🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ƳAN BOKON ƘARSHEN ZAMANI_*
*NA*
*KHADIJAH USMAN*
( _Real tame gari_ )*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
1
_Ina mai bawa ɗaukakin masoya na haƙuri game da jina shiru da kukayi akan littafin da nake rubuta muku,hakan ya faru ne sakamakon wasu dalilai masu muhimmanci,dan Allah kuyi hakuri Nagode da soyayyar da kuka nunamin,hakan yasa naga bazan iya ƙyaleku haka ba,na kawo muku wannan labarin mai taken ƳAN BOKON ƘARSHEN ZAMANI,ku dai ku biyo ni mu antaya dan jin yadda nasu salon yazo da wani irin caskalewa kumu antaya kawai_ 🤣🤣🤣
*_Ƙauyen Ɗandila_*
Yara ne birjik da yawansu zai kai hamsin da ɗoriya,an jera su a layi kamar a makarantar allo, kowanne hannunsa ɗauke da jaridar kosai wasu ma takaddun tsire ne da alama,dan ganin yadda takardar ke maiƙon da inada yakinin ko an ɗora mata alƙalamin rubutun bazai zanu ba,wasu kuma kwali ne a gabansu,kai zan iya cewa duk wani nau'in abin rubutu wato dai na takarda da aka san zai ɗauka ba kuma za'a saya da kuɗi ba to yana nan gurin,idan ka tsaya kayi duba da yadda takardun suke a cike da kalolin zanen da ban gane musu ba,zaka yi tunanin ko rine aka sa yaran suyi,dan suyi kamfala da takardun,dan wajibi ne fa duk wani wanda yake zuwa wannan makarantar yana da fensiri ko biro, waɗanda iyayensu suka bawa karatun muhimmanci sune harda siya musu biro, wasu ma ja aka siya musu dan sufi kowa,masu karamin ƙarfi ne aka basu fensir wai a zuwan su ɗin ƴaƴan talakawa ne,kuma basu bawa boko muhimmanci ba.
Miƙewa sukayi gaba ɗaya da sauri cikin haɗa baki suna faɗin *tony mama! Tony San* !.
Da sauri na juya na kalli wanda akewa wannan kirarin,nan fa na ruɗe cike da tunani.Yara ne da shekarunsu a ƙalla zasu kai sha biyar,mace ce da namiji,abinda yasa na bambance,saboda shigar da sukayi,dn yadda suke tsananin kama da juna fiye da tunanin mai tunani,Ita Macen tana sanye ne da riga da sicket,wasu burguza-burguzaz,yayin da ƙafarta ke sanye da takalmi cover shoe,ta Sanya gilashi fari wanda ya dan yiwa fuskar tata girma,sai wani ƙaramin hijabi data saka,samansa kuma ta ɗora wata babbar hular kamar malafa,hannunta riƙe da wani ƙaton littafi da wasu ƙanana data rungumo a ƙirjinta.Shi kuma namijin yana sanye ne da wando da riga,sai wata ƙatuwar coat kamar wani lauya,ko ina ya samu rigar oho? Shima hular tasa a kansa kamar malafa,yayin da hannunsa ke riƙe da tarin biruka da wasu littattafai shima,shima da glass a hannunsa,amma bai sa ba.Kallo na na kuma kaiwa gefe,inda tarin ɗanyun bulalai shataf ke tare,kai kace damin ciyawa ne,yaran da har yanzu suke a ƙame kamar sojoji suna fareti nabi da kallon tausayi,domin dai har yanzu vda alama suna jiran a amsa musu gaisuwar nanne da sukayi kuma a basu iznin zama.
Sai da suka gama shan ƙamshin su da hura hanci yadda ya kamata sannan Abdurrahman(Hassan) yace "yes ku zaunas". Yayin da yaran duk suka amsa da "yes lica".Shi kuwa wani murmushi ya saki a zuciyarsa yana mai kara jin girma da son kara kasancewar sa malami, musamman daya kalli gefen bishiyar mangwaron da maigari ke zaune yana hango yadda ake koyar da yaransu ilimin zamani,wanda a jiya daya kirawo su Amaturrahman(Usaina) sun sanar masa akwai yaran ma da gab suke da zana jarabawar zama likitoci,hakan yaƙara ƙarfafa gwiwar maigari,ya kuma ƙara godewa Allah da ni'imar da yayiwa garinsa na samun waɗannan ƴan baiwar malamai masu zaman kansukasancewar ba'a taɓa haihuwar ƴan biyu ba a garin,sune kuma suka zo da tarin ci gaba musamman fannin wannan ilimin na zamani.
