2

20 0 0
                                    

*RAYUWA KENAN!*

                   _JIGON LABARI_
_Labari akan zinace-zinace dake faruwa tsakanin maza da matan Aure!_

_GASA.G 8(2021)_

*2*

Misalin ƙarfe bakwai da rabi na bayan Mangariba, Fatima na zaune ta zabga tagumi tana tunanin halin da take ciki, sai taji an janye mata hannu. Ganin wanda ke tsaye a ne yasa ta sau'ke ajiyar zuciya,  murmushi yayi tare da cewa, "tunanin me kike yi ne haka matar?"
"Tunanin Rayuwa!" Ta fad'a tana mi'kewa tsaye.
Abinci ta kawo masa, ya kar'ba yana godiya, bayan ya gama ci yace "akwai wani file da na zo kar'ba wajen Yaya, naga bayanan ko zaki d'aukomin?"
Tace "ok!" Sannan ta fice, bayan ta 'dauko file d'in tana juyowa taga Iliya tsaye a bayan ta, kafin tayi wani yun'kuri sai taji ya rungume ta, a razane ta dube shi, ta kasa magana, cikin sha'awarta yace, "Ki natsu Aunty Fatima! kin san wannan abin temakon juna zamu yi, na san kema kina bu'katar ka-san-ce-wa 'da Namiji, dan haka ki kwantar da hankalin ki!" La'kwas Fatima tayi a jikin sa, a haka ya samu nasaran kashe mata jiki da kalaman sa har ta amince da shi.
***
Tafe take acikin unguwa tana taunar Cingam, cikin shiga ta rashin kamala, Wata mota ce ta tsaya gaban ta, da sauri taja baya tana dalla masa harara bayan ya fito, Murmushi yayi tare da fa'din, "wannan kallon ya gigita min nutsuwa sarauniyar mata, amma dan Allah ga kati na idan kinje gida ki kira ni, dan naga kamar sauri kike". ya mi'ka mata katin, tare da mi'ka mata rafan dubu-dubu yace "Kisa kati!" Washe baki tayi tace "na gode".

Tun daga wannan lokaci Nana suka 'kulla soyayya me 'karfi da Alhaji Tanko kamar ba mai Aure ba, Aliyu bai isa ya tanka mata ba, da yayi magana zata hau kansa da bala'i tana cewa ita ba sa'ar auren sa bace, 'kaddara ce yasa ta auren sa, dan haka bai isa ya takura taba, haka zai tsuke bakin sa yayi Shiru.

ASALIN LABARIN.

  Wacece Amina?

Amina yarinya ce natsats'tsiya mai tarbiya, bayan ta kammala sakandire ne ta had'u da Adamu, ba 'bata lokaci akayi bikin su, bayan biki ba dad'ewa Amina  ta fara fuskantar matsala daga wajen Adamu, sam bai da sana'a, ga mutuwar zuciya, haka za su yini da yunwa babu abinda ya dame shi, saboda soyayyar da take masa ta daure tare da neman sana'a a gida tanayi, amma da ta fara zasu cinye Jarin, a haka Allah ya bata ciki ta haifi 'yan biyu, Kullun jiya iyau, Adamu ya'ki sauyawa Ganin hakane yasa Amina ta fara shiga ma'kota neman abinci, kasancewar iyayenta talakawa ne basu da 'karfin taimakon ta, wata rana ta shiga gidan ma'kwabtan neman abinci sai ta tarar matar bata nan sai mijin, koda ya tambaye ta damuwar ta bata 'boye masa komai ba na halin da take ciki, nan ya nuna mata 'kudirin sa kan cewa zai biya mata bu'katar ta amma shima zata biya masa tasa bu'katar, da farko ta'ki amincewa amma halin da suke ciki na yunwa da rashin kulawa yasa ta amince. _Wannan shine dalilin fa'dawar Amina zinac-zinace.

Wacece Fatima?

Macen kirki me ha'kuri da juriya, tunda Fatima su kayi Aure da Alhaji Mudi yake musguna mata, duk wani d'awainiyar ta na rayuwa aure zai bata, sai dai ba ya biya mata bu'katar auratayya, gata ta kasance mace me tsananin sha'awa, duk lokacin da zata zo wa Mudi da bu'kata sai ya koreta. Wannan shine dalilin fad'awar Fatima harkar zina.
Abinda Fatima bata sani ba Alhaji Mudi ya kasance mazinaci kuma baya zina da kowa se matar aure wadda matsala ta kawo ta wajen sa.

Wacece Nana?

