🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*HALITTA DAGA ALLAH NE*
🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
Na
*Zahra Abdul*
(Momyn ahlan )_MY FIRST NOVEL_
EDITING.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
=========
Bismillahi rahmanir rahimPage 1&2
,,,,,,,,,,,,,,,,, tana tsaye ta zuba masa ido ji take kamar taje ta hadiye shi sbd tsananin soyayyar da take masa, ta jima tana kallonsa tana ayyana abubuwa da yawa a kansa yayinda shi kuma hankalinsa sam baya kanta bai masan da zuwanta ba,
Hankalinsa ya yi quloluwa wajen kallon abin sonsa wato abin alfaharinsa.Wata yar budurwace kwance akan kujera 3seter wacce ba zata wuce shekaru 25 ba a duniya, tana bacci kallonta kawai yake yanajin wani irin farin ciki da annashuwa a game da ita.
Wannan budurwar da take kallonsa ne wadda bai ma san da zuwanta ba
Ita ce ta ce: "Yaya Abbas
Ina... INA.... kwana" juyowa ya yi yana kallonta ya hade rai
a daqile ya ce "lafiya" ita kuma ta saki murmushi.Takowa tayi tazo gabansa ta sa hannunta ta shafi gefen fuskarsa wadda kullum qara kyau yake mata, cikin jin haushi ya buge hannunta
Ba taji haushi ba illa ma dai rungumesa da tayi cikin zafin nama ya bankadeta ai kuwa ta buge da table din parlor din ta dan saki qara hakan ne yasa dayan yarinya dake bacci ta farka a tsorace tana waige-waige kawai sai ta ga Yaya Abbas a tsaye ga kuma HEEDAYA kwance a kasa tana kuka mai cin rai saboda wulakancin da Yaya Abbas yake mata yayi yawa amma maimakon ta tsanesa amma kullum qara sonsa take, da hanzari wacce take kwancen ta miqe tana cewa "sannu Hidaya ina dai ba kiji ciwo ba ko?" kallonta ba tayi ba, zata tashi kenan taqara komawa ta fadi saboda kanta ya bugu sosae dan harya tashi gurin yayi ja abunka da farin fata, HABIBA ta qara yunqurin zata taimaka mata ta daga mata hannu alamun karki kuskura ki tabani,
abinda ya qara bata haushi ya tureta amma kota kanta bayyi ba ma yayi gaba abunsa ya shige bedroom dinsa.Hidaya ma dai part dinta ta wuce tana kukan takaicin abunda Yaya Abbas ya mata.
Shi kuma yana shiga dakinsa ya fara masifa cikin jin haushi.
"mtsww! ita wannan yarinyar bata da kunya ko kad'an! ko ta ga ni Abbas sa'anta ne ni oho! yarinya qarama amma Sai baqar rashin kunya! Ni mai zanyi da ita bandama kaddara mtsww!" yaqara jan tsaki dai-dai nan ne Habiba ta shigo dakin a natse gami da sallama yana ganinta yaji duk wani bacin ransa ya kau ya sakar mata murmushinsa mai tsada ita ma murmushin tayi masa, ya taso ya rungumeta yana lumshe ido
Cikin sanyin murya ta ce masa "Habibina dan Allah ka daina yi ma Hidaya haka wallahi bana jin dadi ka ji?" ta qarasa kamar zatayi kuka dan har kwalla ya cika idonta,
Jikinsa ne yayi sanyi don shi baya son bacin ran Habiba ko kadan, ya kalleta ya ce "to Hibbata na bari" ta shagwabe fuska ta ce "ai kullum haka kake fad'a ka bari amma kuma baka bari ba."Ya ce "to shikenan naji yau nace ba zan sake ba kinyi farin ciki?" ta sake shi ta juya masa baya ta ce "a'a idan ka naso nayi farin ciki kaje ka duba Hidaya
SBD ka ji mata ciwo a goshi ya kumbura" yatsine fuska yyi yana kallonta na d'an wani lkc kafin ya ce "to"
Ya juya ya fice daga dakin amma ba dan yaso zuwa wajen Hidayan ba a'a Sai dan dai kawai Hibbarsa tana son hkan ne.Yana fita Habiba ta sauke ajiyar zcy mai karfin gske, tana sonsa kam fiye ma da yadda yake sonta amma bata jin ddin abinda yakeyi ma Hidaya.
