1

10 0 0
                                    

RAYUWA KENAN!

                         JIGON LABARI
Labari ne akan zinace-zinace dake faruwa tsakanin maza da matan Aure!

GASA.G 8 (2021)

REAL ESHAA_✍🏻

1

Dariya suke 'kyal'kyatawa cikin tsananin farin ciki, kallo d'aya za ka yi masu ka san cewa suna cikin jin d'adin duniya.

Tsagaita dariyar tayi tare da kallon mutumin dake gefen ta, sannan tace dashi a cikin narkakkiyar murya, "Alhaji ya kamata mu canza wajen had'uwa, kasan yanzu duniya ta zama abin tsoro!" Ta 'karasa maganar tana mi'kewa tare da sanya doguwar hijabin ta.

"Ba damuwa Baby na, amma ina kike so mu cigaba da had'uwa?" ya tambaya.

Murmushi tayi sannan tace, "Kawo kunnenka ka ji, dan abin sirri ne".
Matsowa yayi kusa da ita, sannan ta rad'a masa a kunne. Murmushi yayi tare da  sumbatar ta a saman la'b'ba, sannan yace, "lallai kin kawo shawara me kyau!".

Hannu yasa a cikin lokar sa ta kuɗi, sannan ya ciro dubu goma ya bata, sannan ya ha'da mata da babbar leda cike da kaya. Rungume shi tayi, sannan tace, "Ina son ka Alhaji na!" sannan ta ƙara sakar masa wata shu'umar suumba a la'b'ba, sannan kuma  ta d'auki ledan ta nufi 'kofa.

Bayan ta ya biyo ya bud'e mata 'kofar cikin sauri ta fice tana d'aga masa hannu, kasancewar lokacin da ta fita daga gidan ana sallan isha'i ne yasa ta shige gida ba tare da wani ya lura da ita ba.
***
Da sauri ta bud'e 'kofar gidan dake rufe tare da ta kutsa Kai, sannan ta 'karasa shiga tana kallon Yaran dake kwance akan Tabarma suna bacci, kallo d'aya za ka yiwa yaran ka gane baccin wahala ne su ke yi.

Hawaye ne suka zubo mata da ganin halin da 'ya'yanta suke ciki, hannu ta sa ta share hawayen, sannan ta bu'de ledar da ta shigo da ita ta. Biredi ne a ciki leda biyu, sai gwan-gwanin madara, Milo, Lipton da, Sugar.
Ajiyar zuciya ta sau'ke bayan ta gama dubawa, mi'kewa tayi ta shiga d'aki ta ɗauko flaks dake d'auke da ruwan zafi ta fito, cikin mintuna kad'an ta had'a tea kofi uku, sannan ta tashi yaran ta ba su. Hannu baka hannu 'kwarya suka gama dashi, sannan ɗaya daga cikin yaran ta dube ta tare da cewa, "Mama ina kike zuwa samo mana abinci da daddare?"

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace "Hassana kar ku damu da sanin wurin da  nake samo maku abinci, ni dai burina shine kada ku kwana da yunwa!" Tana gama fad'in haka ta mi'ke ta shiga toilet tayi wanka ta fito, sannnan ta fara biyan sallolin dake kanta, bayan ta gama sai ta kwanta ma'kale da waya a kunnen ta. Jin Sallamar baban Hassana a d'akin yasa ahankali tace, "za muyi waya gobe Alhaji na!"
"Ok bye!" Ta sake fad'a sannan ta katse wayar.

