PART 1

64 6 9
                                    

BURIN DUNIYA

"Assalamu Alaikum!" 

wani kyakykyawan matashin me kimanin shekaru talatin da biyar, ne yayi sallamar "Ameen wa'alaikassalam" Daga can gefen falon kan dining table aka amsa mashi. Wurin ya nufa kai tsaye. Wata matashiyar mace ce itama a zaune taci gayu abinta da ganin ta kasan wannan gayun an yi shine domin tarar mai gidan. "Kiyi haƙuri matata na san na ɓata miki" Ya idasa maganar da haɗe hannuwanshi biyu alamar roƙo! Murmushi tayi sannan tace mashi. "Ai kullum haka ka ke yi baka son dawowa gidannan dawwuri" Amsa mata yayi da cewa. "Nasani ba sai kin ce komi ba wallahi aikine yayi min yawa shi ya sa bansamu dawowa da wuri ba. Ina Yaran suke?" "Uuuhhhmm "Sun gaji da jiranka sun ci abinci sun kwanta amma da cewa sukayi sai sunjiraka ka dawo sannan zasu kwanta."

      "Ayya! wallahi nima ba haka na so ba amma dole ta sa ni, tokefa kinci abincinne?" amsa mishi tayi da. "Ai kasan tun da mu ka yi aure bana iya cin abinci ni kaɗai indai ba tafiya ka yi ba." Murmushi yayi yace. "Tabbas nasani. To zuba in baki da kaina Uwar Ƴaƴana."
Da kanshi ya bata abinci harta ƙoshi itama tana bashi har suka gama suna firarsu irinta masoya. kwashe kayan su ka yi a tare suka kaisu kitching. wanke kayan sukayi tsab duk kuwa da dare yayi sai da suka gama komi sannan suka wuce ɗakin barcinsu.

       Washe gari ma da safe tare suka haɗa abin karinsu, gwanin ban sha'awa bayan sun gama mai gidan ya wuce ɗakinshi domin yayi shirin office itama ɗakin yaran ta shiga ta tashe su ta shiryasu tsab domin zuwa makaranta. tsab ta shirya yaranta sannan suka fito dining suka zauna su duka. Yaran ne su ka duƙa har ƙasa su ka gaida Abbansu amsawa yayi fuskarshi cike da murmushi yace.
"Kuyi haƙuri kun ji yarana jiya bandawo dawwuri ba"
Bayan sun gama cin abincin suka miƙe domin wucewa kuɗi ya ciro a aljihunshi ya miƙa mata yace.
"Amina ga kuɗin nan nima jiya mai gida ya bani su ki siya ankon da ki ka ce kinaso"
Jikinta har rawa yake wajen amsar kuɗin kasan cewarta mace me matuƙar son abun duniya, tanacewa.
"Saura kuɗin viju ɗin yara ka san dai ya ƙare ko?"
" huuummm to ba sai ki siya musu ba a cikin wannan kuɗin ba"
Idanu ta zaro waje tace. "Tab wallahi sai dai in ara maka idan ka samu ka biyani"
Amsa mata ya yi da. "To shi kenan ba matsala Allah ya bani ikon biya" juyawa ya yi kan yaran ya ce musu
"Haidar mutafi ko karkuyi latti. Feena kawo in riƙe miki lunch  box ɗinki" miƙo mishi tayi yarinyar tace "Yawwa Abbana nawa ni kaɗai kuma ka cewa Yaya Haidar ya dena hararata!" Ta idasa maganar tana turo ɗan bakinta gaba. Dariya yayi sannan ya juya wajen ɗayan yaron ɗan kimanin shekara bakwai shima ya cika ya yi tab murmushi ya kumayi saboda dramar yaran na bashi dariya. Lallashinsu yayi duka sannan ya ja hannun yaranshi suka fice daga gidan.

       Adai daita sahu ya tara suka shiga shi da yaranshi, ya ajiyesu a wata makaranta Nasara international school privet ce amma me sauƙin kuɗi. Kamfanin su ya wuce babban kamfani ne wanda ya amsa sunanshi kamfani kasancewar shi injiniya. Gaisawa ya yi da ma aikatan gurin cikin sakin fuska kamar yadda ya saba, juyawa yayi zai nufi office ɗinshi, sai ga ɗaya daga cikin ma aikatan gurin ya kira shi "Am dama Sir ne yace in kira ka" amsawa yayi da. "Ok yana office ɗinshi ne?" "A'a ya na waje" yabashi amsa "ok" kawai yace yajuya ya fita.

        Amina ce tafe a hanya tana tafiya, ji tayi an taka burkin mota a gabda ita da sauri ta juya domin ganin kowa ye. Buɗe motar akayi, wata matashiyar mace ce ta fito wadda ba zata wuce sa'ar Aminan ba. Idanu Amina ta zaro tace  "Lah Aisha kece?" rungume juna su ka yi wadda aka kira da Aisha ta amsa da. "Wallahi nice Amina ashe rai kanga rai?" amsawa Aminan tayi da cewa. "Wallahi dai kam shekara da shekaru" Aisha ta amsa da. "Sai alkhairi Amina yanzu yaranki nawa ne?" "yarana biyu ai tunda muka gama makaranta nayi aure" tabata amsa "Allah sarki kinga nima da a Abuja muke zaune da mai gidan amma yanzu wata guda kennan da dawowar mu garinnan da zama" Amina tace. "Allah sarki kin ga rashin sani kuma kin ga bamu taɓa haɗuwa ba" "Wallahi kam a wacce unguwa kike ne?" Aisha ta tambayi Amina "A g.r.a nake da yake kinsan mai gidana injiniya ne" "Lah kinga nima a nan nike yanzu kawai kishiga mota sai mu wuce kinga daganan sainaga gidanki aci gaba da yin zumunci" gaban Amina ne yayi mummunar faɗuwa! a cikin ranta tace 'Na shiga uku to ni wanne gida zannunawa Aisha amatsayinnawa, a cikin g.r.a ni da ba a can nike ba.

BURIN DUNIYAWhere stories live. Discover now