*_ALIYU ASADULLAH♡_*
'''The Lion of Monarchy'''
MrsUsman400
Chapter0️⃣5️⃣
بسم الله الر حمن الرحيم...
Last free Page...
Shiga daki nayi tare da Cigaba da abinda nake, har na fito na hada ruwan wanka Inna, ina shiga naga Innah ta taso daga inda take, a mamakance nake kallon ta, sakamakon yadda ta taso daga inda take tana boye kudin da aka bamu, ban san dalilin ta ba sai na zuba mata ido, na kaita na mata wanka nazo na gyara dakin, sai lokacin na Fahimci dalilin da yasa take boye kudin domin sau biyu na kama Inna larai tana binciken kayan mu, ban damu ba, na gama gyara ko ina na fara karatu kafin lokacin sallah yayi.Washi gari.
Da misalin karfe tara na safe sai ga Hajiya tazo. Muka shirya nayi musu sai da ma dawo, an kai ni babban makarantar koyar da girki na garin tankara, inda ake koyar da girke girke, me suna Shamaki catering services. Gurin yayi kyau mika min kome aka yi tare da nuna min ajin da zan zauna, tun safe da muka isa ban dawo ba sai karfe shida na yamma a gajiye na shigo gidan.Nayiwa innah wanka da alola, sannan nima nayi, na juye mata abincin da nazo dashi. Ina fahimtar abinda ake koyarwa gaskiya duk da yau na fara zuwa amma sosai na saka hankalina da nutsuwa ta akan abinda naje yi.
Ina jin Inna larai da Siyama da Aunty Binta matar Ya Haruna da suka zo, suna gulma ta amma ban kula ba, har ya zo suka bar gidan bai min magana ba, dama suna zargin wai yana sona ne, shi yasa suka shiga tsakanin mu. Lokacin da na gama abinda zanyi na kwanta kallon Inna nayi tana zubda kwalla. Tashi nayi tare da goge mata, sannan na gyara mata kwanciya. Na kwanta.
** Washi gari
Da asuba na tashi tare da yin abin karyawa na ajiyewa Inna nata, sannan na nufi hanyar waje da bokiti xan dibo ruwa, na hadu da wani Almajirin da nake yawan aiken shi karban bokitin yayi yana faɗin.
"Aunty da kanki, kawo na dibo miki." Haka na bashi tare da cewa.
"Nagode!"Na koma cikin gidan, ina zaune. Can sai gashi haka na amsa tare da shiga wanka, ina fitowa na shirya a nutse sannan na musu sallama bayan na taimakawa innah tayi boli, na koma da ita dakin ta kwanta. Karfe takwas yayi min ne a can, dan haka ina shiga wata mata me suna Madam Safiya yar garin Tirkulu ce, dan haka tana gani na tace min.
"Ke kiyi sauri ki shiga cikin kitchen kice su gyara akan lokaci Princess Natashah Abbas tare da Mahirah Musaddam Wazir, sai Nishat Badar Turaki, dan suma zasu zo koyan girki ne."Gyada mata kai nayi tare da shiga cikin nayi musu Bayani, take jikin su ya fara rawa, suka shiga aiki har dani, ina cikin yi Madam Nafisah Shamaki ta shigo.
"Ke Buhayyah lokacin Class yayi ki tafi, kuma ku ajiye aikin ku tafi class, sabida an fara karatu."
"Ok Mah" muka fada tare da nufar hanyar da ta biyo, mace ce kamilah sanye take da kaya irin na alfarma, duk da tana gaban mu, haka ba zai hana ka gano kyanta da cikar halittar ta ba, har zamu shiga tace min."Buhayyah!" A hankali na tsaya a gefen ta nace.
"Yes Mah!"
"Idan kin gama kizo."
"Ok Mah"
Na fada tare da nufar aji.***
Natashah Abbas
D'akinta kawai wata duniya ce me cin gashin kanshi, domin duk wani abu da zaka gani a cikin dakin dauke yake da siffar barbie, gashi tsarin dakin kamar na yara an shekara goma sha daya. A hankali ta ja bargonta me hoton Anna na cikin Froze ita da elsa. Sunyi kyau.
Yar karenta me suna Chu-chu ta lashe fuskarta, murmushi tayi cikin shagwaɓe tace.
"Chu-chu" ta kira sunan ta a yanga ce, murmushi tayi tana kallon karen da take lashe mata fuska. Tashi tayi bayan taji ana buga kofar ta."Amma wannan yarinya baki da mutunci yar iska. Kin manta abinda zamu je yi ne, Prince Asad zai zo da matar shi, shine zaki ajiye mu."
Wani irin yatsina face tayi kamar ta ga abin kyama tace.
"And so what" ta sauke kafarta a kasa, tare da kallon su lokacin da Nishat ta shigo, tana chat.
YOU ARE READING
ALIYU ASADULLAH!!!
General FictionThe best way to find yourself is to lose yourself in the service of others.