🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
🌞🌞 *HALITTA DAGA ALLAH NE*🌞🌞
Na
*ZAHRA ABDUL*
(Momyn ahlan)Sadaukarwa gareki ƙawallita (Ummu Nasmah) na sadaukar da wannan page din gareki na ki ne kiyi yadda kike so da shi saboda addua da kuma karfin gwiwan da kike bani. Allah ya raya mana zuriar mu da dukkan musulmai na dunia baki daya (Ameen ).
Page 0⃣2⃣
Bismillahi
,,,,,,,,Abbas Alhaji Mustapha Hamza shine cikakken sunansa.
Mahaifinsa Alhaji Mustapha ɗa ne wajan Malam Hamza,Malam hamza haifafen garin bauchi ne
yayi karatun almajiranci sosai ta yadda ya gaji wani malaminsu Mlm Shehu.Mlm Shehu sananne ne, lokacin da aka kawo hamza karatu makarantarsa ya yaba sosae da hankalin hamza kasancewar mlm shehu baya da yaro namiji Wanda zai gajesa, 'yarsa ɗaya tilo a dunia wato ummu salma
Yarinya CE mai hakuri ga tarbiyya ga sanin yakamata ko da ake cewa wani lokaci ɗan Malam baya halin Malam amma ita kam salma tayi halin Malam.Akwai wata rana salma taje kaiwa mahaifinta Malam shehu abinci hamza tunda ya ganta yaji zuciyarsa ta buga
Itama kuma ta bangarenta hakan ce ta faru
Tun a ranar hankalin hamza ya tashi domin ya fahimci daga kallo daya ne ya afka kogin kauna.Haka dai yayi ta dakon soyayyarta itama din hakane a wajanta.
Wani lokacin ma sabida ta ganshi ne take kawowa babanta abinci duk da bata son fita.
A haka dai hamza yana ta tunanin yadda zai ce yana son Ummu salma sabida 'yar gidan malaminsa CE.
A haka dai ana cewa abinda babba ya hango yaro koya hau rimi bazai hango ba.
Mlm shehu har ya fara gano 6oye-6oyen da hamza da yar'sa salma tilo sukeyi.
Amma tun kafin ya faɗawa hamza sai da ya zaunar da salma yace mata yanaso ya hadata aure da almajirinsa hamza tanason shi? ai kuwa ta miqe da gudu tayi daki tana dariyan farin ciki mamarta tasa albarka kafin yasa aka kira masa hamza yace yanaso ya haɗashi aure da yar'sa salma hamza yaji dadi sosai haka Mlm shehu ya zamo uwa da uba wa hamza kasancewarsa ya taso maraya.
Haka akasa ranar auren salma da hamza
Masu baqin ciki sunayi masu farin ciki sunayi.Rana bata karya ranar jumma'a aka daura auren
Ummu salma Mlm shehu
Tare da hamza nayaya Mlm shehu.Zaman lpy sosai sukeyi gami da qaunar juna.
,,,,,,
haka dai rayuwa take ta tafiya a kwana atashi asaran mai rai.Wata rana Mlm shehu ya hada dukkan almajiransa yace musu ko bayan ransa hamza shine d'ansa kuma shine magajinsa
Saboda hankalinsa da baiwarsa na ilmi.Bayan Mlm shehu yayi wannan jawabin ne baifi da sati 2 ba wata ranar laraba yatashi da ciwon cikin gaske kafin hamza suyi ƙoƙarin kaisa asibiti yace ga garinku nan.
,,,,,,,
Allah sarki rayuwa kullu nafsin zaa,ikatil maut! Allah kasa muyi kyakkyawar kashe Allah yasa mucika da Kalmar shahada
Laah ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alayhi wa sallam ameen.,,,,,,
salma tasha kuka sosai harda hamzan ma da mahaifiyar salma amma kuma dole sai hakuri daga nan nauyi ya koma kan hamza.Ana hakane salma ta fara laulayin ciki hamza yayi farin ciki sosai harda mamanta shi kuma masha Allah makaranta tana qara bunkasa kafin kace me hamza ya shahara shima kamar margayi Mlm shehu dan yawancin ansanshi agarin Bauchi ayankin ƙasan gada.
,,,,,,,,
Haihuwa Ummu salma tasamu ɗanta namiji karkuso ku ga murna a wajan hamza ba tare da bata lokaci ba kuwa ranar suna hamza ya raɗa ma ɗansa sunan Malam wato shehu, anyi suna an watse lpy.Watan jariri mai sunan Malam 2 a duniya shima yace ga garinku hauka ne kawai salma batayi ba daga baya ta hakura ta bar wa Allah bayan rasuwan shehu ne taqara samun wani cikin ta haifi namiji shi kam ma tun kafin suna Allah ya karbi abunsa. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya sai da tayi shekara 2 kafin taqara samun ciki amma a tsorace take
Allah cikin ikonsa kuwa ta haifi 'yan biyu maza murna akasa musu suna Abubakar da UsmanShekaran su Abubakar 5 ta qara samun ciki ta haifi mace akasa mata sunan Maman salma wato zainaba suna kiranta da ummi awannan lokacin ne kuma Mlm hamza ya saka ummi a skull tana da shekara 3 aka sata a makaranta nursery skull wata malamarsu dama tasan mahaifin su Abubakar kuma ta jima tana sonshi a haka dai wata rana su ummi suna wasa kawai ta fado a saman bishiya ta karya kafa malamar ce ta kaita aka mata dauri daga nan ta kaita gida kullum sai taje duba ummi da ɗan lemunta a hannu.
A haka har suka saba da salma wadda a yanzu yaranta suke kiranta da suna Uwa.
Ba qaramin tasiri hajara (wato malamarsu Ummi) tayi ba acikin zuciyar uwa
,,,,,wata rana tazo mata ziyara ranar babu makaranta
Suna cikin hira sai uwa tace
"hajara ke ba zakiyi aure bane?" sai tace saina samu miji malami kamar naki, shuru na ɗan lokaci uwa tayi kafin tace to Allah yabaki.,,,,
rayuwa tana cigaba da tafia kwanansu abubakar 2 ba suje makaranta ba hakan ne yasa hajara tace bari taje ta duba ko da tazo sai uwa tace mata mamarta ce babu lafiya shiyasa basu je ba duk da tasan ciwon mahaifiyarta bazai shafi karatun yaranta ba. hankalin hajara ba karamin tashi yayi ba kullum tana gidab mamar salma wato uwa tanayi mata hidima.Bayan sati da hakan itama mama tace ga garinku nan.
Aallah sarki mama tabi Mlm
Allah ya jikan magabatanmu damu baki ɗaya ameen.Hajara tayi kuka sai ka rantse ko mamartace ta rasun ko da uwa tayi mata magana akan kukan ya isa haka sai tace mata itama batada iyayen tun tana qarama sukayi hatsari suka rasu ko fuskansu bata sani ba.
Ba karamin tausayi tabawa uwa ba.
Bayan anyi adduar uku wa mama mutane anwatse uwa taje tasami Malam tace mi shi tanaso ya auri malamarsu ummi ta makaranta kallonta kawai Mlm hamza yakeyi ba tare da ya iya furta mata kalma ɗaya ba.
****************
mu hadu a page na gaba ta yadda zamuji shin mlm hamza zai yarda ya auri hajara ko kuwa.****
ta Ku
(Zahra Abdul)
(Momyn ahlan)
Comments
And
Share.