Brother's love

0 0 0
                                    

CLEAVERS WRITERS ASSOCIATION

Typing ✍️
          
              NOOR💥💥💫💫⭐️⭐️

Written by Ayshertou

Page 6️⃣ (brother's love)

Horn din da mai gadi yaji yasa ya taso ya bude masu gate parking space suka nufa dake Chan gefen gidan Ana isa kuwa noor ta bude Motar ta futo zuwa cikin gida ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta kan bed dinta don ta gaji sosai ..
Tana Parlour ta tadda ba kowa sai karar tv dake ta aiki ita kadai direct upstairs ta nufa ta shiga dakinta handbag din ta da handout ta aje kan gado tare da cewa "washh " alamar ta gaji sosai fita tai daga dakin ta leka dakin ammie ,kofar dakin ta tura ta tadda ammie kan sallaya tana sallah dakin ta ta koma a shiga cire kaya ta fada toilet tayi wanka da alwall don tai sallah ..
Ammie ce ta turo kofar dakin ta tadda noor kwance bisa bed dinta tana latsa laptop "baziki sakko dining kici abinciba noor"," ammie zan sakko fa beside ban dade dacin abinchiba a school cafteria "tabe baki ammie tai tace "toh ya test din ?"
"Alhmdllh tayi sauki " "Allah ya bada saa" inji ammie
"Ameen ammiena " fita Ammie tai daga dakin ta sakko down stairs don ta Dora dinner saboda tuwo takeson ci yau kuma ita take son in yin Abunta da kanta balle dama Chan bata bari maids na yi mata aikin abinchi inba she is busy ba saide su taya ta ,