Hidaya kuwa tana shiga part dinta bedroom dinta ta shige ta fadi a saman gado ta qara sakin kukanta mai karfin gsk tanayi tana sambatu, " why!,,,why!,,,whyyyyy!" ta fada da karfi.
"why! Yaya Abbas baka sona? miye aibuna da ka tsaneni!? I love you Yy Abbas! I love you Yy Abbas! I love youuuuuuu!!" ta fada ta ci gaba da kukanta.Tasan ko da zatayi kukan jini ne ba zai taba zuwa ya dubata ba Sai dai ita taje idan kuma taje tasha wulakanci ba kuma shi Zai hanata zuwa gobe ba.
Ga shi ta rasa wa zata kira ta fada masa damuwarta kuma tace ba zata qara gayawa Momma ba
SBD ta taba zuwa ta gaya mata akayi masa fada ransa ya b'aci, ita kuma bata son bacin ransa,
Haka dai tana kwance tana saka da warwara taji anturo kofarta ba tayi tunanin shi bane dan ba tasa a ranta Zai biyota ba.Ta dauka uwani ce wadda take tayata aikin gida da hira lokaci-lokaci, shiyasa ta qara lafewa a gadon dan bata son magana.
Shima kuma daya shigo ya ganta kwance yadda ta wani lafe can karshen gado ne yad'an ja tsaki "mtsw! dalla kalleta wata yar pirit da ita" shi fa a rayuwa baya so ya ga mace babu jiki, yafi son mace yar duma-duma
Bayan haka ma kam ai Hidaya tayi masa yarinya da yawa,
Ya yi nisa cikin tunani, ita kuma Hidaya da taji an shigo kuma ba a fita ba ya sa ta juyowa
Karaf suka hada ido da shi ai kuwa ta miqe da saurinta gami da sakar masa murmushi kafin tayi hugging nasa tana zuba masa hot kiss ta ko INA duk tabi tayi masa kace-kace da kaya, cikin zafin nama ya tureta.Ya fara mgn cikin daga murya "Haba wai ke wa ce irin jarabebbiyace kam! haba na gaji gsky! ke wace irin Marar kunyace!!" tsayawa tayi tana kallonsa
Ta ce "to Yaya Abbas me nayi kuma? laifi ne abinda nayi? bafa haram bane nifa matarkace kuma qanwarka" tsaki ya qarayi ya wuce ya fita yana mgn a zcyr sa "yaran yanzu da rashin kunya suke zuwa duniya, dubi yarinyar da aka Haifa agaban idonsa amma ji mganganun da takeyi" murmushi ya saki daya tuno lkcn da take ce mi shi nifa matarka CE
Tsaki yaja yana cewa "oh ni Abbas wannan yarinyar ce matata cab lallai, gani da Hibbata" hanya parking space yyi zai tafi office yana shiga wayarsa ta hau ringing yana dubawa yaga Anas ya dauka yace gani nan zuwa ya katse kiran yasaki tsaki kafin ya figi motar da karfi gateman ya bude masa yafice.Waye Abbas?
Wacece Habiba?
Wacece Hidaya?🌞🌞🌞🌞🌞🌞
*SAI FA HAKURI😂 BOOK DIN FARKO,WALA EDITING, KURAKURE JIBGI GUDA, A KARANTA HAKA DA HAKURI😂*
Comments
And shareBy
(Zahra Abdul)
( momyn ahlan)