Identity

3 1 0
                                    

CLEAVERS WRITERS ASSOCIATION

Typing ✍️
          
              NOOR💥💥💫💫⭐️⭐️

Written by Ayshertou

Page 2️⃣ (Who is noor)

Alhaji Abdullahi zango wani hamshakin dan kasuwa ne dake garin kano inda mutane dayawa an sanshi saboda shahara da yayi a fannin kasuwanci Allah ya Albarkaci Alhaji Abdullahi da dukiya mai Albarka matarshi daya sunanta maryam inda yaranta ke kiranta da hajja
Allah ya azurta Alhaji Abdullahi zango da yaya ukku kacal bayan kusan shekaru 5 da aurensu da matarshi Hajja biyu maza daya mace babban cikinsu sunanshi Alhaji Umar farouk, wanda shima a yanzu ya zama wani sannanne a Nigeria,Alhaji Umar Farouk Abdullahi zango minister ne na oil and petroleum suna zaune da iyalinshi a garin Abuja mai bimashi shine Alhaji Muhammad wanda shine mahaifin noor shi kuma ambassador ne na nigeria a Egypt ,duk cikin 'yayan Alhaji Abdullahi zango Alhaji Muhammad kadaine ya biyoshi ta fannin kasuwance kasancewar shi yanada shaawar gadon mahaifinsu tun yana karami sun zauna da iyalenshi a Egypt shekarun baya kafin su dawo Nigeria ynxu haka suna Zaune a unguwar Gwarinpa Abuja,karamar cikinsu kuma diya daya tal da Allah ya Azurta Alhaji Abdullahi da itace hajiya zainab ita kuma lawyer ce itada family dinta suna zaune a garin kaduna...

Matar Alhaji umar farouq daya hajiya Aishatu suna ce mata mamee 'ya'yansu ukku biyu mata daya namiji ,babban dan danshi sunanshi Muhammad Ana kiranshi da Aryan saboda sunan kaninshi da akasa wato babansu noor,Aryan yayi karatu a harvard Cambridge university US yanxu haka bai dade da dawowa Nigeria ba bayan ya kammala MBBS (bachelor of medicine and surgery),sai twins mata kannanshi Ana kiransu da Afrah da Afreen wa enda suke a nile university Abuja , su ukku kadai Allah ya ba Alhaji umar farouq,yana matukar son Aryan kasancewarshi da namiji a gareshi ,
A Gidan Alhaji Muhammad kuwa Allah ya Azurtasu da yara biyar ,ukku maza biyu mata babban yayansu sunanshi Ahmad wanda yanzu ya zama babban soja da kasa ke Alfahari dashi,sae mace ke bi mashi sunanta Aunty laila tayi aure harda yaranta biyu tana zaune a garin kano ,sai yaya farooq dake aiki a CBN Abuja bayan yaya farouq akwai Abdulmajeed wanda yake karatu ABU Zaria yana karantar pharmacy sae autar ammie wato maryam Ana ce mata noor .
A gidan Aunty Zainab kuma suma Allah ya azirtasu da yara 3 yaya Fahad (Amaan),hafsat sae autarsu Saar noor sunanta halimatu Ana kiranta imaan....

Allah yayima Alhaji Abdullahi zango rasuwa shekaru biyu da suka wuce sanadiyar ciwon zuciya da yai fama dashi inda iyalanshi harma da mutane da dama sukai kukan wannan babban rashin da sukai,mutuwarshi ta girgiza mutane da dama ciki harda matar da iyalinshi, bayan shekara daya da rasuwar Alhaji Abdullahi zango babban danshi wato Alhaji umar ya ga ya kamata su dauki mahaifiyarsu su dawo da ita kusa dasu saboda kula ynxu haka hajja tana Abuja Gidan Alhaji umar Farouk,ya gina mata shashenta daban a cikin gidanshi ya samu masu kula da ita saboda ita ta bukaci hakan a ganinta sai yafi karta takura masu,hajja na matukar son noor kuma sun shaku sosai saboda tana yawan zuwa mata hutu lokacin marigayi na da rai....

Kasancewar iyayensu na haihu wa kusan a tare yasa zakaga 'ya'yan kusan sa 'annin juna noor,Afrah,afreen da imaaan kusan sa'annine amman Afreen da Afrah ne manya cikinsu sunba noor da imaan kusan Shekara daya ita kuma noor ta girmi imaan da 6 month shiyasa tasu tazo daya,sun shaku sosai kasancewar iyayensu nasu basu
sakaci da zumunchi inda hakan yasa ynxu noor taje hutu gidansu imaaan bayan sunyi hutun semester acewarta sun dade basu ga juna ba sannan su ba a Abuja suke ba kamarsu Afrah da suke ganin juna kusan ko da yaushe.....

Kubiyoni don jin cigaban labari......💃💃

Dedicated to maryam abdoul 🌹

NOOR💥💥✨✨(The light)Where stories live. Discover now