13&14

1.6K 29 5
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*NA GAISHEKI SIS NA🥰 SURRY BABY, ALLAH YA BAR MIN KE.*

*AZIMA DA AZIZA GRP NA GAISHEKU😂 MASU MAFARKAI DA TSORATA NA JINJINA MUKU, A CI GABA DA CHAPTAWA.*🤙🏻

*FREE..*
🅿️==1️⃣3️⃣↪️1️⃣4️⃣

"Zaran saƙar dana kuma?" Hajja ta faɗa tana kallon hannun Baffa da ya riƙe zaren yana kalla, Aziza ce ta matso kusa da  Baffa ta duƙa ta ce
"Baffa me zaran ya ƙunsa?" shuru Baffa ya yi na wasu lukota kafin ya ce
"Ba ƙaramin hatsari wannan zaren yake da shi ba, ana amfani da shi wajan yaƙi! Ko kuma a ɗaure takwabi da shi, duk wanda aka sara ko aka yanka da takwabin da aka d'aure da shi to sunansa gawa! Walau mutum ko aljan! " a firgice Aziza ta ce
"Kenan mutum mutuwa zai yi?"
"E Aziza, wa ya kawo zaran nan gidan nan? Sannan ta ya aka samo shi? Dan nasan ba a samunsa nan kusa sai an je can cikin jejin lore, wanda wannan jeji tun kafuwarsa shekaru aru-aru  babu wani ɗan adam din da ya taba zuwa idan ba ni ba"  Hajja ta ce
"Ai kuwa dai Azima ce na ganta da shi dan tun safe take zaune a inda ka tashin nan take saƙa shi,bayan ta gama ta shige ciki, bata jima da shiga ba ka shigo" da sauri Baffa ya miƙe tsaye ya ce
"Azima! Azima! Azima!?" ya kwala kiran sunanta da karfi, Aziza ta ce
"Bari na kirata Baffa" cikin faɗa Baffa ya ce
"Nan da bukka ta ce bata jin kiran da na mata?" Hajja ta ce
"Ayye Baffan yan biyu ka bi a hankali mana, watakila bacci ne ya kwasheta Aziza kirawota"  Baffa ya ce
"Ke da kika ce ina shigowa bata jima da shiga ciki ba shine har bacci zai kwasheta?"
"Ai Azima bata da wuyan bacci" cewar Hajja, shi dai Baffa shuru ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya maida hannunsa baya yana jiran fitowar Azima.

    Tana kwance a gadon kara, rabin jikinta macijiya sai juyi take yi kanta a hargitse, Aziza ta shigo da sallama ko amsawa Azima bata yi ba, Aziza ta ce
"Ba ki jin Baffa na kiranki ne?"

        "Mtswwwww! Na ji mana, tunda dai ni ba kurma ba ce! Je ki ce ba zan zo ba!" a fusace Aziza ta sa hannnu ta janyo wuyar Azima ta ce
"Wallahi! Wallahi! Wallahi! Kinji na rantse miki ko? To sai kinje, kuma dole ki ba wa Baffa amsar tambayoyin da zai miki, za ki tashi ne ko sai na b'ace dake a dakin nan na wujijjigaki!?" Aziza ta karasa maganar idonta da fatar jikinta suna canza kala, ganin haka yasa Azima miƙewa fuuuu ta fice, rufe ido Aziza ta yi ta dawo dai-dai sannan ta bi bayan Azima, a tsaye ta sameta Baffa na tuhumarta inda ta samo zaren sakar dana, cike da rashin tsoro da rashin kunya ta ce
"A inda ake samu na samo!"

AZIMA DA AZIZA (🐍MACIZAI NE🐍)Where stories live. Discover now