"Yaya Sadeeq ka ga yadda kai kyau kamar ba kai ba ko dai an samu wata 'yar baturiyar ce ta rikita min kai?"
Dariya ya yi mai sauti.
"Ke dai Fatima ba zaki canza daga yadda na saki ba zuwa wata Fatimar daban ba."
"Allah Yaya ka qara kyau har da haske sannan fatarka ta amshi garin."
Ta gyara kwanciyar ta tare da ajje laptop d'in da take video call da kyau a saman gadon kwanarta ta ce."Yaya wai ko kasan shirin da Daddy ke yi a kan ka? La na manta Ummi ta gargad'e ni da kar na fad'a maka."
Tai maganar ta ta karshe da kama bakin ta."Ai tun da kika fara fad'a min sai kin qarasa uban da ya ce kar ki koyi controlling d'in bakin ki. Common tell me my friend (dilla fad'a min)"
"Don Allah Yaya kar ka tursasani abinda zan zo na yi kuka a kai muddin Daddy yaji daga gareni ka fara jin maganar."
"Kar ki damu na yi alkawarin babu wanda zance masa ke ce kika fad'a min wannan maganar."
"Ji na yi Daddy da Baffa Mustapha suna maganar wai za'a had'a ka aure da Aunty Maama don su kara dankon zumunci a tsakanin su."
"What!"
Nan take annurin fuskarsa ya sauya damuwa ce ta maye gurbin farin cikin sa."Yaya don Allah ka tuna da alkawarin daka d'auka kar ka bari su Ummi su ji."
"Tun yaushe aka fara hakan?"
"Yaya an d'an dad'e amma nima ban san dalilin su na rashin fad'a maka ba."
"Maama karamar yarinyar da ko kad'an ba ta birgeni saboda girman kai da nuna ita 'yar islamiya ce za'a aura min? No kila bani Sadeeq d'in kika ji ba Fatima"
"Allah Yaya kai ne kuma fa Yaya Aunty Maama tana da kirki gata da son mutane sannan nasan zata so k..."
"Will you shout up your dirty mouth ( zaki rufe min wannan bakin naki)"
"Yaya!"
Da shagwabbiyar murya ta kira shi ta ta'ba baki kamar mai shirin kuka."It's okay, don't cry baby (ya isa, kar ki yi kuka) amma kar ki yarda ki kara kira min sunan wannan yarinyar in muna hira."
"Yaya"
Ta sake kiransa da muryar kuka."What again (menene kuma)"
"Yaya alkawarin daka d'auka"
"Na ji babu mai ji inhar ke ma ba zaki sake kira min sunan wannan 'yar kauyen a gabana."
"Na yarda amma Yaya tana da kirki fa."
"Tun yanzu kin fara karya alkawarin ki nima in na karya nawa kar ki yi blaming d'ina."
"Shi kenan Yaya sai anjima ina da test gobe a school zan yi karatu."
"Okay, ki nutsu ki yi karatu da kyau kuma ki tabbatar kin ci test d'in nan."
"Zan ci Yaya, sai da safe."
"Ku dare ne a Nigeria amma ni yanzu rana ne anjima kad'an da na yi sallar la'asar zamu tafi evening training."
"To sai anjima kuma sai da safe."
"Take good care of yourself and stay out of trouble ( ki kular min da kan ki kuma ban da fitina)"
"Okay, bye."
Ta yi sallamar da katse kiran a lokaci d'aya. Babu wani test da take da shi kawai hirar Yayan nata ne ya gundire ta saboda bai amince da Aunty Maama ba, bata ta'ba ganin ta yi masa laifi ba duk zuwan da take yi kuma tana kokarin suturta kan ta daga suturun da basu dace ta saka ba.
YOU ARE READING
KADDARAR RAI
Non-FictionKADDARAR RAI! Labari ne kan Kaddarar Maama, Sadeeq, Faiza da Ahmad.