1

30 6 0
                                    

*RAYUWA KENAN.🤦🏻‍♀️*

*JIGO*

_Labari akan zinace zinace dake wa kana tsakanin maza da matan Aure..._

*LITTAFIN GASAR MATASAN MARUBUTA GROUP 8(2021).*

_REAL ESHAA_✍🏻

*1*

_______________________________📖Dariya suke 'kyal'kyatawa cikin tsananin farin ciki kallo 'daya zaka musu kasance wa suna cikin jin daɗi,Tsagaita dariyar tayi tare da kallon mutumin dake gefen ta cikin yau'ki tace "Gaskiya Alhaji na yakamata mu canza wajen ha'du wa kasan yanzu mutane ake kiwo ba dabbobi  ba" tayi maganar tana 'ko'karin mi'kewa tare da 'daukar hijabin ta daya sau'ka har 'kasa tasa,Lashe baki mutumin da takira da Alhaji yayi kamar wani tsohon maye yace"baki da matsala baby na yanzu ina kike so mu dinga ha'du wa??,Shiru tayi na wasu da 'ki'ku kafin tace "Hotel dan can ne zaifi sirri akan gidan ka"Peck ya bata akuncin ta yace "good Idea" hannu yasa a loka yaciro ku'di kimanin dubu goma ya dan'ka mata kana ya 'dauki babban anti jumbo yabata,Rngume sa tayi sannan ta 'dauki ledan Bayan ta yabi,wata 'kofa ya bu'de mata cikin sauri ta fice tana 'daga masa hannu, Kasancewar lokacin da tafito daga gidan an shiga sallar Isha'i, kai tsaye ta shiga gidan ta batare da kowa ya ganta ba.

Bacci tasamu yaran nayi atsakar gida da sauri ta cire hijabin ta,sannan ta bu'de ledan data shigo dashi,sin'kin biredi guda biyu ne aciki se kuma gwangwanin madara da na Bonvita da sauran kayan shayi,cike da farin ciki ta tashi yaran sannan ta ha'da musu shayi,Bayan sun gama sha suka kalle ta tare da fadin "Mama ina kike zuwa kullum da dare kike samo mana abinci??.

Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace "kar kudamu dasanin inda nake samo muku nide fatana ku dinga 'koshi ko yaushe.Tana gama maganan tashiga toilet tayi wanka tana fitowa tayi sallolin dake kanta sannan ta ha'da Tea tasha.
"Kwance take ma'kale da waya a kunne ta taji shigowar Baban Hassana bedroom 'din,A hankali tace "zamuyi waya anjima Alhaji na Ok! bye" tasake fa'da tare da katse wayar.

Zama yayi yana kallon ta yace "Har sunyi bacci ne?,Kai ta gya'da batare da tace komai ba, "Amina babu abinci ne? Wallahi yunwa nakeji rabo na da abinci tun safe" yayi maganan kansa tsaye...

Cike da takaici tami'ke zaune tana kallon sa tace "Fisabilillah! Adamu yanzu ba kaji kunyar tambaya ta abinci ba?tun safe rabon ka da gidan nan baka bar mana komai ba amma yanzu kazo kana tambaya ta abinci"
'Daure fuska yayi yace "toh bani dashi ko kuma sata kikeso naje nayi?."A fusace tace "wallahi hakki na dana yaran nan baze ta'ba barin ka ba irin kune kuke jefa rayuwar matan ku a halaka. Tsaki yayi ya juya yana cewa "sai dai dama Idan tun baya 'bacaccu ne" yana gama fa'din haka ya fice yana 'kananun surutai.....,

