wanka Shukrah za ta faɗa inaji ina gani zasu yi wanka tare su fito nayi kuka na yi kuka har na gaji ganin abun ba na ƙarau bane nima na gyagije kullum cikin bala'i muke babu dare babu rana, wata ranar Alhamis da ba zan taɓa mantawa ba muka tashi  da sabon al'amari yarinyata ta yi ta kuka amma Ammi ta ce ba za a kaita Asibiti ba duk na ruɗe magani mu dama wannan mu kwaba wancan har dai yarinyar  ta ce ga garinku na yi kuka na na gaji babu me lallashina sai Allah gida koda na kai ƙara sai dai a bani haƙuri nida Shukrah kuwa kullum cikin dambe muke bayan rasuwar Ilham da wata biyar na ƙara samun wani ciki na biyu shima nasha wahala fiye da na farko nace zan koma gida Bello ya ce bai yadda ba, da daɗi da ba daɗi haka naci gaba da zama har Allah ya sauke ni lafiya a lokacin itama Shukrah ta haifi ƴarta watanta biyu sai Bello ya roƙi alfarmar ta shayar da yaran su duka, babu musu ta amince amma kullum ni nake yi musu bauta ba da dare ba rana ga gori da ake yimin  kullum wata ranar lahadi muka tashi da faɗa tun safe na kama Shukrah na ɗirka mata dukan tsiya tun daga ranar ta ce ba za ta kuma shayarmin da ƴa ba aka yi roƙon duniya amma taƙi ga yarinyar da masifar kuka kullum dare bama bacci daga ni har babanta itama haka ta yi ta ramewa tana ƙarewa har Allah ya amshi abarsa, sai a lokacin na fara shiga mutane nayi ƙawaye da masu taimaka min da masu bani shawarar nayi family planning duk nayi na'am da zancensu na shawarci Bello amma yaƙi amin cewa nima dole na haƙura

         ****         ******      *******  

      Ummi ta ce Mama kinji yanda muka yi tunda ya ce goben a kai Suhail to zan tashi da wuri muje, yanzun ma duk jikinsa ya yi zafi "
Mama ta karɓi Suhail ta yi mai addu'o'i ta shafa mai ta ce na bashi paracetamol na yara banyi musu ba na ɗauko na bashi a nan wurin ya samu bacci nima sai yau na fita tsakar gida na zauna ina taya su aiki muna hira, sai matar babana ta biyu ta ce
"Ummi me zai hana ki runƙa yi mai ruƙiya ina ganin wannan lamarin kamar akwai sharrin aljanu a cikinsa da mayu sannan inada wasu magunguna na mayu na haɗa tazargadi da Habbatussauda da tsakin kuka kullum kina yi mai hayaƙi dasu zan ɗauko miki su ki fara yi mai kafin muga ya hali zai yi" na ce
"To Anty Nagode "
Ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko ta haɗa min garwashi a kasko na shiga ɗakin dashi na fara turarawa Suhail na bacci sai ya fara kuka yana miƙa na yi sauri na ɗaukesa ina ta tofa masa ayatulƙusiyyu sai kuma ya koma bacci ranar munyi bacci cikin daɗin rai dan wannan kukan duk bai yi shiba, washe gari muka nufi gidan Malam gwani tare da jagorancin Babana koda muka isa yana zaune kan dadduma ya idar da Nafila yana lazimi muka zauna sai da ya idar muka gaisa ya ce dani
"Kece mahaifiyarsa? "
Na ce mai
"Ehh"
Ya ce min
"Tun yaushe yake fama da wannan lalurar"
Na ce masa
"Yau kimanin wata biyar kenan tun haihuwar sa"

Sai ya ce
"Wannan matsalar tana da nasaba da ke domin kema babu shakka akwai matsalar da take damun ki? "
Na ce
"Gaskiya ne malam nima ina fama da matsaloli da dama"

Ya ce
"sannan kema ya kike ji a jikin ki" na ce
Tun asalin faruwar matsalata tun ina budurwa kafin nayi aure nake samu matsaloli a jikina har ila yanzun ina fama da ita

     WACECE FATEEMA

            Sunana Fateema Ibrahim wacce dumbun jama'a suka fi sanina da Ummi asalinmu ƴan nan garin  Maiduguri ne wannan bawan Allan shine mahaifina,  mahaifiyata ta rasu tun ina yarinya a lokacin mahaifina ya miƙani wajen ƙanwarshi amma ba wacce suke ciki ɗaya ba ita kuma tana Zaune ne a Oyoyo state Ibadan a Unguwar Akinyale tun da na tashi ban san rashin uwa ba domin duk wani abu da me uwa ke samu nima ina samu a wajen Hajiya Kulu wacce ake cewa Chiminani Chimina yana Nufin takwara da yarenmu na Barebari



         SAKATARIYA✍🏼

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 20, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Labarine akan ƴan lesbian Where stories live. Discover now