Mace me tsananin kwad'ayi da buri, duk da kasancewar mahaifanta ba masu ku'di bane amma burinta ta auri me kud'i Wanda hakan bai yiyu ba, sai ta auri miji me 'karamin 'karfi,Hakan yasa ta renashi tare da hangen abinda ake yiwa 'kawayen ta, Kwatsam wata rana ta had'u da wani Alhaji me suna Tanko,daga rana Nanar ta watsar da martaban Auren ta.
Wannan kenan

***
Da Sallama 'dauke ta ta shiga falon tana sakar masa murmushi, take fara'ar fuskar sa ta gushe, ajiye kwalban tularen dake hannun sa yayi, yace "lafiya zaki shigo min 'daki ba Sallama?."Still dai murmushi a fuskar sa tace "shigowa nayi mu gaisa" Da mamaki yake kallon ta, Ido ta kashe masa tare da fad'in "sai da safe miji na" tana gama fad'in haka ta fice.
Fatima na fita wayarta ta hau ruri, ta na dubawa taga Iliya, a tsorace ta amsa tace "me yasa ka kirani yanzu?"
Cikin sauri ta juya jin Alhaji Mudi nacewa "da wa kike waya?" Cikin rawan murya tace "Iliya ne yace ya kira wayar ka bai shiga ba, juyawa yayi ya ce "Fita zanyi kice zan kirasa gobe".
"Ok!'' tace sannan tayi saurin kashe wayar.

Alhaji Mudi na fita yakira wayar Amina, Lokacin da kiran ya shiga Amina na kallo amma ta kasa d'agawa saboda suna tare da Adamu, kallon ta yayi yace "ki amsa mana"kai ta girgiza tace "a'a kiran ba mai amfani bane"
Bai ce komai ba ya mi'ke ya shiga ban d'aki, da sauri ta amsa kiran da ya sake shigowa kafin tayi magana Alhaji Mudi ya riga ta yace"kifito ina jiran ki" be jira jin abinda za tace ba ya kashe.
Kallon Adamu da ya fito daga ban d'aki tayi tace "Zanje gidan aiki sun kirani yanzu" "Ok!" kawai yace.
Da sauri ta fice daga gidan tana jin zuciyar ta na tsinkewa.
Bayan sun fara tafiya a motar Alhaji Mudi ya ce "meke damun ki ne ?" "kawai yau haka nake jin bani da kuzari inaga daga yau zamu ha'kura da fita".
Da mamaki yake Kallon ta ya bud'e baki da niyar magana, wata mota tayo kansu, duk yadda yaso ya kaucewa motar amma ya kasa, sai da motar tabi ta kansu, a take mutane suka yo kansu dan ceton rayuwar su.

Nana da Alhaji Tanko kuwa sun samu matsala duk yanda yaso shawo kan Nana ya kasa, ashe sabon saurayi tayi shiyasa take masa wula'kan ci, rannan da ya gane kuwa baram-baram su kayi.

******
Amina kuwa lokacin da ta farfad'o a asibiti kuka ta dinga yi dan ta samu karaya a'kafa d'aya,
Tun da tadawo gida babu abinda takeyi face kuka da neman yafiyar Adamu kan yayafe mata lefin data masa.
Adamu kuwa jikin sa ba'karamin sanyi yayi ba ganin halin da Amina ta shiga ba, duk dan tasamo musu abinci sosai yayi na damar halayyar sa tare da yin alkawarin ze nemi Sana'a dan ya kula dasu, sannan ya yafe mata.

Alhaji Mudi kuwa 'kafar sa ta hagu tayi dameji aka yankedan haka. Da ya  dawo gida yaga tashin hankali dan turmi da ta'barya ya kama Fatima da Iliya akan gadon sa.
Sosai yaci kuka tare da nadamar mugayen halayyar sa, Yanda yake Zina da matan wasu haka akayi da nasa.

Fatima kuwa kuka ta dinga yi tana cewa seya saketa domin shi ya janyo mata halakar da tafad'a dan tagama zama dashi, da ace yana kula da ita bazata fad'a halaka ba, Dur'kusawa yayi yana kuka tare da bata hakuri kan ya canza hali kar taguje sa,da 'kyar ta ta'amince zata cigaba da zama dashi.
Nana kuwa ta ga gararin rayuwa, domin videon ta tsirara ta gani, suna aikata masha'a yana yawo a duniya, Nana ta zama abin 'kyama a cikin Al'umma, Aliyu kuwa ganin haka yasa yayi mata saki uku tare da koran kare....

_Dan Allah masoyana kuna min 'kauna ta hanyar voting_

RAYUWA KENANWhere stories live. Discover now