31

210 7 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

Written by Noor Eemaan

Page 61_62

(not edited)
Cikin zallan mamaki su yaya Nadeen ke bin Daddy da kallo tamkar wani sabon hallita, Ammi ta fi kowa shiga mamaki mai yawan gaske... Kuka ta fashe da dashi a lokacin da Daddy ya kai aya a maganar sa, kuka sosai na zallan farinciki hadi da tausayin tilon yarta

Gaban Abrar da na Aaban kusan lokaci daya ya bada sautin "dam daram!" a tunanin su Ammi bata farinciki da auran.

"Haba Rahilat ya kuma kike kuka?" Anty Raheenat ta tambayeta, itama fuskar ta dauke da murmushi.

"Dole in yi kuka Anty, ace diyata tayi aure ban sani ba, wanda babu abinda ya janyo hakan face kin yi wa maganarta duba na nutsuwa, amma ina farinciki sosai da hakan Allah ya basu zaman lafiya"... Ammi ta ce tana kuka, yayinda idanun yan dakin ya ciko da kwallan tausayin su...

Ajiyar zuciya Abrar ta saki da ya taho da hawaye masu sanyi, haka ma Aaban ajiyar zuciya ya saki mai karfi da ya sanya Daddy kallonsa kana ya girgiza kai yana murmushi domin ya fahimci  Aaban sarai.

"Mijin Abrar dita ka zo gareni" Ammi ta ce tana sakar masa murmushi, shima murmushi ya saki mai taushi take son matar ya darsu aransa, dai-dai gabanta ya durkusa, sumar sa mai yalwa ta shafa, hadi da sa masa albarka, cikin jindadi ya amsa hadi da jifan Abrar dake zaune har yanzu kan cinyar Ammi da kallo na
soyaaya...

Murmushi jindadi su Mummy suke yi yayinda farinciki ya cika zuciyoyin su, Hanan ce ta mike zuwa wajen Ammi, Abrar ta fara turewa tana cewa "malama tashi daga kan cinyar Ammi na, katuwa dake salon ki karya ta"

'Wallahi bazan tashi ba" Abrar tace tana murgudawa Hanan baki hadi da sakalo hannunta a wuyar Ammi...

"Toh wallahi sai dai mu raba dan ba zai yu ba, ai nima Ammina ce"....

Dariya yan dakin suka shiga musu, yayinda Aaban ya mato kan kallon Abrar musamman da ta murguda baki wa Hanan sai ya ga ta kara masa kyau ainun...

Nan hira ta barke tsakaninsu, har da baba da ke kwance na sanya musu baki cikin hirar tasu jefi-jefi, sosai shima ke cikin farincikin wanna ranar...

"Ina da magana" Ammi ta ce kanta na kasa.

"muna jin ki Rahilat" in ji Mama

"Ina son a raba aure na da Shettima" Ammi tace tana runtse idanunta domin sunan shi ma bata son shi...

"Yo ko baki fada ba, wallahi kin gama zama a gidan shi, kuma dole mu maka shi kotu abi muku hakkin ku" anty Raheenat tace cikin kakkausar murya dake nuna tana jin tsana da haushin alhaji Shettima.

Hawayen farinciki ne suka zubo wa Abrar jin wai Ammi da bakin ta ta nemi rabuwa da alhaji Shettima...

Gyaran murya Daddy ya yi kana yace" ya kamata idan zamu yanke hukunci mu yanke ba a lokacin fushi ba, shakka babu Shettima ya cancani karban ko wani irin hukunci ne, sai dai bazan so sunan surukata ya baci ba, wanda hakan kan iya shafan jikokina in Allah ya yarda, saboda haka nakeso ayi shari'ar nan  ba tare da duk duniya ta sani ba, saboda kare mutuncin surukata kuma diyata ".

Jinjina kai suka yi cikin gamsuwa, domin ba karya cikin abubuwan da ya fada, tabbas sunan Abrar zai iya baci a duniya wanda zai iya shafan yayan ta, domin yanzu abu zai faru, amma wasu mutane su lauya maganar ya dawo na batanci...

" sanna ya kamata ace mun ziyarci nijar domin Abrar ta gana da kakarta ta wurin uba da ma sauran yan uwansa na can" Cewar yaya Nadeen yana kallon Ammi.

Wani tsohon mikin ne ya taso wa Ammi, take ta ji ranta ya baci tuno wasu abubuwa da suka shude "ba zamu je ba yaya Nadeen ka gafar ce ni" ta ce kanta na kasa alamun girmamawa...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now