*******

Cikin shigar alfarma tashigo falon nasa tana baza 'kamshi zaune ta same shi da waya yana latsawa, Kamar wanda aka aikowa da sa'kon mutuwa haka fuskar sa ta koma babu alamar rahma aciki ganin ta da yayi Cikin sanyin murya tace "Barka da warhaka Alhaji yanaga kamar bakaji da'din zuwa na ba?" "Kinga Fatima bana bu'katar 'kananun magana idan kinsan ba magana me muhimmanci zaki fa'da min ba kina iya tafiya dan inada abin yi" Cikin rawan murya irin na wanda ke shirin zubar da hawaye tace "Alhaji kaji tsoron Allah ka dinga sau'ke hakkin mu dake kan....," Bai bari ta 'karasa ba yanuna mata hanya tare da fa'din "Fice min a'daki banza ace sam mace batada hakuri"Da gudu Fatima tafita tashiga 'dakin ta sai da tayi kuka me isarta,ganin dare yayi nisa ne yasa tamiƙe ta shiga toilet tayi alwala tare da kaiwa Ubangiji kukan ta kan ya kawo mata dau'ki acikin rayuwar ta....

*******

Da yammaci misalin 'karfe 5 bayan tagama dafa abinci ta juye akula ta kalli 'ya'yan ta tace "Ga abinci nan kar Ku yadda kufita ko ina sannan ku kula da kanku duk wanda yazo ne mana kuce naje chemists"Toh" sukace sannan tafice,Wayar ta dake cikin purse ta Ciro tare da kiran wani number ana 'dagawa tace "Alhajina gani na fito katuro min address ɗin" "Ok!" yace sannan ta katse Wayar,kafin ta isa bakin titin massage yashigo,tana gani ta tari 'dan adedeta ta fa'da masa inda zai kaita,Adedeta na ajiye ta  ta biya sa,Wani Babban Hotel ne mai ƙyau facemask taciro  tasa sannan ta kutsa kai ciki kasancewar har number 'dakin ya tura mata, Knocking tayi cikin sauri ya 'karaso ya bu'de mata tana shige ta cire hijabin tare da rungume sa.Cikin jin da'di ya 'dagata yana juyi da ita Cikin wata narkakkiyar murya tace "kaga nan babu me kallon mu se muci gashin kan mu"Kai ya gya'da mata, daga nan suka shiga aikata masha'ar su....

Yau ma kamar kullum bayan tagama duk abinda take ta kalli 'ya'yan ta da suka zuba mata Idanu, 'Dauke kanta tayi tare da fa'din "Ku kula da kanku sannan kar kufita" Da sauri Hassana tace "Mama dan Allah yau ki zauna damu kar kifita tsoro muke ji" ta'karashe kamar zatayi kuka...

Murmushin da be wuce saman la'b'banta ba tayi tace"Idan ban fita ba a ina zan samo mana abinci?, Kuka Hassana ta fashe dashi tace "Mama mude bama son abincin ki zauna damu,Idan Abba yadawo zance ya dinga kawo mana, suma sauran Kuka suka Sanya tare da fa'din "Mama ki zauna" Zama tayi tashiga rarrashin su anma fir sun'ki yin shiru. Ganin suna son gigita mata tunani ne yasata buga musu tsawa ka tafice daga gidan, Direct hotel 'din da suka saba ha'du wa tashiga,Nan suka fara aikata masha'arsu kamar ko yaushe...

******

Fatima na zaune Iliya yayi sallama yashiga,tana ganin sa tayi murmushin tare da fa'din barka da zuwa mai gida na,yana murmushi yace "yawwa,bayan sun gama gaisawa tami'ke tashiga kitchen abinci da drinks ta kowa masa,Bayan ya gama cine yace"Ina Alhaji ne?Tun safe daya fita be dawo ba,ayyah dama nazo 'daukar sa'ko ne a 'dakin sa"Mikewa tayi tace "Bari na duba maka tana gama fa'din haka tafice,Bayan ta bin ciko tana 'dagawa taga Iliya tsaye akanta yana Binta da wani shu'umin kallo....

*MASOYA 'YAN UWA NA DA ABOKAN ARZI'KI DAN ALLAH DUK WANDA YA KARANTA YA TAYANI SHEARING DOMIN NUNA MIN 'KAUNAR KU,SANNAN KUYI VOTING 'DINA....*

RAYUWA KENANWhere stories live. Discover now