Malama Ama.... Ce ta kalli tarin yaran ta hura hanci tare da ɗaga kai sama sannan bisu da kallo har zuwa kan wata yarinya bilkisu tace"ke bilki"! Jikinta na rawa duk da farin cikin Malama ta kirata,amma tsoro ya danne murnar,haka ta ƙaraso jiki ba ƙwari ta tsugunna tace"gani Malam...." Bata karasa ba taji saukar bulalar data sata gantsarewa ta callara kuka,nan fa taci gaba da zabga mata,da yarinya taga dai ba sarki sai Allah,aikuwa ta kwasa a guje tayi gida,nan Malama ta rakata da harara kafin tace"Aikuwa kinbar makarantar nan har abada kenan dan ubanki,kuma wallahi ko waye zai dawo dake bazamu karɓe ki ba,kinjawa danginku asarar karatun bokoko hegiya mai kan goruba". Shikam malam Abdul baice ƙala ba illah cigaba da yayi da abinda yakeyi wato rubutu,babu abinda zai baka tausayi ga yaran da aka tara,sai yadda aka tashi mutum biyu a ciki sune zasu riƙe allon da za'a musu rubutu dashi,wanda ba wani abun kirki bane wani kwali ne daya sha joni da jone-jone ba iyaka.A haka aka fara gabatar musu da karatun kamar kullum,wanda bayan sun gama koyar da darasi aka shiga fannin tambaya akan abinda aka koyar,nan fa yara suka kama raba idanu,dan su kansu malaman in za'a kashesu bazasu iya maimaita abinda suka koyar ɗinba🤣 haka dai aka bi kowa ana masa tambayar inya kasa a zaneshi har suka kammala da fannin da suka ɗauka sannan aka koma fannin faɗin sunayen dabbobi da turanci, wannan kam kusan kowa ya haddace shi,dan a ganinsu duk cikin karatun da ake koyar dasu sunayen dabbobin yafi komai sauki,dan haka ko da Malama tace "waye zai faɗa mana sunan mage da turanci,nan aka shiga rige rigen ɗaga hannu.Sai da ta gama baza ido kafin ta zaƙulo Nasiru ɗan gidan malam liman tace "yauwa Nasiru faɗa mana ya sunan mage da turanci?". Saida ya wula ya nisa sannan yayi murmushi yace "sunan ta MAG"in kuma suna da yawa a kira su da MAGES ,namijin kuma ana kiransa da MUZ,idan suma suna da yawa ana kiransu da MUZUROS ".RAFFFFFFFFFFFFFF!!!!!!!
Guri ya ɗau tafi,yayin da Nasiru keta sakin murmushin jin daɗin ƙoƙarin da yayi yau,da kuma yadda yaga malaman na gyaɗa kai alamar yaba masa,sai hakan ya ƙara sa masa son karatun sosai.
Wata tambayar ta malam Abdul ya kuma jefowa yace" to tunda Nasiru ya faɗa mana sunan mage waye zai faɗa mana na ɓera kuma? Dan muna son mu ƙara gwada yadda kuke fahimtar karatun".Da sauri Laure ta ɗaga hannu tace"Sunan ɓera da turanci Ɓerrr".
"Ku tafa mata" malam ya faɗa nan itama Laure ta hau murnar ƙoƙarin da tayi yau,a take a gurin aka naɗa Nasiru monita,Laure kuma asistan monita,babu ɓata lokaci aka tsige na baya,su Nasiru nata murna,yayin da wasu keta fatan suma a naɗa su wata rana,dan kusan kullum sai an canza monita,da zarar anyi tambaya ka amsa to fa kaine monita,kullum da i haka tsarin wannan makaranta ke tafiya aka gama biya karatu kowa ya watse yayi gidansu.*************************
"wallahi bazan yarda ba,wannan cin zali har ina,duk makarantar nan waya kai bilki ƙoƙari, yarinyar nan kwana takeyi yin karatu,kuma kaf ƴan gidanmu Babu wanda bata iya sunansa da turanci ba,kai inta so ma juya baki takeyi in mun mata magana sai dai ta bamu amsa da Yaren da ake koyar dasu,amma fa hakan bashi zaisa a maidamin ƴata jaka ba,kullum sai ta dawo gida tana kuka kamar ita kaɗai ce ɗaliba ni fa sam bazam lamunta ba wallahi a he". Ta ƙarasa maganar tana girgiza jiki da dukan cinya".
