DA NASANI PAGE 1 TO END

459 3 3
                                    

*DA NASANI*

*wannan labarin labarine na gaskiya ba qagaggen labari bane. Na Jima da rubutashi tun kafin nasan qa'idojin rubutu, Dan haka marubuta ayimin uziri idan anga nayiwa adabi hawan qawara😂*

*ZM Chubaɗo✍️*

*_Bisimillahirrahmanurrahim_*

*_Page: 1 to end_*

*GARIN KANO*
Unguwar Rijiyar Zaki da misalin ƙarfe 10:30pm na dare, gidane Babba me kyau da ƙawatuwa, duk wani kayan Alatu na rayuwar Duniya an zubashi a wannan gidan tundaga farkonsa har zuwa inda katangar gidan ta kare, Unguwarmu unguwace ma'abociyar manyan gidaje. dukda cewa Unguwar ta masu hannu da shuni ce amma a kwai tsattsamar zamantakewa a tsakanin mu, duba da yanda muke rayuwa babu me shiga harkar kowa.

da mutum ɗaya Kacal nake hulɗa a makotana ita ce Jameelah. sabida a Rayuwata na tsani ƙananan magana da kwashe-kwashen kawaye,

Tun da sauran haske wajen gabatowar lokacin sallar isha'i nake jiyo sautin kuka daga gidan Jameelah, a raina ban kawo komai ba na cigaba da kimtsa yarana na mukayi kalacin dare sannan na kaisu ɗakunansu suka kwanta kasancewar mijina baya gari yayi tafiya zuwa ƙasar Amurka, bayana na koma ɗakina ina shirin kwanciya na sakejin wannan sautin wannan kukan da kunnuwana suka ji daga gidan jameela ɗazu, zuciyatace ta fara saƙamin cewar "anya kuwa wannan kukan da nake jiyowa na lafiya ne ?"

Kawar da tunanin nayi da sauri sbida bana son shiga hurumin da ba nawa ba, a haka har bacci ya fara ɗaukata, sama-sama nake jin sautin kukan kamar a gidana akeyi, da sauri na miƙe na leƙa ta window don ƙara tabbatarwa, haryanzu dai daga gidan Jameelah kukan ke tashi.

Wayar dake gefan gadona na jawo na shiga kiran wayar mijina Dukda cewar a Ƙasar da yake A wannan lokacin darene sosai, cikin sa'a kuwa na sameshi nan da nan na shiga shaida masa abinda ke faruwa tareda neman izininsa kan cewar Idan har ya amince min to zan shiga gidan jameelah na gani ko lfiya, ɗan jim yayi kaɗan sannan yace

" kinga ki kula sosai fa Hafsa, banason wani abu ya taso akan wannan lamarin ballan tana wata magana nikam da zakiji ta nawa ma wllh danace karkije musu gida, wllh banason problem da kowa a unguwar nan Ballantana kuma da Hafiz wanda ko gaisuwar kirki ba haɗamu take dashi ba.

Ya faɗa yana sauke numfashi cikin nutsuwa.

Marairaice masa nayi tareda bashi tabbacin insha Allah baza'a samu wata matsala a sanadina ba, kasancewar yasan nima bame son fitina bace ko ƙananan magana yasa bansha wata wahalaba ya amince min da inje ɗin, Hijjabina na zura akan doguwar Rigar dake jikina na fito, takalma na kawai nasaka sannan na sanar da Murjanatu me Aikina ta kular min da yara zan shiga gidan Jameelah Na dawo, da to ta amsa min sannan na fice zuciyata duk a dagule.

A haka na isa ƙofar Get ɗin gidan me gadinsu ya buɗemin na shiga kasancewar yasan ni, abinda ya ƙara ɗagamin hankali guda ɗaya ne tundaga farfajiyar gidan nakejin sautin Wannan kukan dai gamida shashsheƙa me matiƙar taɓa ran duk wani me Imani, hakanne yasa na ƙara ƙaimi wajen ganin na isa ga Ainihin ƙofar babban falon gidan inda Sautin Kukan ke fitowa.

Da sallama na tura ƙofar Falon cikeda son tabbatar da zargina, Jameelah ce zaune Dirshen ta saka ƴarta guda ɗaya da Allah ya bata Hanan a gaba tanata Gurzar kuka kamar Ranta ze fita, a haka na ƙarasa har inda take jikina a matiƙar saluɓe sabida rashin ƙwarin gwiwa.

Harna isa gareta batama san da shigowata ba Sabida tsabar tashin hankalin datake ciki seda na taɓa ta, a firgice ta maida kallonta gareni idanunta na tsiyayar ƙwalla ta ƙanƙame hannuna tana me ƙara sautin kukan ta, al'amarin daya ƙara tayarmin da hankali kenan, da ƙyar ta iya tsaida kukan datakeyi ta kalleni cikeda Rauni tace "don girman Allah Hafsa ki taimakani ki bani Dubu biyar intafi gidan mu kozan samu ƙarshen Rqyuwata yayi kyau Kamar kowace mace Hafsah, wllh ina cikin masifa da tashin hankali!!! Ta faɗa tana rushemin da kuka.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 27 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DA NA SANIWhere stories live. Discover now