Begining of the journey

5 1 1
                                    

CLEAVERS WRITERS ASSOCIATION

Typing ✍️
          
              NOOR💥💥💫💫⭐️⭐️

Written by Ayshertou
   
Page 1️⃣ ( The beginning of the journey)

Bismillahir rahmanir rahim
(Da sunan Allah mai rahama mai jinkai)
Godiyah ta tabbata ga Ubangijin talikai da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin Ina rokon Allah ya bani ikon gamashi lapia Ameen I hope you guys will enjoy it Thanks

I dedicated the whole story to you
Maryam Abdoul 🌹 words are not enough to describe how much I love you

Kaduna international airport........
    Wata matashiyar budurwa ce take sakkowa daga jirgi hannunta rike da hand bag sanye take cikin shadda light brown ta yane kanta da mini veil sakkowa take daga stairs din jirgin kamar wadda Kwai ya fashema wa a ciki daga nesa ta hangosu take fuskarta ta washe zuwa murmushin da ke karama fuskar ta kyau tafiya take izuwa wurinsu cikin hanzari wadda kallo daya za kai mata ka gane ta kagu ta isa garesu  ,tun daga nesa ta fara bude hannun tanai ma Wata matashiyar budurwa oyoyo,budurwar dake tsaye tana kallonta tun lokacin da ta taho itama bude hannuwanta tayi tareda yimata oyoyo fada wa tai jikinta ta rungume ta tana murmushi tare da cewa "I miss you Imaan "  " I miss you more autar Ammie " budurwar tace murmushi shimfide a fuskarta juyowa tai zuwa wurin wani matashin saurayin dake jingine jikin mota hannun shi rungume yana kallonta matsowa tai gabdashi tana dariya ciki ciki ganin ya daure fuska tace   "yaya Amaan Ina yini " murtuke fuska yai alamar bai ganetaba sanan yace "pls who are you?" Dariya tai sanan tace "haba yaya Amaan dinmu mi nai za ae fushi dani saurayin da ta kira yaya Amaan ne ya juyo yana kallonta sanan ya tabe baki yace"sai ynxu kika ganni kenan da duk bakisan da ni ba kou?"
Budurwar da naji ankira da imaan ce ta matso tare da kamo hannun ta "haba yaya Amaan kayi hakuri kasan noor in ta ganni mantawa take da kowa " imaan ta fada tana murmushi tabe baki yayi yace "parrot kinxo shigarmata kou my friend shi ga mota mu wuce time na tafiya "tare suka nufo wurin motar dake gefensu shiga sukai sanan ya tada motar suka fita daga Airport din gabadaya .......

A mota labarinsu suke tayi wanda jefi jefi yayan nasu yake magana da ka gansu kaga wanda sukai missing din juna hanyar millennium city dake hayin dan bushiya suka nufa ..
*************************************
Tun daga nesa na hango wani tamfatsetsan gida wanda da alama sabone baa dade da tare wa ba a kofar gidan sukai parking horn sukai mai gadi ya bude masu gate suka shiga cikin gidan tun kafin ai parking imaan take kokarin bude motar juyowa yaya Amman yai ya dalla mata harara baki ta turo gaba sanin halin yayan nasu ya tsani haka saida ya gyara tsayuwar motar a parking lot sanna imaan ta futo motar har tai gaba sai kuma ta dawo baya ta bude ma wannan budurwar mota tare da jan ta sukai cikin gida ,A bakin kofa suka kusan cin karo da wata budurwa wadda ta dan finsu girma daga gani yayar su ce hugging din juna sukai cikin farin ciki "welcome noor" budurwar tace cikin faraa wadda naji an kira da noor ce ta ce "thank you yaya hafsat "...Ahh muryar wanike ji kamar noor " inji wata mata dake fitowa sanye cikin wanni tsadadden lace taci ado kallo daya zakai mata kagane yar gayuce da gudu wadda ake kira da noor taje wurin ta tare da hugging dinta tace"mommy nice mun iso yanzu ni ke shirin nemanki" dan hararanta matar tai sannan tace "yaushe zaki nemeni bayan kin ga ' yan uwanki " dariya noor tai parlorn suka shiga suka zazzauna aka fara hirar yaushe gamo kafin daga baya mommy tace ma Imaaan ta kai ta Daki tai wanka sannan su fito su ci abinci "Toh" iman tace tare suka shiga dakin su imaan din Imaan na janye da trolleyn noor wadda mai gadi ya shigo da ita ynzu wanka noor tai sannan daga baya suka fito parlour tare kamar twins dinning din dake gefen parlor suka nufa mommy ce zaune inata da yaya hafsat suna cin abinci bayan sun gama suka shiga Hirar yaushe gamo

Kubiyoni don ji yaya zata kaya ?wacece noor ? Gidansu wa tazo holiday ? Duka cikin next page 💃💃
Pls don't forget to vote 🙏

NOOR💥💥✨✨(The light)Where stories live. Discover now