Uwar biyu dake tsaye tana kallonta tace"Banda abinki talatuwa kya zo nan ki tasa Ni gaba kina masifa,alhalin ban san hawa ba ban san sauka ba,kije can gurin masu laifin ki musu ni kam bazan iya da wannan maganar da kullum bata ƙarewa ba,kawai abinda zance miki kiyi haƙuri,kuma ki cire ƴarki daga makarantar su"."Ai ko baki ce ba dole zan cire ta, wannan boko ko ƙaddara"tana kaiwa nan ta figi hannun bilki suka fice,Uwar biyu ta bisu da kallo bayan ta riƙe haɓa a fili tace"Yau naga ikon Allah,Ni dai wannan makaranta ta yaran nan anya ba saina karɓo musu maganin tsari ba kuwa? Dan yadda aka sako su a gaban nan gaskiya nan gaba kaɗan za'a fara jefe min su,dan anga Allah ya basu baiwa,to aniyar kowa ta bishi,bari malam ya shigo gobe inyi sammako in tafi hauran kafi in anso musu taimako".Haka dai taita surutunta ita kaɗai ta hau kauda kayan dake makeken filin tsakar gidan.
*Wannan kenan*
****************************
"Dan Allah Alhaji ka taimaka kasa yaran nan a makarantar boko,wallahi ni harna gaji da ce musu gobe zaka sasu ko jibi,kullum damuna sukeyi ,kuma inka duba yaran nan kullum ƙara girma sukeyi ƙwaƙwalwarsu yanzu a buɗe take in suka kai wani munzali ba'a sasu ba karatun zai musu wuya wallahi".
Saida ya gyara zaman farin glas ɗin fuskarsa, bayan ya ƙara buɗe wani shafin na jaridar dake hannunsa ya ƙurawa wani hoto ido kamar mai nazarin wani abu,harta ma fidda ran samun amsa sannan taji yace"Tunda bakya gajiya da jin amsa ɗaya Kubrah bari na maimaita miki,Kin ganni nan" ya faɗa yana nuna kansa,"Tunda na mallaki hankalin kaina na fara gane rayuwa da gwagwarmaya karatun boko ke burgeni,tun ana yinsa kyauta naso nayi iyayena suka hanani,haka na tashi da son karatun dole na haƙura na rungumi kasuwanci,nayi faɗi tashi na tara kuɗaɗena,Ni kaɗai nasan irin wahalar da nasha na tara kuɗina tun da canma,sai dai zamani na tafiya da salo daban-daban, ina son yarana suyi karatun boko dan su taimaka min a wasu harkokina,to amma fa sai yanzu da zamani yazo kuma karatun ma yayi tsada sosai,ni kuma bazan iya kashe ma'udan kuɗaɗe ba akan yara dayawa suyi karatu ba,duk rayuwa tana da tsari,kuma ita dukiya ba'a son ana almubazzaranci,shiyasa na tsaya nayi tunanin yadda yara na zasu samu ilimi mai inganci,na yanke shawarar kashewa mutum ɗaya kuɗi yayi karatu koda zaiga ƙarshen biro ne,inya so shima yazo gida ya dinga koyawa ƙannenshi abinda ya koya tun daga farko har ƙarshe wannan ita ce hikima ta ina fatan kin gane ai".
Saida ta gyara zamanta kafin ta kalleshi cikin marairaice fuska kamar zatayi kuka tace"Haba yallaɓai,yau shekara nawa kana jiranshi har yanzu bai dawo ba,kuma yaran nan kullum daɗa girma sukeyi, tun kafin ka aureni kake cemin ɗanka na ƙasar waje yana karatu,gashi har yanzu dana zo na haifi yara huɗu suna ta girma amma bai dawo ba,kullum daga yace yana nan tafe ƙarshen watan nan sai yace ƙarshen shekara,ka duba lamarin nan,sai zuwa yaushe zai dawo? Kuma ma idan ya dawo ɗin shi da ba malamin makaranta ba inashi ina koyarwa,dole nasa uzurin zai gabatar ai ko? Tunda yana da iyali,dan Allah ka duba lamarin nan kaji Alhaji".
Murmushi yayi ganin yadda taƙarasa maganar,dan haka ya ɗan sassauta ɗaure fuskar da yayi yace"To naji zan duba insha Allah zan yi waya dashi ya gaggauta dawowa cikin satin nan"........*Ban fara posting ba saida na kammala shi idan har banga comments ba to alamu sun nuna bai karɓu ba,dan haka Inga comments ɗin da zai gamsar dani nima in suburbuɗo muku shi gaba ɗaya*
*Alƙalamin khady* ✍🏻08065599605
YOU ARE READING
ƳAN BOKON ƘARSHEN ZAMAANI
Actionlabari ne daya ƙunshi barkwanci,da kuma darasin zamantakewa ta yau da kullum