**************************************

Around 5:00pm noor ta sakko parlour direct kitchen ta nufa ta tadda ammie na yanka alayyahu sai Baba jummai tana yanka kifi Suna hira "Ammie Ina abinchina " inji noor tana yamutsa fuska alamar yunwa takeji " gayanan bisa kaina zoki diba "inji ammie da ko dagowa Batai ba ta kalle ta ,direct dining ta nufa tana zumbura baki sanin halin Ammien na rashin son sakarci ,food warmers din dake kan dinning ta bude taga lafiyayar jellof rice da taji vegetables tsaye tai kan dinning din kamar mai nazarin wani Abu sannan daga baya ta dauki plate tai serving kanta ta fara ci tana gamawa ta koma kitchen wurinsu ammie don ta tayasu aikin sunayi suna hira..
Kiran sallar magrib ne yasa suka koma upstairs kowa ya nufi hanyar domin yayi sallah,after magrib noor ta shiga dakin ammie ta isketa tana waya hayewa tai kan gadon tare da chanza channel din tv tana kallo ,juyowa ammie tai tana kallon noor tace "ga noor din nan ma kan gado abaka ita koh?" Baki noor ta washe kasancewar ta gane wa ammien ke waya dashi miko mata wayar ammie tayi karba tai tare da yin sallama "waalaiku mussalam mama nah ya kike?" "Lpia klau Abbie ya aiki" "Alhmdllh ya lectures ? Kinade karatu koh?" " eh Abbie inayi ,don Allah yaushe zaka dawo Ina missing dinka fa"noor tace cikin shagwaba kamar tana gabanshi dariya Abbie yayi yace "soon mamana but karki damu wannan karon tare zamu dawo da ammienki in ta zo ,zaro Ido noor tai kamar zatai kuka tace " Abbie wai dama ammie ma Egypt din zata je  ban  saniba  ,shine baa gayaman ba"ta fadi  tana zumburo baki "haba auta ko kin manta tana zuwa medical check up na idonta ,kiyi hakuri ai bazata dade ba kinji,beside ma tare zamu dawo kinga sai kiga ammienki da Abbienki tare koh?" Ya fada ya na murmushi ,lallashinta  Abbie ya shiga yi har ta fara dariya sannan sukai bankwana ta Mika ma ammie dake gefenta tun dazu wayar ta fita daga dakin ita ala dole tana fushi da ammie ..
Dakinta ta shiga ta kunna laptop dinta ta cigaba da kallon film din da tai downloading ko takan tv dake makale a dakin bata biba saboda she prepares to watch a laptop ,karar horn din da taji daga Chan bakin gate yasa ta leka ta jikin window taga ko wanene da yake Ana hango gate din daga upstairs ,motar yaya farouq ta gani ta kunno kai cikin gidan laptop dinta ta kashe ita ma ta sakko kasa saboda daman tun dazu shi take jira ta kai mashi karar ammie 😂,
Tana sakkowa yaya farooq na ida Shigowa parlorn Ido suka hada yayi murmushi yace "my angel kuma autar ammie mi akai maki naga kina wani tsare gida"matsowa tai kusa dashi ta gaida shi amsawa yayi tare da cewa Ina ammienki? " Tana daki" tace
Haurawa yayi upstairs don ya gaida ammie ta bishi a baya kamar jela tare suka shiga dakin ammie suka taddata kan sallaya tana karanta Al-Quran dagowa tai ta kallesu sannan ta ajeshi a gefe "Ammie Ina yini " "lpia klau Farouk an dawo lpia " " lpia Lau "
"Toh Masha Allah " inji ammie juyowa yayi Yaga noor na nan tsaye taki ta zauna sai zumbura baki take smiling yayi tareda cema ammie "wai ammie yau mi akaima auta ne tun da na dawo naga tana ta fushi" "ohon mata ka tambayeta kaji Nima ban saniba " murmushi yaya Farouk yayi tareda yima ammie sallama ya fita daga dakin ,binshi noor tai abaya juyowa yayi yace "what's wrong ne noor ,mi akai maki" cikin concern manner da lallashi,kwal kwal tai da Ido kamar zatai kuka sanin halinta yanzu zata iya breaking into tears cos she can cry for Africa😌,yasa yace mata "yanxu bari in shiga daki in dan watsa ruwa ki jirani  sai inji waya taba autar Abbie "kai kawai ta daga batare da tace komai ba ta zauna a parlour tareda concentrating akan tv ,daki shima ya nufa don yai wanka ya rage gajiya ,tana zaune tana kallo har ammie ta gama abinda Takeyi ta sakko kasa don suyi dinner .
Suna zaune sai ga yaya farooq ya fito daki shima cikin shirin bacci dinning din ya nufa ya zauna tashi noor tai itama daga kallon ta koma kan dinning din serving dinsu tai abinchin sannan ita ta zuba nata,bayan sun gama cin abinchin ne yaya Farouk ya tambayeta mi akai mata Mar mar tayi kamar zatai kuka sannan ta fara zayyana mashi "yaya farouq wai Ashe ammie Abbie zatabi egypt cikin week din nan shine bata gayaman ba" dariya yaso yayi jin abin da yasa taketa kumbure kumbure kenan tun dazu shi harga Allah yasa wani babban Abu ne,gimtse dariyar yayi don kar ta kara yin fushi sannan yace"noor rigima tou bakisan dama zata je check up bane ba ,kefa da kika tafi kd kika barta bata ce komai ba ,do you mean bakisan da tafiyan ba sai yau? "ya fada don yasan Sarai tasan ammie na zuwa check up na idonta akai akai yanxu ma don noor na school ne Amman da in su ka ta tafi sae sun dade suke dawowa Nigeria "Ni na manta" noor ta fada cikin Shagwaba ,dariya yayi yace "toh ai ynxu kin tuna kou beside bake kika ce kinason karatu a Nigeria ba ,ba yadda Abbie bayi dake ba ki zauna Egypt a samo maki wata universityn tare dasu kika ki ke me 'yan uwa kika ce ai school dinsu Afrah zaki ko ba haka ba ,and you know saboda ke Nema ammie take zaune a Nigeria da ynxu tana Chan tare da mijinta"ya ida maganar yana dariya ,harara ammie dake zaune gefensu tun dazu tana jinsu ta jefame sosa kai ya shigayi sanan yace "toh ynxu ba sae ki tafi gidan su Afrah ba daman ai haka kike so koh? Shiyasa ki ka dage school daya zakuyi " kai ta shiga girgizawa tana kakalo Kwalla tace "Aa fa yaya su fa suka dameni in ce skul dinsu nikeso don mu rinka haduwa kuma ni nafison in rinka ganin hajja banason inyi missing dinta shiyasa nace zan zauna naija kuma fa nasan in ba anan Nike karatu ba zan dade bamu haduba in ba sun biya Egypt din ba shima sai bayan shekara in sun dawo daga aikin hajji ," toh ba sae kiyi hakuri ki zauna wurin hajjar kiba "ya fada yana dariya kukan Shagwaba noor ta fara tana buga kafa  ala dole sai ammie ta Zauna har sae anyi masu Hutu sannan su tafi tare ,banza ammie tai da ita kamar bata San tanayiba yaya Farouk ne ya shiga lallashinta har sai da tai shiru tareda yi mata promise kala kala duk don ta hakura,
Ammie ce ta tashi alamar zata je ta kwanta  don ita kam  ta gaji da ganin wannan ta barar gwanda taje ta huta sallama tai masu tai hayewar ta sama abunta nan tabar yaya Farouk da aikin lallashi
Washe baki noor tai jin yaya Farouk ya ambachi ze kaita Tasha ice cream gobe "Amman de kai kana nan kou?" " Ina zani angel Ina aiki inanan gida ai ko da da muke tafiya tare don Ina masters dinane shiyasa muke tafiya mu barki Amman ynxu na gama karki damu zan rinka lekoki beside I know those talkatives will never leave you to feel lonely "ya fada referring to su Afrah dariya noor tai tace "sune talkatives yaya Farouk " eh mana ai duk daya kuke" murmushi tai sannan ta kauda zanchen tare da cewa "yowwa sweet bro pls in zaka xo ka rinka tahoman da tsara ban ice cream dasu chocolate ,Amman fa in zaka bani kar ka ban gaban wannan hajjar don bata bari insha wallahi  kwacewa takeyi ahr su afrah su tayiman dariya "ta fada tana zumburo baki dariyah yayi yace wanann tsakaninkune wa ze shiga yaji kunya ,karki damu zan rinka kawo maki kinji ,0ya tashi kije ki kwanta it's getting late "kai ga gyada alamar ta gamsu da abinda yace sanannan tai mai sallama ta nufi dakinta don ta kwanta...

Ayshertou 🥰

NOOR💥💥✨✨(The light)Where stories live. Discover now