Zama yayi yana kallon ta yace "Har yaran sun yi bacci?" Kai ta d'aga ba tare da tace Komai ba. "Wallahi yunwa na keji rabona da abinci tun safe!" Ya faɗa kansa tsaye.
Mi'kewa zaune tayi cike da takaici tace, "Fisabilillahi Adamu baka ji kunyar tambaya ta abinci ba? Rabon ka da gidan nan tun safe bayan ka san baka bar mana komai ba fa, amma saboda rashin tausayi kazo kana tambaya ta abinci!".
'Daure fuska yayi yace, "toh bani dashi! Ko kuma sata ki keso na yi?" A fusace tace, "Wallahi hakki na dana 'ya'yan ka ba zai bari ka ci gaba a rayuwar ka ba, Irin ku ne ke jefa rayuwar matan ku da 'ya'yan ku cikin halaka!"
Tsaki yayi sannan yace, "sai kuma kiyi jarababbiya, halaka da kike faɗa  dama sai dai idan tun can matar lalatatta ce!" yana gama fa'din haka ya fice yana kunfar baki. Sosai Amina tayi kuka kamar ranta zai fita, bacci 'barawo shiya sace ta ba tare data shirya ba.
*****
Cikin shigar alfarma ta shigo falon tana baza 'kamshi, kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa tare da 'daure fuskar sa kamar wanda aka aikawo da sa'kon mutuwa, zama ta yi a kusa dashi sannan tace dashi a cikin sanyin murya, "Dear sai na ga kamar ba kayi farin cikin shigowa ta ba ko?"
Tsawa ya daka mata mai ƙarfi, sannan yace, "kinga Fatima dan Allah ki 'kyaleni, ke baki da aiki sai 'kananun maganganu, idan kinsan baki da abin fad'a mai mahimmanci kina iya tafiya!"
Cikin rawan murya tace, "Alhaji kaji tsoron Allah, ka san cewa Ubangiji zai tambaye ka hakkin mu da ya baka.......!"
A  fusace yace, "Fice min da ga 'daki, banza marar ha'kuri! Ko so kike ki mayar dani inji ?" "A ce sam baki da ha'kuri, Allah ya ba matan da mazajen su ke tafiya wata da watanni basu gansu ba ha'kuri!"
Da gudu Fatima ta fice daga d'akin tana wani irin kuka me ban tausayi, Shin ya za tayi da wannan jarrabawan da Allah ya d'aura mata, wanda take tunanin shi zai biya mata bu'katar ta, gashi ya banzatar da ita tare da fatali da damuwar ta.
***
Wurgi tayi da turmin atamfar dake hannun ta, cike da bala'i ta dube shi tace, "Wallahi Aliyu nafi 'karfin 'daura atamfar dubu takwas, dan haka ka d'auki tsiyar ka bana bu'kata! Cikin sanyin murya ya kalleta yace, "kiyi ha'kuri Nana! Kin san cewa albashina ba mai yawa bane, san...." Da sauri ta d'aga masa hannu tace, "Nifa ban nemi jan magana ba! Gaskiya ce na fa'da maka, ko kuma so ka ke inje cikin 'Kawaye na su ganni da wannan matsiyacin zanen?" Ta 'karashe tana me jifar sa da wani wula'kantaccen kallo, ba tare da yace komai ba ya d'auki Atamfar sa ya fice.
Dogon tsaki taja tace, "Insha Allah na kusa tsinke wannan gurgun Auren da kai, dan ba zan iya zama da matsiyaci ba kamar ka ba, matan da basu kaini kyau da diri ba ma suna auren masu kud'i bare ni da nake a waye.....!
******
Da yammaci misalin 'karfe shida bayan Amina ta gama aiyukan ta, ta juye jolof 'din shinkafar da ta dafa a kula. Sannan ta mayar da kallon ta a kan Hassana da Usaini da suka zuba mata idanu, murmushi ta sakar musu cike da 'kaunar su tace, "ga abinci a Kula kar ku fita ko ina, sannan ku kula da 'kanin ku, idan wani yazo nema na ku ce naje siyan magani" Kai suka 'daga tare da fa'din "Mama kar ki dad'e tsoro muke ji!" Murmushi tayi musu, sannan tace, "Insha Allah ku kula da kanku"
Tana gama fad'in haka ta fice cikin 'katon hijabin ta har 'kasa kamar ko yaushe...
Wayar ta dake cikin 'karamar jakar hannu ta ciro tare da danna kira, ana 'dagawa tace "Alhaji na fito ka turo min da address d'in".
"Ok! gashi nan zuwa".
Kafin ta 'karasa bakin titi massage din yashigo tana bu'dewa taga address din, da sauri ta tari 'dan-adedeta tare da fad'a masa wurin da zai kai ta.
Ba ɓata lokaci ya kai ta wajen, tana sauka daga adedetan ta d'aga kai tana kallon 'katon Otal d'in, takunkumin fuska (Face maks) ta ciro a jakar ta rufe fuskar ta, kai tsaye d'aki ta nufa kasancewar har da number d'akin yatura mata.
Da sauri ya bud'e mata 'kofar bayan ta 'kwan'kwasa, Ba zato ta ji ya 'da gata sama yana juyi da ita, Murmushi fara yi tana cewa, "Nayi kewar ka Alhaji na!" gira ya 'daga tare da kashe mata ido, sannan yace,"ko?" Kafin tace wani abu ya rungume ta, daga nan suka fara aikata masha'arsu...!
*******
*_Dan Allah Masoya kuyi shearing  sannan kuyi voting lokacin da labarin ya kammala..._*

RAYUWA KENANWhere stories live. Discover now