CIN AMANAR RUHI BABI NA D'AYA

62 4 0
                                    

💔❣ *CIN AMANAR RUHI* 💔❣

*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*

PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️

*BABI NA D'AYA* 1⃣

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI ,TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W ) DA ALAYANSA DA SAHABBANSA*

*SALONSA NA DABAN NE DA SAURAN LITATTAFAI, KU FARA BIN SA DOMIN KAR AYI BABU KU*🥰

MAFARI

©️ Da wani irin gudu mai tsanani yake figar mashin d'in, yana tsalle kamar zasu fad'o k'asa shi da k'aninsa, yayin da Mukarram yake ruk'unk'ume da Ya Aslam d'in jikinsa na matuk'ar rawa ganin irin gudun da Aslam d'in ke yi na fitar hankali, wata irin zabura Aslam yayi ya kuma dannawa a guje yana k'yalk'yala dariyar tsokana, jin ihun da mukarram ke yi yana numfarfashin tsoro da fad'in,

"Wayyo Ya Aslam don Allah ka jamu a hankali, ina jin kaina na juyawa tamkar zamu fad'o k'asa fa"

Wani irin birki Aslam ya ci, sannan ya kuma zabura ya figa da azabar gudu fiye da na baya yana ta tuntsira dariya yana jin nishad'i, bai damu da magiyar da Mukarram ke masa ba, Mukarram kam kwanciyarsa yayi a bayan Aslam d'in yana sake ruk'unk'umeshi, zuciyarsa cike da tsananin tsoro da fargaba idanuwansa a runtse, jin yadda jikin Mukarram ke rawa sai Aslam ya kuma fashewa da dariya yana wani irin wasa da mashin d'in da suke kai yana karkacewa yana d'angaleshi sama, jin kamar zaso rufto ta baya yasa Mukarram ya kuma fasa k'ara da ihu yana k'ara cusa kansa jikin Aslam, cikin wata shesshek'a mai alamun tsoro ya sake magana.

"Please Ya Aslam zuciyata bugawa take yi fa, Daddy fa ya ce kar muyi gudu, donn Allah ka daina wannan gudun kaji Ya Aslam"

Dai dai lokacin Aslam yayi nufin juyowa daga kewayen da suke yi a layin gidan nasu, tuni daman ya kai k'arshen layin yana juyowa, kusan sau biyu kenan suna zagaye na uku, da k'arfi yasha kwana har yana wata irin mik'ewa akan mashin d'in iska na kad'a rigar da ke jikinsa, shi kam Mukarram k'ara rungumo k'ugun Aslam yayi sosai cikin tsinkewar zuciya da bugun k'irji.

             Daf da zasu iso k'ofar gidan su tuni idanuwan Aslam ya rufe matsanancin gudu yake yi yana jin nishad'i a zuciyarsa babu tsoro ko kad'an, bai ankara ba mashin d'in ya daki wani babban dutse da ke kan hanya a ajiye, tuni kan mashin d'in ya k'wace daga hannunsa ,tamkar k'iftawar ido suka hantsila ta kansu suka fad'i da ka, Kan su ya bugi dandaryar k'asa, yayin da mashin d'in ya hantsilo kan su ya dannesu. Kafin kace me kan Mukarram ya fashe jini yayi tsartuwa yana malala, tuni kuma Mukarram d'in ya sume saboda mummunar buguwar da yayi a kan sa .

       Shima Aslam jini ne  ke zuba a jikinsa, ga hannunsa da mashin ya danne masa, ko yunk'uri ya kasa yi balle ya iya mik'ewa, tsananin azabar da ya keji tamkar ya mutu, ga layin babu kowa babu shige da ficen mutane ko ina yayi d'if, kusan minti goma jini na malala a jikinsu har Aslam ya fara jin wata hajijiya daga inda yake kwance, idanuwansa suka fara lumshewa yana jin tsananin ciwo na sukar sa a gab'ob'in jikinsa, kafin shi ma numfashi ya fara yi masa wahalar shak'a, a take shi ma ya sume a wajen .


*******************


Zaune yake cikin harabar gidan a kan benci da k'aramar rediyo a hannunsa, yana sauraren labarai, yayin da gyangyad'i yake kwasarsa saboda rashin baccin da baya samun yi sosai, jin magana da k'arar k'aramar dariya ya saka shi firgigit ya bud'e idanuwansa yana gyara hular kansa dake k'ok'arin fad'uwa k'asa, yaron da ke gabansa ya kalla Wanda ba zai wuce shekaru goma  kacal a duniya ba, dariya yaron yake yi saboda gyangyad'in da ya tarar Baba mai gadi yana yi,

Baban ya gyara zaman sa yana washe baki da fad'in,

"Ameer yaushe kazo nan? Ban ma san kazo ba bacci ne ya ke d'ib ana wallahi saboda gajiya"

CIN AMANAR RUHIWhere stories live. Discover now